Wani Daraktan Tsaron Amurka Ya Yi Murabus kan Yaki da Iran, Ya Tona Asirin Trump

Wani Daraktan Tsaron Amurka Ya Yi Murabus kan Yaki da Iran, Ya Tona Asirin Trump

  • Joseph Kent ya yi murabus daga mukaminsa na shugaban cibiyar yaƙi da ta’addanci ta Amurka, kan yadda Donald Trump ke yaki da kasar Iran
  • Tsohon daraktan ya zargi gwamnatin Trump da fara yaƙi da Iran sakamakon matsin lambar da ta samu daga ƙasar Isra'ila da wasu masu fada a ji
  • A cikin wasiƙar da ya aika wa Trump, Kent ya gargaɗi Amurka cewa yaƙin Iran wata makarkashiya ce da aka shirya, kamar yadda aka yi a Iraki

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Amurka - Daraktan cibiyar tsaro da yaƙi da ta’addanci ta Amurka, Joseph Kent, ya girgiza gwamnatin Donald Trump bayan ya sanar da yin murabus daga muƙaminsa a yau Talata.

Kent ya bayyana cewa ba zai iya ci gaba da goyon bayan yaƙin da ake yi da ƙasar Iran ba, yana mai bayyana yaƙin a matsayin wanda aka ƙirƙire shi ba tare da wata gamsasshiyar hujja ta tsaro ba.

Kara karanta wannan

Trump ya yi magana da babban jigo a tsaron Amurka ya yi murabus saboda yaki da Iran

Wani babban jami'i a gwamnatin Amurka ya yi murabus daga mukaminsa saboda yaki da Iran
Joseph Kent, daraktan cibiyar yakin Amurka da ya yi murabus tare da Shugaba Donald Trump. Hoto: @joekent16jan19
Source: Twitter

Daraktan tsaro a Amurka ya yi murabus

A cikin wasiƙar murabus ɗinsa mai ban mamaki wadda ya aike wa shugaban ƙasa kuma ya wallafa a shafinsa na X, Kent ya jaddada cewa ƙasar Iran ba ta taɓa zama wata barazana ta kusa ga Amurka ba.

Ya ce a fili yake cewa Trump ya shiga yakin ne kawai sakamakon matsin lamba daga ƙasar Isra'ila da kuma ƙungiyoyin gwagwarmaya na Amurka masu goyon bayan Isra'ila waɗanda suke da iko sosai a fadar White House.

Kent ya ci gaba da bayyana cewa ko da yake yana goyon bayan manufofin harkokin waje na "America First" waɗanda Trump ya yi yakin neman zaɓe a kansu a shekarun 2016, 2020, da 2024, ya yi amanna cewa wannan yaƙin ya saɓa wa waɗancan manufofin.

Ya tunatar da shugaban cewa har zuwa watan Yunin 2025, Trump ya fahimci cewa yaƙe-yaƙe a Gabas Ta Tsakiya tarko ne da ke lakume rayukan jaruman sojojin Amurka tare da tafi da dukiyar ƙasar.

Kara karanta wannan

"Mun girgiza": Trump ya fadi abin da ya ba shi mamaki a yaki da Iran

Kent ya zargi Isra'ila da wasu 'yan Amurka

Kent ya yaba wa matakan soja da Trump ya ɗauka a baya, kamar kisan Qasem Soleimani da kakkabe ISIS, inda ya ce shugaban ya nuna zai iya amfani da ƙarfin soja ba tare da jawo Amurka cikin yaƙin da ba ya ƙarewa ba.

Sai dai ya zargi manyan jami'an Isra'ila da wasu kafafen yaɗa labarai na Amurka da ƙaddamar da yaƙin yaɗa labaran ƙarya domin yaudarar Trump ya yarda cewa Iran barazana ce, kuma kai hari a yanzu zai kawo nasara cikin sauri.

A matsayinsa na tsohon soja da ya yi aiki a fagen fama sau 11, kuma mijin jarumar sojar nan Shannon Kent da ta riga mu gidan gaskiya, Kent ya ce ba zai iya goyon bayan tura sababbin matasan Amurka su je su mutu a yaƙin da ba shi da amfani ga jama'ar Amurka ba.

An zargi Isra'ila ta matsa lamba ga Trump har ya shiga yaki da Iran.
Hagu zuwa dama: Shugaba Donald Trump, tsohon jagoran addinin Iran, Ayotallah Khamenei da Firayim Minista, Benjamin Netanyahu. Hoto: Chip Somodevilla, @khamenei_ir, JACK GUEZ/POOL via Getty Images
Source: Getty Images

An ba Trump muhimmiyar shawara

Ya kwatanta wannan yanayi da yaudarar da aka yi wa Amurka har ta shiga yaƙin Iraki wanda ya lakume rayukan sojoji.

Kara karanta wannan

'Ba Amurka ba ce,' an gano kasa 1 da take da makullin bude kasuwar mai ta duniya

Daga ƙarshe, ya yi kira ga Shugaba Trump da ya sake yin tunani tare da canza alkibla kafin ƙasar ta sake nutsewa cikin hargitsi da koma-baya.

Wannan murabus na Kent ya nuna fargabar dake cikin jami'an tsaro kan yadda yaƙin Iran zai iya shafar makomar Amurka a nan gaba.

Karanta wasikar a nan kasa:

Kasashe 7 sun ki amince wa da bukatar Trump

A wani labari, mun ruwaito cewa, wasu ƙasashen NATO sun yi watsi da kiran shugaban Amurka Donald Trump na neman su sa hannu a yaƙin da yake fafatawa da Iran.

Shugaba Trump dai ya bayyana cewa gwamnatinsa ta tuntuɓi ƙasashe bakwai inda take sa ran za su taimaka wajen samar da tsaro a mashigar ruwan Hormuz da Iran ta toshe.

Sai dai, bayan Japan, da Burtaniya, an samu karin kasashe biyar da suka bayyana cewa ba su iya tura jiragen yaƙi zuwa mashigar ruwan Hormuz ba, kamar yadda Trump ya bukata.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com