Babbar Matsalar da Kasar Saudiyya Take Fuskanta a Yakin Amurka da Iran
- Saudiyya ta kakkabo makami mai linzami wanda baraguzansa suka fada kusa da sansanin sojin saman Amurka dake Al-Kharj a safiyar Laraba
- Baraguzan makaman Iran na ci gaba da lalata gine-gine da kayayyakin more rayuwa a sassan kasar Saudiyya, kamar matatar man Aramco
- An dakatar da sufurin jiragen sama a Dubai bayan gobarar da hare-haren jirage marasa matuka na Iran suka haddasa a yayin yaki da Amurka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Saudiyya - Ma’aikatar tsaron ƙasar Saudiyya ta sanar cewa dakarun tsaronta sun yi nasarar kakkabo wani makami mai linzami da aka harba zuwa gundumar Al-Kharj.
Baraguzan makamin da aka tarwatsa a sararin samaniya sun faɗa kusa da sansanin sojin saman Yarima Sultan, wanda ke karbar bakuncin dakarun Amurka.

Source: Getty Images
An kakkabo jiragen Iran a Saudiyya

Kara karanta wannan
Ban da hare haren Iran, an gano wata barazana da sojojin Amurka ke fuskanta a Gabas
Wannan babban sansani ya dade yana fuskantar hare-hare akai-akai tun bayan barkewar yaƙin Amurka da Isra’ila da ƙasar Iran a ranar 28 ga Fabrairu, 2026, kamar yadda Aljazeera ta rahoto.
Rahotanni sun nuna cewa a iya safiyar yau Laraba, an kuma kakkabo wasu jirage marasa matuƙa guda 13 a lardin Gabas na ƙasar.
Faduwar baraguzan makamai masu linzami ko na jirage marasa matuka da Iran ke harbawa, ya zama babbar matsala ga Saudiyya, domin yana lalata kayayyaki da ma jikkata mutane.
Tarihin fadowar baraguzan makamai a Saudiyya
Tun farkon wannan yaƙi, Saudiyya ta fuskanci hare-hare da dama daga Iran, kuma ko da yake fannin tsaronta na kakkabe yawancin makaman, wasu sassan na faɗowa ƙasa.
Ga yadda jerin abubuwan suka faru:
- 2 ga Maris, 2026: Dakarun Saudiyya sun kakkabo jirage marasa matuka guda biyu kusa da matatar man fetur ta Aramco Ras Tanura. Baraguzan jiragen sun haddasa gobara tare da jawo dakatar da aiki a matatar na ɗan lokaci.
- 10 ga Maris, 2026: Bayan kakkabe wasu makamai, wani jirgi mara matuƙi da aka harbo ya faɗa wani yanki na garin a Al-Zulfi. An samu lalacewar gine-gine amma ba a rasa rai ba.
- 5 ga Maris, 2026: An kakkabo wasu makamai masu linzami (cruise missiles) guda uku a wajen birnin Al-Kharj, wanda baraguzan ya fado kasa, ya yi barna, in ji rahoton Iran International.

Kara karanta wannan
Iran ta yi ruwan bama bamai a tsakiyar Isra'ila bayan kisan Larjani, an kiɗima Yahudawa
Wannan wasu misalai ne kawai daga cikin jerin hare-haren makamai ko jirage marasa matuka da Saudiyya ta tare, kuma baraguzan suka fado kasa.

Source: Getty Images
Harin jirgin Iran ya haddasa gobara a UAE
Amma a ƙasashen Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), an samu rahotannin yadda ragowar makaman da aka kakkabo suka yi sanadiyyar mutuwar mutane ko haddasa gobara mai girma.
A ranar Talata, BBC ta rahoto cewa babbar tasha kuma rumbun ajiyar man Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), Fujairah, da filin jirgin Dubai sun sake fuskantar harin jirage marasa matuka.
Rahoton ya nuna cewa an dakatar da sauka da tashin jirage a ranar Litinin bayan gobara ta tashi a kusa da filin jirgin, sakamakon hare-haren Iran.
Iran ta lalata jiragen Amurka a Saudiyya
A wani labari, mun ruwaito cewa, an samu karin hare-haren dakarun Iran kan sansanin sojan Amurka bayan, inda aka ce sun lalata jiragen yaki biyar a kasar Saudiyya.
Runudnar sojin Amurka da ke kula da Gabas ta Tsakiya bata yi karin bayani ba game da harin da aka ce Iran ta kai kan jiragenta a yankin.
Labarin kai harin ya fito ne bayan shugaba Donald Trump ya yi ikirarin cewa ya kai hari kan wani tsibirin da Iran ke hako danyen mai cikin dare.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng