Switzerland Ta Rufe Ido, Ta Dakatar da Sayar wa Amurka Makamai kan Yaƙi da Iran

Switzerland Ta Rufe Ido, Ta Dakatar da Sayar wa Amurka Makamai kan Yaƙi da Iran

  • Gwamnatin Switzerland ta dakatar da ba kamfanoni lasisin sayar wa Amurka makamai saboda shigarta yakin Iran da ya saba wa dokar kasar
  • Tun bayan harin farko da Amurka da Isra'ila suka kai kan Iran a watan Fabrairu, Switzerland ta dakatar da sayar wa kasashen biyu makaman yaki
  • Switzerland ta kuma ki amincewa da bukatar Amurka na yin amfani da sararin samaniyarta domin zirga-zirgar jiragen yaki zuwa Iran a kwanan baya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Switzerland - A yau Juma'a ne gwamnatin Switzerland ta sanar cewa ba za ta sake bayar da lasisi ga kamfanoni domin fitar da makamai zuwa ƙasar Amurka ba.

Wannan mataki ya biyo bayan hare-haren da ake ci gaba da kai wa ƙasar Iran, inda Switzerland ta kafa hujja da dokarta ta kasancewa ƙasar da ba ta shiga yaƙin kowa.

Kara karanta wannan

Yaki ya yi zafi, Amurka ta fara neman $200bn don ci gaba da farmakin Iran

Switzerland ta dakatar da kasuwancin makaman yaki da kasar Amurka.
Hagu zuwa Dama: Shugaban Amurka, Donald Trump, da shugaban Switzerland, Guy Parmelin. Hoto: Nathan Howard / NurPhoto via Getty Images
Source: Getty Images

Switzerland ta soke sayar wa Amurka makamai

A cikin wata sanarwa da gwamnatin ta fitar, ta bayyana cewa ba za a amince da fitar da kayan yaƙi zuwa ƙasashen da ke da hannu a rikicin makami na duniya da Iran ba, in ji rahoton Aljazeera.

Saboda wannan dalili, a halin yanzu Switzerland ba za a bai wa Amurka damar sayen makamai daga ƙasar ba.

Kazalika, gwamnatin ta bayyana cewa tun bayan da Amurka da Isra'ila suka fara kai hare-hare kan Iran a ranar 28 ga Fabrairu, 2026, ba ta sake bayar da wani sabon lasisin fitar da kayan yaƙi zuwa Amurka ba.

Bugu da kari, Switzerland ta kuma ƙara da cewa tun shekaru da dama ba ta bai wa ƙasar Isra'ila lasisin sayen makamai daga kamfanoninta ba.

Switzerland ta ki amincewa da bukatun Amurka

Wannan mataki ya yi daidai da irin wanda Switzerland ta ɗauka a lokacin mamayar Iraki a shekarar 2003, inda ta dakatar da zirga-zirgar jiragen yaƙi a sararin samaniyarta da kuma sayar wa ƙasashen da ke yaƙin makamai.

Kara karanta wannan

Gobara ta tilasta wa jirgin yakin Amurka gudu wa daga yakin Iran

A ƙarshen mako da ya gabata, Switzerland ta tabbatar da cewa ta yi watsi da buƙatun Amurka guda biyu na amfani da sararin samaniyarta domin zirga-zirgar jiragen yaƙi da ke da alaƙa da rikicin Iran, ko da yake ta amince da wasu buƙatun guda uku na daban.

Gwamnatin Switzerland ta ce wani rukunin kwararru zai riƙa nazari kan halin da ake ciki akai-akai domin tabbatar da cewa kowane mataki da aka ɗauka ya yi daidai da dokokin zama a tsaka-tsaki na ƙasar.

Kasar Switzerland ta ce ta yi watsi da wasu bukatu 2 da Amurka ta gabatar mata a yaki da Iran
Shugaban kasar Switzerland, Guy Parmelin. Hoto: NurPhoto via Getty Images
Source: Getty Images

Amurka na jin 'Turai ta ha'ince ta' - Lukashenko

Wannan na zuwa ne yayin da shugaban ƙasar Belarus, Alexander Lukashenko, ya bayyana cewa Amurka na jin cewa ƙasashen Turai sun yaudare ta ta hanyar ƙin ba ta goyon bayan soja a rikicinta da Iran, cewar kamfanin dillancin labaran Rasha.

Lukashenko ya ruwaito cewa Shugaba Donald Trump ya shiga damuwa sosai game da yadda ƙasashen Turai suka "watsar" da Amurka duk da irin taimakon da Amurka ta ba su ta fuskar tattalin arziki da kuma tsaro a ƙarƙashin ƙungiyar NATO.

A cewar Lukashenko, Amurka na ganin wannan mataki na Turai a matsayin cin amana, musamman idan aka yi la'akari da tarihin yadda Amurka ta taimaka wa Jamus da sauran ƙasashe bayan yaƙi.

Kara karanta wannan

"Ba mu miƙa wuya ga azzalumai": Iran ta gindaya sharadin kawo ƙarshen yaƙi da Amurka

Ra'ayin Switzerland kan yakin Iran da Amurka

Tun da fari, kun dai ji cewa, Ministan tsaron Switzerland ya ce hare-haren Amurka da Isra’ila kan Iran sun karya dokokin ƙasa da ƙasa.

Gwamnatin Switzerland ta bayyana cewa irin waɗannan hare-hare sun saɓa da dokar hana amfani da ƙarfi tsakanin ƙasashe.

Wasu manyan jami’an Turai da masana sun nuna shakku kan halaccin wannan yaƙi a dokokin duniya bayan Isra'ila da Amurka sun haɗa kai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com