Iran Ta Yi Ruwan Bama Bamai a tsakiyar Isra'ila bayan Kisan Larjani, An Kiɗima Yahudawa

Iran Ta Yi Ruwan Bama Bamai a tsakiyar Isra'ila bayan Kisan Larjani, An Kiɗima Yahudawa

  • Iran ta kai hare-hare kan wuraren soji sama da 100 a ƙasar Isra’ila a matsayin ramuwar gayya bayan mummunan harin da aka kai mata
  • Harin makamai masu linzami da Iran ta kai ya hallaka mutane biyu a kusa da Tel Aviv bayan Isra'ila ta kashe jagora a tsaron kasar, Ali Larjani
  • An kuma kai hari kan ofishin jakadancin Amurka a Bagadaza da sansanin soja a UAE bayan mummunan hari a Iran

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Iran – Kasar Iran ta ƙara tsananta hare-haren soji kan kadarorin Amurka da kuma Isra’ila a ranar Laraba, 18 ga watan Maris na shekarar 2026.

Wannan na zuwa a matsayin wani mataki da ake ganin ramuwar gayya ce bayan kashe babban jami’in tsaron kasar, Ali Larijani, da aka yi cikin dare.

Kara karanta wannan

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta tsoma baki game da harin Iran kan kasashen Larabawa

Iran na ci gaba da harin ramuwar gayya a Isra'ila
Yadda makamai masu linzami da Iran ta harbo ke sauka a birnin Tel Aviv, kasar Isra'ila. Hoto: MENAHEM KAHANA / Contributor
Source: Getty Images

Al-Jazeera ta wallafa cewa an kuma ji karar fashe-fashe a yankin Gush Dan bayan sojojin Isra’ila sun fitar da gargadi kan shigowar makamai daga Iran.

Iran ta yi ruwan makamai a Isra'ila

CNBC ta wallafa cewa rundunar IRGC ta bayyana cewa makaman roka da ta harba sun kai hari kan wuraren soji da tsaro fiye da 100 a tsakiyar yankunan Isra’ila.

Ta ce an kai hare-haren ne domin daukar fansa kan mutuwar Larijani, dansa da kuma hadiminsa da aka kashe.

Rahotanni sun nuna cewa rundunar ta kuma yi amfani da jiragen yaki marasa matuki wajen kai farmaki a birnin Tel Aviv da wasu sassan tsakiyar Isra’ila.

Jami’an agajin gaggawa sun tabbatar da cewa mutane biyu sun mutu sakamakon harin makami mai linzami da aka kai kusa da birnin.

Iran ta fadada hare-hare

Baya ga Isra’ila, Iran ta kai hare-hare kan wasu wurare masu alaka da Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya yayin da yakin ke ƙazanta.

Kara karanta wannan

Rudani: Shugaban majalisar tsaron Iran ya fitar da sanarwa bayan Isra'ila ta ce ta kashe shi

Rahotonni sun ce an harba jiragen yaki marasa matuki masu dauke da abubuwan fashewa zuwa ofishin jakadancin Amurka da ke Baghdad

Wannan lamarin da ya janyo kararrawar gaggawa da kuma fashewa kusa da harabar ofishin jakadancin.

Iran ta ce ba za ta hakura da mayar da martani ba
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian a yayin wani taro Hoto: Masoud Pezeshkian
Source: Getty Images

A wani bangare, Firaministan Australia, Anthony Albanese, ya ce an harba wani makami kusa da sansanin sojin kasarsa a Hadaddiyar Daular Larabawa, amma babu wanda ya jikkata.

Wadannan hare-hare sun biyo bayan farmakin da Isra’ila ta kai a ranar Talata, 17 ga watan Maris, 2026 inda ta kashe Larijani, shugaban majalisar tsaron kasa ta koli ta Iran.

Haka kuma g kashe ɗansa, tare da Gholamreza Soleimani, jagoran wata kungiyar mayaka mai karfi da ke da alaka da IRGC a Iran.

Majalisar tsaron kasar Iran ta tabbatar da mutuwar Larijani, dansa Morteza Larijani, shugaban ofishinsa Alireza Bayat, da kuma wasu jami’an tsaro.

Saudiyya na fuskantar matsala a yakin Iran

A baya, mun wallafa cewa Saudiyya ta kakkabo makami mai linzami wanda baraguzansa suka fada kusa da sansanin sojin saman Amurka dake Al-Kharj a safiyar Laraba, 18 ga watan Maris, 2026.

Kara karanta wannan

Duk da ba ya Najeriya, Zulum ya aiko da sako bayan tagwayen bama bamai a Maiduguri

Baraguzan makaman Iran na ci gaba da lalata gine-gine da kayayyakin more rayuwa a sassan kasar Saudiyya, kamar matatar man Aramco tun bayan fara ganin a karshen Fabarairu.

A yayin da hare-haren ke ƙara ƙamari a Gabas ta Tsakiya, an dakatar da sufurin jiragen sama a Dubai bayan gobarar da hare-haren jirage marasa matuka na Iran suka haddasa a yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng