Babbar Magana: An Kashe Kusan Duka Shugabannin Kasar Musulunci Ta Iran

Babbar Magana: An Kashe Kusan Duka Shugabannin Kasar Musulunci Ta Iran

  • Shugaba Donald Trump ya yi ikirarin cewa hare-haren Amurka da Isra'ila sun yi ajalin manyan jagorori na Jamhuriyar Musulunci ta Iran
  • Wannan na zuwa ne bayan Iran ta nada Mojtaba Khamenei a matsayin wanda ya gaji mahaifinsa da aka kashe, Ayatollah Ali Khamenei
  • A wata hira da aka yi da Trump yau Litinin, ya ce sun kashe rukunin farko na shugabannin Iran, sun tura rukuni na biyu lahira

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Amurka - Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya yi ikirarin cewa hare-haren kasarsa da na Isra'ila sun halaka kusan duka shugabannin Jamhuryar Musulunci ta Iran.

Trump ya ce luguden wutar da sojojin Amurka da kawarta Isra'ila suka yi a biranen Iran sun yi sanaidn mutuwar manyan shugabannin kasar, yana mai cewa kusan dukkan su sun rasa rayukansu.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: Ana cikin musayar wuta, an kama masu yiwa Iran zagon kasa a yaki da Amurka

Shugaban Amurka, Donald Trump.
Shugaban Amurka, Donald Trump lokacin da ya yi hira da yan jarida a filin jirgi Hoto: @Foxnews
Source: Twitter

Trump ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi da tashar talabijin ta Fox News oh yau Juma'a, 16 ga watan Maris, 2026.

Trump ya yi ikirarin kai hari wurin tarukan Iran

A cewar Trump, hare-haren da aka kai kan wasu tarukan shugabannin Iran sun yi sanadin hallaka su a yakin da ake ci gaba da yi a Gabas ta Tsakiya.

“Dukkan shugabanninsu sun mutu a iya bayanan da na samu. Mun hallaka rukunin farko, sannan rukunin na biyu ma an hallaka su, duk sun mutu.
"Daga baya rukunin na uku suka hadu, kuma ina ganin yanzu suna jin tsoron yin taro," im ji Shugaba Trump.

Furucin na Trump na zuwa ne a daidai lokacin da yaƙin da Amurka da Isra’ila ke yi da Iran ke ci gaba da tsananta, inda aka kai dubban hare-haren sama tun bayan fara rikicin a ranar 28 ga watan Fabrairu, 2026.

Kara karanta wannan

Tirkashi: Donald Trump ya yanke lokacin da yakin Iran da Isra'ila zai kare

Jami’an tsaron Amurka sun ce hare-haren sun lalata manyan cibiyoyin soji, makamai masu linzami da kuma wuraren ajiye makamai na Iran, in ji tashar Al-Jazeera.

Iran na ci gaba da mayar da martani

Duk da hare-haren, Iran ta sha alwashin ci gaba da mayar da martani ga Amurka da Isra’ila, ta#ina mai cewa ba za ta dakatar da hare-harenta ba har sai an kawo ƙarshen farmakin da ake kai mata.

Rikicin dai ya bazu zuwa wasu sassan Gabas ta Tsakiya, inda hare-haren makamai masu linzami da jiragen yaki ke ci gaba da janyo asarar rayuka da barna.

Khamenei.
Jagoran addinin Iran, Mojtaba Khamenei da shugaban Amurka, Donald Trump Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

Iran ta kuma kai hare-hare tsakiyar Isra'ila

A wani rahoton, kun ji cewa Iran ta harba makamai masu linzami zuwa kasar Isra'ila yayin da ake ci gaba da gwabza fada tsakanin Jamhuriyar Musulunci da Amurka, Isra'ila.

Akalla wurare 10 a tsakiyar Isra'ila ne makaman ko kuma baraguzan makaman da aka kakkabo suka afka wa ranar Litinin, 16 ga watan Maris 2026,

Rundunar 'yan sandan Isra'ila ta bayyana cewa ta tura ƙungiyoyin kwashe baraguzan makaman da suka faɗo, sannan ta yi kira ga jama'a da kada su kusanci wuraren da makaman suka faɗa

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262