'Ba Amurka ba ce,' An Gano Kasa 1 da Take da Makullin Bude Kasuwar Mai Ta duniya

'Ba Amurka ba ce,' An Gano Kasa 1 da Take da Makullin Bude Kasuwar Mai Ta duniya

  • Kamfanin Saudi Aramco ya kasa tabbatar da tashar da zai fitar da mai a watan Afrilu sakamakon ikon da Iran ke da shi kan mashigar Hormuz
  • Masana sun bayyana cewa ikon Iran na amfani da jirage marasa matuka zai sa yaƙinta da Amurka, Iran ya yi tsayi fiye da yadda Trump ke tsammani
  • Ana fargabar 'yan Houthi za su iya kai hari tashar Yanbu dake Saudiyya, wanda hakan zai katse hanyar karshe ta fitar da man fetur daga kasar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Saudiyya - Wata wasiƙa da kamfanin Saudi Aramco ya aika wa abokan huldarsa a makon nan ta nuna sabon yanayin da aka shiga, inda kamfanin ya ce ba shi da tabbas kan wace tashar jiragen ruwa zai yi amfani da ita wajen fitar da mai watan Afrilu.

Kara karanta wannan

Yaki da Iran: Shugabanni a Amurka sun fadawa Trump masifar da ke tunkaro duniya

Wasiƙar ta nuna cewa kamfanin zai iya loda man ne daga tekun Red Sea ko kuma daga yankin Tekun Fasha, lamarin da ya sa masu sayen man ganin cewa Iran ce, ba Amurka ba, ke da ikon yanke hukuncin yaushe za a buɗe kasuwar makamashi ta duniya.

Ana ganin cewa Iran ce take da ikon juya kasuwar mai ta duniya ba Amurka ba.
Wani na nuna mashigar Hormuz da ke kusa da gabar tekun Iran a jikin taswira. Hoto: JULIEN DE ROSA / AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Iran ce ke da makullin kasuwar mai

Duk da cewa Shugaba Donald Trump ya sha nanata cewa Amurka ta kusa yin nasara a wannan yaƙi da ke ƙara ruruwa, masana na ganin cewa akwai sauran rina a kaba, in ji rahoton Reuters.

A cewar rahoton, masana da shugabannin kamfanonin makamashi na Gabas ta Tsakiya sun yi gargaɗin cewa lallai sai Iran ta amince da yarjejeniya kafin zirga-zirga ta koma daidai a mashigar Hormuz.

Hukumar Makamashi ta Duniya (IEA) ta bayyana wannan rikici a matsayin mafi munin tarnaki da aka taɓa samu ga samar da mai da iskar gas a tarihin duniya, sakamakon rufe mashigar Hormuz da Iran ta yi.

Fargabar masana kan hare-haren Iran

Ikon da Iran take da shi na tura jirage marasa matuƙa masu rahusa ya ba ta damar gurgunta zirga-zirgar jiragen ruwa a wannan babbar mashiga, koda kuwa Amurka ta ayyana ƙarshen yaƙi.

Kara karanta wannan

Ana tsakiyar musayar wuta, Trump ya yi magana kan kawo karshen yaki da Iran

Wani babban jami'in makamashi a yankin Fasha ya bayyana cewa ba za su tura jiragen dakaransu ba har sai Iran ta ba da tabbacin cewa ba za ta farmake su ba, in ji rahoton jaridar The Dawn.

A cewar babban jami'in, rakiyar sojin ruwa da Amurka ke shirin bayarwa ba za ta iya tsayar da harin jirage mara matuka ko makaman Iran na cikin ruwa ba idan har Theran ba ta amince da sharuɗɗan zaman lafiya ba.

Kamfanin Aramko ya nuna shakkun fitar da mai a watan Afrilu saboda rikicin Gabas ta Tsakiya.
Navigator Terminals, wani babban rumbun ajiyar mai da ke kan hanyar River Thames a Landan, kasar Ingila. Hoto: Dan Kitwood/Getty Images
Source: Getty Images

Tashoshin man Larabawa a tafin hannun Iran

A ranar Asabar, jirage marasa matuƙa suka kai hari cibiyar loda mai ta Fujairah a ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), sa'o'i kaɗan bayan Amurka ta kai hari tsibirin Kharg na Iran.

Masana irin su Helima Croft daga RBC Capital sun bayyana cewa Iran na aika saƙo ne cewa babu tashar jirgin ruwa da take da tsaro a wannan rikicin, cewar rahoton Business Recorder.

Haka kuma, ana fargabar cewa 'yan tawayen Houthi na kasar Yemen, waɗanda ke samun goyon bayan Iran, za su iya kai hari tashar ruwan Yanbu ta ƙasar Saudiyya, wadda ita ce kaɗai hanyar da Saudiyya ke amfani da ita yanzu wajen fitar da mai.

Kara karanta wannan

Harin tsibirin Kharg: Shugaban Amurka ya ga abin da bai yi tsammani ba a yaki da Iran

Yaki da Iran: An gargadi Shugaba Trump

A wani labari, mun ruwaito cewa, manyan shugabannin kamfanonin man fetur na Amurka sun gargaɗi Donald Trump cewa matsalar makamashi da yaƙin Iran ya haddasa tana iya ƙara muni.

Shugabannin kamfanoni irin su ExxonMobil da Chevron sun gana da ministan makamashi na Amurka, Chris Wright, don fada wa gwamnati masifar da ke tunkaro kasar da duniya baki daya.

Shugabannin sun ce tsaikon safarar mai da sauran kayan makamashi ta mashigar Hormuz zai haddasa rashin tabbas a kasuwar makamashi ta duniya, wanda zai shafi Amurka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com