China Ta Gaza Hakuri, Ta Sake Yunkurowa kan Yakin Amurka da Kasar Musulunci Ta Iran

China Ta Gaza Hakuri, Ta Sake Yunkurowa kan Yakin Amurka da Kasar Musulunci Ta Iran

  • China ta jaddada kudirinta na ci gaba da shiga tsakani don neman dakatar da rikici da kawo karshen yakin da ya barke tsakanin Amurka, Isra'ila da Iran
  • Ministan Harkokin Wajen China, Wangi Yi ya bayyana cewa yakin bai kamata ya faru ba kuma babu dalilin ci gaba da shi
  • Ya nuna goyon baya ga Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) wajen kare 'yancin kasar da tsaronta yayin da yakin ke yaduwa a Gabas ta Tsakiya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

China - Yayin da yaki tsakanin Amurka/Isra'ila da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ke kara tsananta, kasar China ta jaddada bukatar tsagaita wuta don samar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.

Ministan Harkokin Waje na China, Wangi Yi, ya bayyana cewa kasarsa za ta ci gaba da kokarin shiga tsakani domin dakatar da rikici da kawo karshen yaki a yankin Gabas ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

Kasashen Musulmi sun kira taron gaggawa saboda yakin Iran da Amurka

Shugaban China.
Shugaban kasar China, Xi Jinping a wurin taron kasa da kasa Hoto: Vincent Thian
Source: Getty Images

Kasar China ta shirya shiga tsakani

Tashar Al-Jazeera ta tattaro cewa Ministan ya bayyana haka ne a wani zaman tattaunawa da ya yi da Jakadan Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) a China.

A wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen China ta fitar yau Laraba, 18 ga watan Maris, 2026, ta nakalto ministan na cewa babu dalilin fara wannan yaki tun farko, don haka za su shiga tsakani.

Wangi Yi ya ce:

“Wannan yaki bai kamata ya faru ba tun usuli, kuma babu wani dalili na ci gaba da shi.”

China ta jaddada goyon baya ga UAE

Haka kuma, Wangi Yi ya jaddada goyon bayan China ga Hadaddiyar Daular Larabawa wajen kare ‘yancin kasarta da tsaron al’ummarta, cewar rahoton Global Times.

Ya kara da cewa samun zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya zai amfani duka bangarorin duniya kuma zai kawo ci gaba mai dorewa ga yankin.

Ministan ya kuma yi kira ga dukkan kasashen da ke da hannu a rikicin, watau Amurka, Isra'ila da Iran, da su nemi hanyoyin sulhu da tattaunawa maimakon amfani da karfi.

Kara karanta wannan

Saudiyya da Qatar sun sake sabon lale, sun yunkuro kan batun yakin Iran da Amurka

Mojtaba da Netanyahu.
Jagoran addinin kasar Iran, Mojtaba Khamenei da Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

China na son zaman lafiya a duniya

Wannan mataki na China na nuna sha’awar kasar wajen zama mai shiga tsakani a harkokin duniya da tallafawa zaman lafiya.

A ranar Asabar, 28 ga watan Fabrairu, 2026 aka fara yaki tsakanin Iran da hadakar Amurka da Isra'ila, lamarin da ya jawo asarar dubban mutane da jikkata wasu da dama.

Tuni dai gwamnatin China ta fara tura kayan tallafi ga Iran da wasu kassshen Gabas ta Tsakiya domin taimakawa mutanen da wannan rikici ya shafa.

China ta tallafawa iyalan dalibai a Iran

An ji cewa kasar China ta bayyana cewa za ta bayar da tallafin $200,000 ga iyalan daliban da aka kashe a harin makami kan wata makaranta a Iran.

Gwamnatin China ta bayyana harin a matsayin wanda aka kai ba tare da tantancewa ba, tana mai cewa ya faru ne a farkon rikicin da ya barke a Gabas ta Tsakiya.

Gwamnatin Iran ta zargi Amurka da Isra’ila da kai harin makamin da ya afkawa makarantar da ke kudancin kasar a ranar farko ta yakin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262