Trump Ya Yi Magana da Babban Jigo a Tsaron Amurka Ya Yi Murabus saboda Yaki da Iran
- Shugaban Amurka Donald Trump ya mayar da martani kan murabus din babban jami’in yaki da ta’addanci Joe Kent
- Kent ya yi murabus ne daga mukaminsa ne saboda adawa da harin da Amurka da Isra'ila ke yi kan Iran
- Trump ya bayyana cewa tun farko yana ganin Kent mai rauni ne wajen tsaro, yana mai cewa bai san shi sosai ba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Washington DC, US - Shugaban Amurka Donald Trump ya yi martani kan murabus din babban jami’in yaki da ta’addanci, Joe Kent
Majiyoyi sun tabbatar da cewa Kent ya yi murabus ne saboda nuna adawa da matakin Amurka na kai hari kan Iran.

Source: Twitter
Legit Hausa ta samu martanin Trump ne a wani faifan bidiyo da Fox News ta wallafa a yammacin yau Talata 17 ga watan Maris, 2026.
Musababbin murabus din Joseph Kent
Wannan martani na zuwa ne bayan Kent ya ajiye aikinsa saboda rashin amincewa da tsarin Trump na yakar Iran ba bisa ka'ida ba.
Joseph Kent ya yi murabus daga mukaminsa na shugaban cibiyar yaƙi da ta’addanci ta Amurka, kan yadda Donald Trump ke yaki da kasar Iran.
Tsohon daraktan ya zargi gwamnatin Trump da fara yaƙi da Iran sakamakon matsin lambar da ta samu daga ƙasar Isra'ila da wasu masu fada a ji.
A cikin wasiƙar da ya aika wa Trump, Kent ya gargaɗi Amurka cewa yaƙin Iran wata makarkashiya ce da aka shirya, kamar yadda aka yi a Iraki.

Source: Getty Images
Murabus din Kent: Martanin da Trump ya yi
Trump ya ce tun da farko yana kallon Kent a matsayin mai rauni a fannin tsaro, yana mai cewa bai san shi sosai ba, amma yana ganin mutum ne mai kirki a dabi’a.
Sai dai Trump ya ce bayan ya karanta bayanin da Kent ya fitar, ya fahimci cewa ya fi dacewa ya bar mukamin, saboda ya bayyana cewa Iran ba ta zama barazana ga tsaro ba.
Ya ce:
“Na dade ina tunanin cewa yana da rauni wajen tsaro. Rauni sosai a bangaren tsaro. Ban san shi sosai ba. Amma na ga kamar mutum ne mai kirki.
"Amma lokacin da na karanta bayaninsa, na fahimci cewa alheri ne ma ya fita, domin ya ce Iran ba ta zama wata barazana ba.”
Sai dai wasu na ganin murabus din Kent zai bar wagegen gibi a yaki da ta'addanci da Amurka ke yi saboda kwarewarsa, cewar The Hill.
Yakin Iran: Gargadin da aka yi wa Trump
An ji cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya samu gargadi kan abin da zai iya faruwa idan aka kai wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Majiyoyi sun bayyana cewa an sanar da shugaban na Amurka cewa akwai abubuwan da Iran za ta iya yi muddin aka kai mata hari.
Daga cikin abin da aka sanar da Trump shi ne Iran za ta iya rufe mashigar ruwa ta Hormuz wadda ke da matukar muhimmanci wajen jigilar kayan makamashi.
Asali: Legit.ng

