Switzerland ta bankaɗa yadda ta kulla sakin 'yan mata 82 da 'yan Boko Haram suka rike har shekaru 3
- Switzerland ta shiga al’amarin ne "da kasar Najeriya ta nemi taimakon gareta
- Wadanda an saki sun kasance fiye da ‘yan makaranta 200 da Boko Haram suka sace
- Najeriya na godiya ga gwamnatin Switzerland, da kwamitin ‘Red Cross’
- Cikkaken bayani daga cikin tattaunawar da ya sa aka saki 'yan matan ba a bayyana tukuna
Kakakin harkokin kasar waje na Switzerland Noemie Charton ya ce kasar Switzerland ta tsayar tattaunawar na sakin 'yan mata 82 daga cikin wadanda kungiyar Boko Haram suka sace a Najeriya.
Ya ce kasar Switzerland ta shiga al’amarin ne "da kasar Najeriya ta nemi taimakon gareta "kuma saboda" damuwa agaji."
Da farkon watan Mayu, 'yan kungiyar Boko Haram sun saki 'yan mata wanda suna kãmamme tun shekara 3, a musayar da fursunoni.
KU KARANTA: Fafaroma ya yafewa babban faston da yayi fyade da yara 30 har ya cinna musu cutar Kanjamau (Bidiyo)
Wadanda an saki sun kasance wani ɓangare na fiye da ‘yan makaranta 200 da Boko Haram suka sace daga kauyen Chibok, a cikin jihar Borno, a watan Afrilu 2014.
Najeriya na godiya ga gwamnatin Switzerland, da kwamitin ‘Red Cross’na kasashen waje, kazalika da na gida da kuma kungiyoyi masu zaman kansu na kasa domin taimakawa sakin 'yan matan. “Shigewan Switzerland cikin wannan al’amarin ya taso ne don shiryar da ka'idodin ta rashin alaka da kuma rashin tsangwama.”
Charton ya kara da cewa Switzerland na kiran a saki sauran 'yan matan Chibok har yanzu ƙangin bautar da kungiyar.
A kalla 'yan matan Chibok 21 ne aka saki karshe Oktoba a wani kulla yarjejeniyar ta Switzerland da kuma ‘Red Cross’. An yi imani da cewa sauran 'yan mata 114 har yanzu na wurin 'yan Boko Haram.
KU KARANTA: Muhimman ayyuka 5 da Osinbajo yayi tun bayan tafiyar Buhari Landan
"Wakilin Switzerland ya yi muhimmiyar taka rawa a shirya tattaunawar daga cikin Najeriya da kuma waje Najeriya tare masu fada a ji na gida kamar Barrister Zannah Mustapha da kuma lauya hakkin yan Adam Asiha Wakil wanda dangantaka su da ‘yan ta’addan ya kawo dõgara acikin maganan," ya ci gaba.
Cikkaken bayani daga cikin tattaunawar da ya sa aka saki 'yan matan ba a bayyana tukuna, kuma kadan ne aka sani game da fursunonin da aka musayar.
Ka tuna cewa Legit.ng ma ya ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta musayar biyar 'yan Boko Haram ga 82 ‘yan makarantar Chibok da aka saki kwanan nan. Wannan ya saba wa wasu rahotannin kafofin watsa labaru cewa shugabannin ‘yan Boko Haram 2 kawai ne aka saki a cikin musayar.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Wannan Legit.ng bidiyo na nuna tunawan shekaru 3 da aka sace 'yan matan makarantan Chibok
Asali: Legit.ng