Hormuz: Kasashen Turai Sun Yanke Shawara kan Abin da Amurka Ta Nema a Yakinta da Iran
- Kasashen da ke karkashin kungiyar Tarayyar Tarayya sun kunyata bukatar Shugaba Donald Trump kan batun mashigar Strait of Hormuz
- A wani taro da suka gudanar, wakilan kasashen Turai sun ce suna mamakin abin da jiragen ruwansu za su yi, wanda na Amurka suka gaza
- Yakin Amurka, Isra'ila da Iran na ci gaba da zama baranzana ga tattalin arzikin duniya sakamakon tashin farashin danyen mai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Brussels - Kasashen Turai sun yi watsi da bukatar Shugaban Amurka, Donald Trump ta su tura jiragen ruwa da sojoji domin taimakawa wajen buɗe mashigar Strait of Hormuz da karfin tsiya.
Ministocin harkokin wajen ƙasashen da ke karkashin kungiyar Tarayyar Turai (EU) ne suka yanke wannan matsaya a taron da suka gudanar a birnin Brussels.
MTashar Al-Jazeera ta tattaro cewa a wannan taro, wakilan kasshen Turai sun tattauna kan tashin gwauron zabi da farashin fetur ya yi sakamakon yaƙin da Amurka da Isra'ila ke yi da Iran.

Kara karanta wannan
Duk da ba ya Najeriya, Zulum ya aiko da sako bayan tagwayen bama bamai a Maiduguri
Wace bukatar Trump ya turo Turai?
Tun farko, Trump ya bukaci ƙasashen da suka hada da Birtaniya, China, Faramsa, Japan da Koriya ta Kudu da kuma ƙasashen kawancen NATO, da su tura jiragen ruwa domin kare mashigar Hormuz.
A cewarsa, idan ƙawayen NATO ba su taimaka wajen kare mashigar ba, hakan na iya haifar da matsala ga makomar kawancen.
Turai ta nemi karin bayani kan yakin
Sai dai ministocin harkokin wajen EU sun bukaci ƙarin bayani daga Amurka da Isra’ila kan manufar yaƙin da kuma lokacin da za a kawo ƙarshensa kafin su yanke shawarar ko za su ba da goyon baya.
Ministan harkokin wajen Jamus, Johann Wadephul, ya bayyana cewa ƙasarsa ba ta da niyyar shiga wannan yaki.
Ya ce:
“Muna sa ran Amurka da Isra’ila su sanar da mu abin da suke yi, su kuma gaya mana ko sun cimma manufofinsu.”
Ya kara da cewa bayan an samu cikakken bayani, sai a tattauna tsarin tsaro na yankin Gabas ta Tsakiya tare da ƙasashen da ke makwabtaka da yankin.
Wane mataki NATO ta dauka?
A nasa bangaren, kakakin gwamnatin Jamus ya bayyana cewa wannan rikici ba yaƙin NATO ba ne, domin kawancen an kafa shi ne domin kare yankin mambobinsa.
Haka kuma ministan tsaron Jamus, Boris Pistorius, ya yi tambaya kan abin da Trump ke tsammani ƙananan jiragen ruwan Turai za su iya yi a mashigar Hormuz, cewar rahoton RFI Hausa.
Ya ce:
“Me Trump yake tsammanin wasu kaɗan daga cikin jiragen ruwan Turai za su yi a Hormuz wanda rundunar ruwan Amurka mai ƙarfi ba za ta iya yi ba?”

Source: Getty Images
An fara hurowa Trump wuta a Amurka
A wani rahoton, kun ji cewa shugabannin kamfanoni mai irin su ExxonMobil da Chevron sun gana da Ministan lmakamashi na Amurka, Chris Wright, da ministan cikin gida, Doug Burgum.
A taron, manyan shugabannin kamfanonin man feturin na Amurka sun gargaɗi Shugaba Donald Trump kan matsalar makamashi da ke kara tunkaro duniya saboda yakin Iran.
Sun ce tsaikon safarar mai da sauran kayan makamashi ta mashigar Hormuz zai haddasa rashin tabbas a kasuwar makamashi ta duniya, wanda zai shafi Amurka.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
