Trump Zai Sauya Salon Yaki da Iran, Sojojin Amurka 2,500 Sun Nufi Gabas ta Tsakiya
- Amurka ta tura karin dubunnan dakarun sojojin ruwa da jiragen yaki zuwa Gabas Ta Tsakiya domin karfafa yakin da take yi da kasar Iran
- Gwamnatin Trump na nazarin tura sojojin kasa zuwa tsibirin Kharg na Iran domin lalata karfin tattalin arzikin kasar da danyen man fetur dinta
- Jirgin yakin USS Bush ne zai maye gurbin USS Ford a yankin Gulf yayin da yakin da ake yi a Gabas ta Tsakya ya cika mako uku cif
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Amurka - Gwamnatin Amurka ta fara tura dubban dakarun sojojin ruwa zuwa yankin Gabas Ta Tsakiya domin ƙarfafa dakarunta dake fafatawa da ƙasar Iran.
Jami’an Amurka sun shaida wa manema labarai cewa, ko da yake ba a yanke shawarar tura sojojin cikin ƙasar Iran kai-tsaye ba, wannan ƙarin dakarun zai taimaka wajen gudanar da wasu manyan ayyuka na soja a nan gaba.

Source: Getty Images
Amurka ta tura dubban sojoji Gabas ta Tsakiya
A cikin wannan sabon shiri, babban jirgin yaƙi mai ɗaukar dakarun ruwa da na sama, USS Boxer, tare da tawagar dakarun soji na musamman (MEU) guda 2,500, sun bar gaɓar tekun yammacin Amurka makonni uku kafin lokacin da aka tsara, in ji rahoton Reuters.
Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan da aka bayyana cewa gwamnatin Shugaba Donald Trump na nazarin tura ƙarin dubban sojoji domin ƙarfafa hare-haren da take kaiwa a yankin.
Wannan ƙarin dakarun zai haɗu da sojojin Amurka kusan 50,000 da tuni suke yankin Gabas Ta Tsakiya, kuma suke aiwatar da hare-hare a yakin da ake yi da Iran.
Shirye-shiryen tsananta hare-hare kan Iran
Rahoton jaridar The Detroit News ya nuna cewa wasu daga cikin dabarun da Amurka ke shirin aiwatarwa sun hada da:
- Sauya jiragen yaƙi: Jirgin yaƙi mai ɗaukar jiragen sama na USS Bush ne zai maye gurbin USS Ford, wanda ya sami matsalar gobara a cikinsa kuma yake kan hanyarsa ta zuwa gyara a tsibirin Crete na ƙasar Girka.
- Tsaron mashigar Hormuz: Rahotanni sun nuna cewa ɗaya daga cikin abubuwan da Trump ke nazari shi ne tura dakarun ƙasa zuwa gaɓar tekun Iran domin tabbatar da tsaron mashigar ruwan Hormuz da aka toshe.
- Harin tsibirin Kharg: Gwamnatin Amurka ta tattauna yiwuwar tura sojojin ƙasa zuwa tsibirin Kharg na Iran, wanda shi ne matattarar kashi 90% na man fetur ɗin da Iran ke fitarwa zuwa ƙasashen waje.

Source: Getty Images
Hadarin tura sojojin Amurka cikin Iran
Duk da waɗannan shirye-shirye, Shugaba Trump ya shaida wa manema labarai a jiya Alhamis cewa bai riga ya tura sojoji "ko'ina ba," yana mai cewa idan ma zai yi hakan, ba zai sanar da 'yan jarida ba, in ji rahoton The New York Times.
Masana na ganin cewa tura sojojin ƙasa cikin Iran babban haɗari ne na siyasa ga Trump, ganin yadda jama'ar Amurka ba sa goyon bayan wannan yaƙin, sannan kuma hakan ya saɓa wa alkawuran da ya yi na guje wa jefa Amurka cikin sabon yaƙi a Gabas Ta Tsakiya.
Bataliyar MEU ta bar kasar Japan
A wani labari, mun ruwaito cewa, Amurka ta shirya tura bataliyar sojojin ruwanta masu hatsari zuwa Gabas ta Tsakiya domin kare jiragen ruwa a mashigar Hormuz.
Dakarun za su tashi daga kasar Japan a cikin jiragen yaki karkashin USS Tripoli domin karfafa ayyukan sojin Amurka kan kasar Iran.
Wannan runduna ta musamman tana da jiragen yaki da na kwashe mutane wadanda za su iya kai hare-hare ta cikin ruwa baki daya.
Asali: Legit.ng

