Dan Jaridar Amurka Ya Yi Ikirarin Netanyahu Ya Mutu har Lahira
- Ana cigaba da yada rade-radi game da ikirarin mutuwar Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu a yakin da suka fara da kasar Iran
- Wani dan jarida mai zaman kansa a kasar Amurka, Nathan Levins ya yi ikirarin cewa Benjamin Netanyahu ya mutu a farkon watan Maris, 2026
- Hakan na zuwa ne duk da wani bidiyo da shugaban ya fitar domin ƙaryata rade radin mutuwarsa da nuna cewa yana raye kuma yana lafiya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - A kwanakin baya, an yaɗa rade-radin cewa Firaministan Isra'ila ya rasu bayan wasu hare-hare da Iran ta kai birnin Tel Aviv.
Domin nuna yana raye bayan hare-haren, Firaminista Benjamin Netanyahu ya fito ya yi wani bidiyo dauke da kofi yana shan shayi a wani ofis.

Kara karanta wannan
Isra'ila ta jawo wa kanta, Rasha ta shiga kafar wando daya da ita kan hari a Lebanon

Source: Getty Images
Ana tsaka da rade-radin mutuwar ne wani dan jarida mai zaman kansa a Amurka, Nathan Levins ya wallafa sako a X yana cewa Netanyahu ya mutu.
Ikirarin mutuwar Benjamin Netanyahu
Dan jarida daga kasar Amurka, Ethan Levins, ya yi ikirarin cewa Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya rasu a ranar 8 ga Maris, 2026.
Levins ya kuma yi zargin cewa dan Firaministan, Yair Netanyahu, bai yi wani rubutu a dandalin X ba na tsawon kwanaki bakwai saboda zaman makoki nd Yahudawa ke yi.
Levins ya ce:
“Netanyahu ya rasu a ranar 8 ga Maris, 2026.
"Wannan ne ya sa Yair ya dauki hutu na kwanaki 7 a X, domin zaman makokin Yahudawa.
"Ya yi rubutu na karshe a ranar 8 ga Maris, sannan ya jira daidai kwanaki 7 kafin ya sake fitar da wani sako a ranar 15 ga Maris.”
Wasu rahotanni sun ce Ethan a da yana goyon bayan Isra’ila kafin daga baya ya sauya ra’ayi ya fara sukan kasar kan hare-hare da take kaiwa.
Game da waye Levins, an bayyana cewa shi ɗan jarida ne mai zaman kansa daga Amurka wanda a halin yanzu yake sukar hare-haren Isra’ila a Gaza, Lebanon da kuma Iran.
Da gaske Netanyahu ya mutu?
Tun bayan da Amurka da Isra’ila suka fara yaki da Iran a ranar 28 ga Fabrairu 2026, wasu kafafen sadarwa suka rika yada labarai game da mutuwar Netanyahu da sauran manyan ‘yan siyasar Isra’ila.
Ana haka ne Firaministan ya fito a kafafen sada zumunta a ranar Lahadi, 15 ga Maris 2025 yana musanta jita-jitar, inda ya wallafa wani bidiyo.

Source: Getty Images
A cikin bidiyon, an ji wata muryata tana cewa wa Netanyahu:
“Mutane a yanar gizo na cewa ka mutu.”
Euro News ta wallafa cewa ya amsa da cewa:
“Ina son shayi sosai. Ka san me? Ina matukar kaunar al’ummata. Yaya suke? Madalla. Kana so in kirga yatsuna?”
An ga bakon jirgin yaki a Amurka
A wani rahoton, kun ji cewa wani jirgin yaki maras matuki da ba a san daga ina ya fito ba ya yi shawagi a sansanin sojin Amurka.
An bayyana cewa jirgin ya bayyana ne a sansanin sojin da ministocin yaki da na harkokin wajen Amurka ke zama a Washington.
Lamarin ya dauki hankali tare da jawo zaman dar-dar lura da yadda Amurka da Isra'ila ke gwabza yaki da Iran a Gabas ta Tsakiya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

