Saudiyya da Qatar Sun Sake Sabon Lale, Sun Yunkuro kan Batun Yakin Iran da Amurka
- Saudiyya da Qatar sun sake tattaunawa kan yakin da ke gudana tsakanin Amurka, Isra'ila da Jamhuryar Musulunci ta Iran
- Ministan cikin gida na Saudiyya, Abdulaziz bin Saud bin Nayef ya yi magana da takwaransa na Qatar kan tasirin yakin a Gabas ta Tsakiya
- Wannan na zuwa ne yayin da yakin Iran da Amurka ya shiga rana ta 18, lamarin da ke kara zama barazana ga yankin ciki har da Saudiyya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Saudi Arabia - Kasashen Saudiyya da Qatar sun sake tattaunawa domin duba yadda za su tunkari yakin da ke kara zafi tsakanin Amurka, Isra'ila da Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Wannan yaki, wanda aka fara a ranar Asabar, 28 ga watan Fabrairu, 2026, na ci gaba da kara jefa yankin Gabas ta Tsakiya cikin tashin hankali da rashin kwanciyar hankali.

Kara karanta wannan
China ta shirya kai dauki, ta bayyana tallafin da za ta tura kasar Musulunci ta Iran

Source: Getty Images
Ministocin Saudiyya da Qatar sun yi waya
Tashar Al-Jazeera ta rahoto cewa ministocin cikin gida na Saudiyya da Qatar sun fara tattaunawa domin sake duba matakan da suka dauka don kaucewa tasirin wannan yaki.
Bayanai sun nuna cewa Ministan cikin gida na Saudiyya, Abdulaziz bin Sau bin Nayef ya tattauna kan tasirin wannan yaki da takwaransa na Qatar, Sheikh Khalifa bin Hamad Al Thani ta wayar tarho.
A wata sanarwa da ya fitar, Abdulaziz bin Saud ya ce tattaunawar ta mayar da hankali ne kan tasirin tsaro da halin da ake ciki a yankin Gabas ta Tsakiya sakamakon yakin da ke gudana.
Ya ce:
“Mun tattauna batun tsaro da abubuwan da ke faruwa a yanzu, musamman hare-haren da Iran ke kai wa kasashen yankin Tekun Fasha da sauran sassan yankin Gabas ta Tsakiya."
Saudiyya ta jaddada goyon baya ga Qatar
Ministan ya kuma jaddada cewa Saudiyya tana nan tare da Qatar wajen tabbatar da tsaro da kare rayukan mazauna kasar da baki da ke cikinta.

Kara karanta wannan
To fa: Musayar wutar da ake tsakanin Amurka, Isra'ila da Iran ta shiga wani muhimmin mataki
Ya bayyana cewa masarautar Saudiyya za ta ci gaba da hada kai da kasashen yankin domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, cewar Vanguard.

Source: Getty Images
Saudiyya ta tattauna da UAE
Rahotanni sun kuma nuna cewa Abdulaziz bin Saud ya yi irin wannan tattaunawa ta waya da mataimakin firaminista kuma ministan harkokin cikin gida na Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), Saif bin Zayed Al Nahyan.
Wannan na zuwa ne yayin da yakin da ke tsakanin Amurka, Isra’ila da Iran ke kara tada hankula a Gabas ta Tsakiya, lamarin da ke sa kasashen yankin ke kara karfafa hadin gwiwar tsaro domin dakile yaduwar rikicin.
Iran ta aika sako ga kasashen musulmi
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin kasar Iran ta ja hankalin Saudiyya da sauran kasashen musulmi da ke yankin Gabas ta Tsakiya kan yakin da ke gudana.
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta nuna damuwa kan abin da ta bayyana a matsayin rashin nuna goyon baya daga yawancin ƙasashen Musulmi a yakin da take da Amurka da Isra'ila.
Gwamnatin ta bayyana cewa juriyar da Iran ke nunawa kan hare-haren Amurka da Isra’ila, ta samo asali ne daga kokarinta na kare muradun duniyar Musulmi.
Asali: Legit.ng