"Ba Mu Miƙa Wuya ga Azzalumai": Iran Ta Gindaya Sharadin Kawo Ƙarshen Yaƙi da Amurka
- Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian ya ce ba kasarsa ce ta jangwalo fara yaki da Amurka da Isra’ila ba
- Ya jaddada abin da ƙasarsa ke yi a yanzu shi ne kare kasa, wanda hakki ne na dabi’a da Iran ke da shi
- Ya nemi duniya ta yi Allah-wadai da abin da ya kira mamaya bayan harin haɗin gwiwa da Amurka da Isra'ila suka kai masu
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Kasar Iran – Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya bayyana cewa ƙasarsa ba za ta mika wuya ga duk wata barazana daga kasashen waje ba.
Ya tunatar wa duniya cewa ba Iran ce ta fara rikicin da Amurka da Isra’ila ba, illa suna zaman zamansu a far masu da hari.

Source: Twitter
Al-Jazeera ta wallafa cewa Pezeshkian ya ce kare kai daga duk wani hari ko mamaya hakki ne na dabi’a ga kowace kasa mai cin gashin kanta.
Za mu kare kanmu - Shugaban Iran
Middle Eye East t wallafa cewa Shugaban Iran, Pezeshkian ya kara da ce Iran na da kwarewa wajen kare kanta daga irin wannan barazana da Amurka da Isra'ila ke kai mata.
Ya ce amfani da sansanonin sojin Amurka da ke yankin domin kai wa Iran hari ko kuma tada zaune tsaye a dangantakarta da kasashen makwabta abu ne da ya kamata a dakatar da shi.
Shugaban ya kuma bayyana cewa ya tattauna wannan batu da takwaransa na Faransa, Emmanuel Macron, ta wayar tarho.
Yayin kiran, shugabannnin biyu sun yi musayar ra’ayi kan yadda za a shawo kan rikicin da ke kara kamari a yankin.
Kiran Iran ga kasashen duniya
A cewar Masoud Pezeshkian, ba za a iya samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Gabas ta Tsakiya ba, matukar ba a dauki matakin dakile abin da ya kira mamayar Isra’ila da Amurka kan kasarsa ba.

Source: Facebook
Ya jaddada cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta taba mika wuya ga masu masu zaluntar su ba.
Ya yi kira ga kasashen duniya da su yi Allah-wadai da wannan mamaya tare da matsa lamba kan masu kai harin su mutunta dokokin kasa da kasa.
Shugaban ya kara da cewa fara yaki bisa bayanan karya domin mamaye wata kasa dabi’a ce ta tsohon zamani, wadda bai kamata a rika yi a karni na 21 ba.
Pezeshkian ya ce maganar kawo karshen yaki ba ta da ma’ana matukar ba a tabbatar da cewa ba za a sake kai wa Iran hari a nan gaba ba.
Ya jaddada cewa sai an samu tabbacin samun tsaro mai dorewa ga kasarsa kafin maganar sulhu ta yi ma'ana a yakin da ake gwabzawa.
Amurka ta magantu kan sulhu da Iran
A baya, mun wallafa cewa Shugaba Donald Trump ya ce kasar Iran ta matsu domin a fara tattaunawa da Amurka game da yakin da ake yi da haɗin gwiwar Isra'ila.

Kara karanta wannan
To fa: Musayar wutar da ake tsakanin Amurka, Isra'ila da Iran ta shiga wani muhimmin mataki
Trump ya bayyana cewa har yanzu bai ga alamun cewa Iran ta shirya yin abin da ake bukata domin sulhu ba, inda ya ce yana tattaunawa da wasu ƙasashe kan Hormuz.
Sai dai Iran ta ce ba ta nemi a yi zaman sulhu ba, kuma ba za ta anemia na matuƙar Amurka da Isra'ila za su ci gaba da kai masu hare-hare da keta alfarmar kasarta.
Asali: Legit.ng

