Wuya Ta Yi Wuya: Amurka Ta Yi Magana kan Cire Takunkumin da Ta Sanya wa Iran
- Amurka na shirin janye takunkumin da ta kakabawa danyen man Iran dake makale a teku domin rage radadin tsadar mai da ya addabi duniya
- Ministan makamashin Amurka, Chris Wright, janye takunkumin zai sa a iya tace man don ya shiga kasuwa a cikin kwanaki 30 zuwa 45 masu zuwa
- Sai dai kuma, tuni hukumar IEA ta yi gargadin cewa za a dauki watanni shida kafin a dawo da zirga-zirgar mai da iskar gas daga yankin Gulf
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Amurka - Gwamnatin Amurka ta ce janye takunkumi kan danyen man kasar Iran dake makale a cikin manyan jiragen ruwa zai ba da damar isar da man zuwa nahiyar Asiya cikin kwanaki uku zuwa hudu.
Ministan makamashin Amurka, Chris Wright, ya bayyana cewa wannan mataki zai taimaka wajen saukar da farashin mai da ya yi tashin gwauron zabi sakamakon rufe mashigar ruwan Hormuz da Iran ta yi.

Kara karanta wannan
Trump zai sauya salon yaki da Iran, sojojin Amurka 2,500 sun nufi Gabas ta Tsakiya

Source: Getty Images
Amurka za ta janye takunkumin Iran
Ministan baitul malin Amurka, Scott Bessent, ya goyi bayan wannan mataki a jiya Alhamis, inda ya ce Washington na neman hanyoyin dakile hauhawar farashin mai a kasuwannin duniya, in ji rahoton Aljazeera.
A cewar Chris Wright, da zarar an janye takunkumin, man zai isa tashoshin jiragen ruwa cikin kwanaki kadan, sannan a tace shi domin ya shiga kasuwa a cikin kwanaki 30 zuwa 45 masu zuwa.
Sai dai duk da wannan yunkuri, farashin man fetur ya ci gaba da yin sama a yau Juma'a. Shugaban Hukumar Makamashi ta Duniya (IEA), Fatih Birol, ya yi gargadi kan hakan.
Tasirin rufe mashigar Hormuz ga farashin mai
Birol ya ce duniya na fuskantar babban kalubalen makamashi mafi muni a tarihi, inda ya bayyana cewa za a iya daukar akalla watanni shida kafin a farfado da zirga-zirgar mai da iskar gas daga yankin Gulf.
Shugaban na IEA ya kara da cewa ’yan siyasa da kasuwanni na raina girman matsalar dake akwai, ganin cewa kusan kashi daya bisa biyar na danyen mai da iskar gas na duniya ne ya makale a halin nanzu, cewar rahoton The Irish Times.

Source: Twitter
Hauhawar farashin mai da gas a duniya
Farashin kowace gangar danyen mai na Brent ya lula zuwa sama da dala 119 a ranar Alhamis, wanda shi ne mafi girma tun tsakiyar shekarar 2022.
Tun bayan barkewar yakin, farashin man na sauya wa da akalla dala 10 a kowace rana sakamakon hare-hare kan kayayyakin makamashi, in ji rahoton CNBC.
Haka zalika, farashin iskar gas ya ci gaba da kasancewa cikin fargaba, inda bankin ECB ya yi gargadin cewa za a iya samun hauhawar farashin kayayyaki a yankin Turai zuwa kashi 6.3 tare da janyo koma-bayan tattalin arziki.
Trump na shirin matsawa Iran lamba
A wani labari, mun ruwaito cewa, Amurka tana duba wasu tsare-tsare na mamaye ko killace tsibirin Kharg na Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Gwamnatin Donald Trump tana duba yiwuwar hakan ne domin matsa wa ƙasar Iran lamba ta buɗe Mashigar Hormuz, don farashin mai ya sauko.
Kulle mashigar Hormuz da Iran ta yi ya jawo an samu tashin farashin danyen mai da sauran kayan makamashi a duniya, lamarin da shafi kowa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
