Abin da Muka Sani game da Soleimani, Babban Jami'in Iran da Isra'ila Ta Kashe

Abin da Muka Sani game da Soleimani, Babban Jami'in Iran da Isra'ila Ta Kashe

Iran - Rundunar sojojin Iran (IRGC) ta sanar da kisan daya daga cikin manyan kusoshinta, Birgediya Janar Gholamreza Soleimani, wanda shi ne shugaban dakarun sa-kai na Basij.

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Sanarwar, wadda aka fitar a ranar Talata, ta bayyana cewa Janar Soleimani ya riga mu gidan gaskiya ne sakamakon wani hari na Amurka da Isra'ila.

Rundunar sojojin Iran (IRGC) ta sanar da kisan daya daga cikin manyan kusoshinta, Birgediya Janar Gholamreza Soleimani, wanda shi ne shugaban dakarun sa-kai na Basij.
Birgediya Janar Gholamreza Soleimani, shugaban dakarun sa-kai na Basij da Isra'ila ta kashe. Hoto: Morteza Nikoubazl/NurPhoto via Getty Images
Source: Getty Images

Iran: Kisan Gholamreza Soleomani da Ali Larijani

Janar ɗin, wanda ke da shekaru 62 a duniya, ya kasance babban jigo a tsarin tsaron cikin gida na Iran na tsawon shekaru shida da suka gabata, cewar rahoton The Wall Street Journal.

Baya ga kisan Soleimani, gwamnatin Iran ta kuma tabbatar da wani babban rashi a safiyar yau Laraba, inda aka sanar da kisan Ali Larijani.

Kara karanta wannan

Rudani: Shugaban majalisar tsaron Iran ya fitar da sanarwa bayan Isra'ila ta ce ta kashe shi

Larijani ya kasance babban sakataren majalisar tsaro na ƙasa, kuma ɗaya daga cikin fitattun 'yan siyasa dake da tasiri sosai a manufofin tsaron Iran.

Muhimman abubuwan sani game da Soleimani

Ga wasu muhimman abubuwan sani game da marigayi Soleimani:

1. Soleimani: Daga ɗan sa-kai ziwa janar ɗin soja

Tarihin rayuwar Gholamreza Soleimani ya nuna irin yadda ya sadaukar da rayuwarsa ga tsarin juyin juya halin Iran.

An haife shi a shekarar 1964 a birnin Farsan dake lardin Chaharmahal da Bakhtiari.

Ya fara tafiyarsa a harkar soja ne tun yana matashi ɗan shekara 17, inda ya shiga yaƙin Iran da Iraki (1980-1988) a matsayin ɗan sa-kai.

Duk da cewa yana ɗauke da suna ɗaya da marigayi Qassem Soleimani, tsohon shugaban rundunar Quds da Amurka ta kashe a 2020, babu wata alaƙa ta jini a tsakaninsu.

2. Daukakar Soleimani a rundunar tsaron Iran

A lokacin yaƙin na shekaru takwas, Soleimani ya shiga manyan shirin hare hare daban-daban kamar su Operations Tariq al-Qods da Beit ol-Moqaddas, inda ya nuna bajinta har ya zama kwamandan bataliya.

Kara karanta wannan

Duk da ba ya Najeriya, Zulum ya aiko da sako bayan tagwayen bama bamai a Maiduguri

Bayan kammala yaƙin, ya ci gaba da riƙe manyan muƙamai na shiyya-shiyya a ƙarƙashin rundunar IRGC.

A shekarar 2017 ne aka ƙara masa girma zuwa matsayin Birgediya Janar, kamar yadda rahoton Aljazeera ya nuna.

Baya ga kishin ƙasarsa, Soleimani babban masani ne, inda yake da digiri a fannin tarihi daga Jami'ar Isfahan, kuma yana kan karatun digirin-digirgir a fannin tarihin Musulunci kafin rasuwarsa.

3. Tasirinsa a matsayin shugaban Basij

A ranar 2 ga Yuli, 2019, jagoran juyin juya halin Musulunci, Ayatollah Ali Khamenei, ya naɗa Soleimani a matsayin shugaban dakarun Basij.

Basij wata runduna ce ta sa-kai dake ƙarƙashin IRGC, wadda aka ɗora wa nauyin tabbatar da tsaro a kowane lungu da saƙo na ƙasar Iran.

Babban aikin da aka ba shi shi ne ya raya "al'adun gwagwarmaya" da kuma tabbatar da cewa matasan Iran sun duƙufa ga koyarwar juyin juya hali.

Gholamreza Soleimani ya rike manyan mukamai a fannin tsaron Iran kafin mutuwarsa.
Birgediya Janar Gholamreza Soleimani, shugaban dakarun sa-kai na Basij da Isra'ila ta kashe. Hoto: ATTA KENARE/AFP via Getty Images
Source: Getty Images

4. Sukar da Soleimani ya sha a duniya

To sai dai kuma, jagorancin Soleimani ya fuskanci suka mai tsanani daga ƙasashen duniya sakamakon yadda dakarun Basij suka murƙushe zanga-zangar adawa da gwamnati.

Kara karanta wannan

Bukukuwan Sallah: Jerin gwamnonin Arewa 5 da za su biya albashin Maris da wuri

Musamman a watan Nuwamban 2019, dakarun nasa sun yi amfani da ƙarfin soja wajen kashe masu zanga-zanga, kamar yadda wani rahoto da aka wallafa a shafin WikiPedia ya nuna.

Wannan ya sa ƙasashe irin su Amurka, Kanada, Burtaniya, da Tarayyar Turai (EU) suka sanya masa takunkumi mai tsanani a shekarar 2021.

Kisan Soleimani da Larijani ya bar babban gibi a tsarin mulki da tsaron ƙasar Iran, yayin da duniya ke zuba ido ganin matakin da Iran za ta ɗauka wajen mayar da martani a wannan yaƙi da ke ƙara ruruwa.

Isra'ila ta kashe kwamandojin Iran

A wani labari, mun ruwaito cewa, Isra'ila ta kashe Birgediya Janar Abdullah Jalali Nasab da Amir Shariat a wani harin sama da ta kai kan cibiyar leken asiri a Tehran.

Wadannan kwamandoji ne ke da alhakin nazarin bayanan sirri na yaki da Isra'ila kuma kisan su babban koma-baya ne ga tsaron Iran.

Kasar Iran ta rasa manyan kwamandojin tsaro da suka hada da Ministan Tsaro da Shugaban IRGC tun bayan barkewar wannan babban yaki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com