Iran Ta Kama Ɗan Leƙen Asirin Isra'ila ana tsaka da Yaƙi, An Zartar Masa Hukunci

Iran Ta Kama Ɗan Leƙen Asirin Isra'ila ana tsaka da Yaƙi, An Zartar Masa Hukunci

  • Iran ta sanar da kama ɗan leƙen asiri, mutumin ya yi wa Isra’ila leƙen asiri ta hanyar ba da hotuna da bayanai masu muhimmanci
  • An kama shi a lokacin rikicin kwanaki 12 tsakanin Iran da Isra’ila wanda ke ƙoƙarin mamaye Gabas ta Tsakiya bayan tsoma bakin Amurka
  • Rahotanni sun ce an ɗauki ɗan leƙen asirin aiki ta yanar gizo yayin da yake Sweden, inda ya zo aikin sa ido a Iran

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Ƙasar Iran–Hukumomin ƙasar Iran sun sanar da aiwatar da hukuncin kisa kan wani mutum da suka zarga da yi wa hukumar leƙen asirin Isra’ila, wato Mossad, aiki.

Rahotonni sun bayyana cewa an kashe mutumin ne bayan an bi dukkanin matakan shari’a, kuma Kotun Koli ta amince da hukuncin.

Kara karanta wannan

Iran ta yi ruwan bama bamai a tsakiyar Isra'ila bayan kisan Larjani, an kiɗima Yahudawa

Iran ta kama ɗan leƙen asirin Isra'ila
Shugaban ƙasar Isra'ila, Masoud Pezeshkian Hoto: Masoud Pezeshkian
Source: Getty Images

Al-Jazeera ta ruwaito a cewar rahoton, mutumin ya shiga hannun dakarun IRGC a watan Yuni a birnin Savjbolagh, a daidai lokacin da ake fama da rikicin kwanaki 12 tsakanin Iran da Isra’ila.

Iran ta kashe dan leken asirin Isra'ila

Reuters ta ruwaito an ce jami’an tsaro sun kama mutumin da ake zargi bayan samun bayanan sirri da suka nuna yana hulɗa da jami’an leƙen asiri na waje.

Rahoton ya kara da cewa lokacin da aka kama shi, yana dauke da wasu kayayyakin sadarwa na zamani da suka hada da na’urorin leƙen asiri da hanyoyin sadarwar tauraron dan adam.

Hukumomi sun bayyana cewa irin wadannan kayayyaki na nuna yadda ake gudanar da ayyukan leƙen asiri na zamani cikin sirri.

An ruwaito mutumin ya fara hulɗa da jami’an Mossad ne ta yanar gizo yayin da yake zaune a ƙasar Sweden inda ya sanya bayanansa a wani shafin talla na tafiye-tafiye.

Kara karanta wannan

Trump ya soki NATO, ya yi magana game da ƙasashen da suka ki taya su yaƙar Iran

An kashe dan leken asirin Isra'ila a Iran
Firaministan kasar Isra'ila, Benjamin Netanyahu da shirin yaƙi Hoto: Benjamin Netanyahu
Source: Facebook

Rahotanni sun tabbatar da cewa daga wannan talla ne wani jami’in Mossad mai jin harshen Farisanci ya tuntube shi har aka kulla alaƙa.

Bayan wannan hulɗa ta farko, ana zargin ya fara aika hotuna da bayanai game da wurare masu muhimmanci a cikin Iran ga jami’an Isra’ila.

Yadda aka kai dan leken Isra'ila kotu

Hukumomin Iran sun ce irin wannan aiki na barazana ga tsaron ƙasa, musamman a lokacin da ake cikin rikici da wata ƙasa.

Rahoton ya bayyana cewa bayan an kama shi, an gurfanar da shi a gaban kotu inda aka same shi da laifi. Daga nan ne aka yanke masa hukuncin kisa, wanda daga bisani Kotun Koli ta tabbatar.

Wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun takun-saka tsakanin Iran da Isra’ila.

Hukumomin Iran sun sha alwashin ɗaukar matakan tsaro masu tsauri kan duk wanda aka samu da hannu a irin waɗannan ayyuka.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: Ana cikin musayar wuta, an kama masu yiwa Iran zagon kasa a yaki da Amurka

Iran ta kai hari Isra'ila

A baya, mun wallafa cewa Iran ta kai hare-hare kan wuraren soji sama da 100 a ƙasar Isra’ila a matsayin ramuwar gayya bayan mummunan harin da aka kai mata.

Harin makamai masu linzami da Iran ta kai ya hallaka mutane biyu a kusa da Tel Aviv bayan Isra'ila ta kashe jagora a tsaron kasar, Ali Larjani da wasu manyan mutane.

An kuma kai hari kan ofishin jakadancin Amurka a Bagadaza da sansanin soja a UAE bayan mummunan hari a Iran da ya kara jefa ƙasar a cikin mummunan hali.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng