An ‘Gano’ Yadda Rasha Ta Tallafa wa Iran a Yakinta da Isra’ila, Amurka

An ‘Gano’ Yadda Rasha Ta Tallafa wa Iran a Yakinta da Isra’ila, Amurka

  • Rahotanni sun bayyana cewa Rasha na taimakawa Iran da bayanan tauraron dan Adam da fasahar jiragen yaki
  • Majiyoyi suka ce Rasha ta ba Iran bayanan wuraren sojojin Amurka domin kai hare-hare domin samun nasara a yakin
  • Donald Trump ya ce yana ganin Rasha na taimakawa Iran ta wasu hanyoyi duk da musanta hakan da ta yi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Moscow, Russia - Rahotanni sun bayyana cewa Rasha ta kara karfafa hadin gwiwar soji da Iran tun farkon yakin da take yi da Amurka da kuma isra’ila.

Wasu majiyoyi suka ce Rasha na ba Iran bayanan sirri na amfani da tauraron dan Adam da fasahar jiragen yaki marasa matuki.

Ana zargin Rasha na taimaka wa Iran a yaki
Shugaba Masoud Pezeshkian na Iran da Vladimir Putin na Rasha. Hoto: Alexander KAZAKOV/POOL/AFP.
Source: Getty Images

Ana zargin Rasha na taimakon Iran

Jaridar The Wall Street Journal ta ruwaito cewa Rasha ta bai wa Iran bayanan tauraron dan adam domin taimaka mata gano wuraren sojojin Amurka a Gabas ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

Mashigar Hormuz: Kasashe 5 sun kunyata Donald Trump bayan bukatarsa gare su

An ce wannan taimako ya hada da bayanai kan wuraren da sojojin Amurka da kawayenta suke, domin saukaka kai hare-hare.

Haka kuma, rahoton ya ce Rasha ta bai wa Iran sababbin fasahohi na jiragen yaki marasa matuki, musamman inganta jiragen Shahed.

An bayyana cewa sababbin kayan sun taimaka wajen kara ingancin gano hari da kuma daidaiton kai farmaki, kamar yadda Reuters ta ruwaito.

Bugu da kari, Rasha ta ba Iran shawarwari kan yadda za ta yi amfani da jiragen yaki marasa matuki, ciki har da adadin da ya dace da kuma tsayin da za su kai hari.

Ana zargin Rasha na ba Iran taimako a bangarori da dama
Shugaba Vladimir Putin na kasar Rasha. Hoto: Gavril Grigoroc.
Source: Getty Images

Zargin da Amurka ke yi wa Rasha

A wani rahoto na The Washington Post, an ce Rasha ta kuma ba Iran bayanai kan wuraren jiragen ruwa da jiragen sama na Amurka.

Masana sun ce wannan taimako na da muhimmanci saboda Iran na da karancin tauraron dan adam na soja.

Sai dai wakilin Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya, Steve Witkoff, ya ce Rasha ta tabbatar musu cewa ba ta taimakawa Iran a kai hare-hare.

Kara karanta wannan

Rasha: Amurka ta fara bakin jini a Turai saboda yakin Iran

Duk da haka, Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce yana ganin Rasha na iya taimakawa Iran ta wasu hanyoyi, yana kwatanta hakan da yadda Amurka ke taimakawa Ukraine.

Abin da Amurka ke gani kan zargin Rasha

Witkoff ya kara da cewa Amurka za ta iya daukar maganar Rasha a matsayin gaskiya, amma har yanzu ana sa ran hukumomin leken asiri su kara bincike kan lamarin.

Sannan Witkoff ya ce shi da Jared Kushner sun kuma yi wata tattaunawa ta daban da mai ba shugaban Rasha shawara kan harkokin waje, Yuri Ushakov.

Rasha ta karyata zargin taimakawa Iran

Mun ba ku labarin cewa majiyoyi sun bayyana cewa kasar Rasha ta yi martani game da zarginta da ake yi da ba da bayanan sirrin sojojin Amurka.

Maganar ta fito ne bayan tattaunawar waya tsakanin Shugaba Donald Trump da Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin game da yakin Iran da Isra'ila.

Rahoto ya zargi Moscow da bai wa Tehran bayanan wuraren jiragen ruwan yaki da jiragen sama na Sojojin Amurka a yankin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.