Isra'ila Ta Yi Fariya, Ta Fadi Nasarar da Ta Samu a kan Fadar Ayatollah Khamenei

Isra'ila Ta Yi Fariya, Ta Fadi Nasarar da Ta Samu a kan Fadar Ayatollah Khamenei

  • Kasar Isra’ila ta ce rundunar sojinta ta lalata jirgin da ake dangantawa da marigayi jagoran Iran, Ayatollah Ali Khmanei
  • Ta bayyana haka bayan kusan mako uku da rasuwar jagoran da ya gamu da ajalinsa a harin Isra'ila da Amurka
  • Tana wannan fariya ne a yayin da Iran ta rike wuta, tana kai mata munanan hare-hare a babban birnin kasar Tel Aviv

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Israel – Rundunar sojin Isra'ila ta sanar da cewa ta lalata wani jirgin sama da ake alakanta shi da marigayi jagoran Iran, Ali Khamenei.

A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce jiragen yakin sojinta sun kai harin ne da cikin dare zuwa ranar Litinin.

Isra'ila ta yi iƙirarin kai hari Iran
Firaministan ƙasar Isra'ila, Benjamin Netanyahu Hoto: Benjamin Netanyahu
Source: Facebook

Al-Jazeera ta wallafa cewa an kai harin zuwa filin jirgin saman Mehrabad da ke babban birnin Tehran, inda aka yi barna sosai.

Kara karanta wannan

Bayan ta sha alwashin kashe Netanyahu, Iran ta kai farmaki muhimman wurare 2 a Isra'ila

Isra'ila ta kai hari Iran

Reuters ta wallafa cewa rundunar ta bayyana cewa harin ya lalata jirgin da ake zargin ana amfani da shi wajen gudanar da wasu muhimman tafiye-tafiye na shugabannin gwamnatin Iran.

Sojojin Isra’ila sun ce wannan mataki wani bangare ne na kokarin rage karfin Iran wajen tsara ayyukanta na soja da kuma hulda da kasashen da take kawance da su.

A cewar rundunar:

“Lalata jirgin na iya kawo cikas ga yadda shugabannin gwamnatin Iran ke hada kai da kasashen da suke kawance da su, da kuma kokarin kara karfin sojoji.”

Dalilan harin Isra'ila kan fadar Khamenei

Sanarwar ta kara da cewa harin zai iya rage karfin gwamnatin Iran wajen sake farfado da wasu muhimman ayyukan soji ko na tsaro da take kokarin ginawa.

Isra'ila ta samu lalata jirgin Khamenei
Marigayi Ayatollah Khamenei, Shugaban addini na Iran Hoto: : @khamenei_ir
Source: Twitter

Rundunar ta yi zargin cewa jirgin da aka lalata yana taka muhimmiyar rawa wajen tafiye-tafiyen shugabanni da muhimman jami’an gwamnati.

Ta ce tana ganin ana amfani da jirgin musamman a harkokin hulda da kawayen Iran a yankin Gabas ta Tsaki.

Kara karanta wannan

To fa: Musayar wutar da ake tsakanin Amurka, Isra'ila da Iran ta shiga wani muhimmin mataki

Zuwa yanzu, babu tabbacin wannan hari daga hukumomin Iran da ke ci gaba da kai munana hare-haren a sassan babban birnin Isra'ila, Tel Aviv.

No a safiyar wannan rana ta Litinin, 16 ga watan Maris, 2026, Iran ta kai hari Tel Aviv, lamarin da ya rikita Isra'ila, musamman mazauna yankin.

Iran ta farmaki Isra'ila da hatsabibin makami

A baya, mun wallafa cewa rahotanni sun nuna cewa Iran ta yi amfani da makamai mai linzami mai hadarin gaske da ta kira da Sijjil a kan Isra'ila a ranar Lahadi 15 ga Maris, 2026.

Masu bincike sun bayyana cewa makamin yana da gudun gaske, inda ya ke da karfin ikon zuwa Isra'ila daga Iran a cikin minti bakwai ba tare da ya samu matsala kowace iri ba.

Hakan na zuwa ne yayin da yakin da ake tsakanin Amurka, Isra'ila da Iran ke cigaba da rincabewa ba tare da alamun tsagaita wuta ba, bayan Yahudu da Nasara sun haɗe kai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng