Yaƙin Iran da Isra'ila Ya Tsaya wa Trump a Wuya, Ya Faɗi Alherin Kawo Karshen Rikicin

Yaƙin Iran da Isra'ila Ya Tsaya wa Trump a Wuya, Ya Faɗi Alherin Kawo Karshen Rikicin

  • Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi magana kan tasirin da yakin Iran da Isra'ila ke yi kan farashin mai a duniya
  • Trump ya ce farashin mai zai ragu sosai bayan yaƙin Iran ya ƙare, duk da tsadar man fetur da ake fama da ita yanzu
  • Yaƙin da ake yi da Iran ya haifar da tashin farashin mai, yayin da jiragen dakon mai suka makale a mashigan Hormuz

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, US - Shugaban Donald Trump ya yi albishir kan saukar farashin mai a duniya yayin da ake yaki a Gabas ta Tsakiya.

Trump ya nuna cewa farashin mai zai sauka cikin sauri bayan kammala yaƙin da ake yi da Iran a yankin Gabas ta Tsakiya.

Trump ya magantu kan saukar farashin mai a duniya
Shugaba Donald Trump na kasar Amurka. Hoto: Al Drago/Bloomberg.
Source: Getty Images

Albishir daga Trump kan farashin mai a duniya

Kara karanta wannan

Wani daraktan tsaron Amurka ya yi murabus kan yaki da Iran, ya tona asirin Trump

Trump ya ce ba sai ya jira shawarar masu ba shi shawara ba domin ya san halin da ake ciki, yana mai jaddada cewa farashin kaya da hauhawar farashi za su ragu, cewar Fox News.

A halin yanzu, farashin galan ɗaya na man fetur ya kai kusan $3.72 a faɗin ƙasar, sakamakon tasirin rikicin da ake yi da Iran.

Trump ya jaddada cewa abin da ya fi muhimmanci shi ne hana Iran mallakar makamin nukiliya, yana gargadin cewa hakan zai iya jefa Gabas ta Tsakiya cikin haɗari.

Ya kuma bayyana cewa an lalata rundunar ruwan Iran, amma har yanzu jiragen dakon mai sun kasa wucewa ta mashigan Hormuz saboda tsoron nakiyoyi.

Shugaban ya ce Amurka ta shirya taimakawa da rakiyar jiragen ruwa da inshorar gwamnati, domin tabbatar da tsaron zirga-zirgar mai a yankin.

Yakin Iran da Isra'ila ya taba tattalin arzikin kasashen duniya da dama
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu da sabon jagoran addini a Iran, Mojtaba Khamenei. Hoto: Gil Cohen-Magen.
Source: Getty Images

Kasashen da ke dogaro da mashigan Hormuz

Trump ya kuma tattauna batun China, yana mai cewa ƙasar na samun yawancin man fetur daga yankin, yana ƙorafin cewa Amurka na kare su ba tare da buƙata ba.

Ya ce Japan ma na dogaro sosai da mashigan Hormuz wajen samun mai, yana nuna rashin jin daɗi kan yadda Amurka ke ɗaukar nauyin kare waɗannan hanyoyi.

Kara karanta wannan

Abin boye ya fito; Gargadin da aka yi wa Trump kafin fara yaki da Iran

A ƙarshen mako, Trump ya buƙaci ƙasashen NATO da Japan da Koriya ta Kudu su taimaka wajen rakiyar jiragen ruwa a yankin amma babu wanda ya amince.

Daga baya, ya sake nuna damuwa kan rashin goyon bayan ƙawayen Amurka, yana mai cewa ya kamata su nuna godiya tare da bayar da cikakken haɗin kai.

Martanin Trump da Kent ya yi murabus

Mun ba ku labarin cewa shugaban Amurka Donald Trump ya mayar da martani kan murabus din babban jami’in yaki da ta’addanci Joe Kent.

Kent ya yi murabus ne daga mukaminsa ne saboda adawa da harin da Amurka da Isra'ila ke yi kan Iran wanda ya jawo suka daga ƙasashen daban-daban.

Trump ya bayyana cewa tun farko yana ganin Kent mai rauni ne wajen tsaro, yana mai cewa bai san shi sosai ba duk da ya yi tsammanin mutumin kirki ne da farko.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.