Yaki da Iran: Shugabanni a Amurka Sun Fadawa Trump Masifar da Ke Tunkaro Duniya

Yaki da Iran: Shugabanni a Amurka Sun Fadawa Trump Masifar da Ke Tunkaro Duniya

  • Manyan kamfanonin mai na Amurka sun gargaɗi Donald Trump kan ta'azzarar matsalar makamashi yayin da Amurkar da Iran suka ki yarda da zaman sulhu
  • Shugabannin kamfanonin sun yi gargadin cewa rufe mashigar Hormuz zai jawo rashin tabbas a kasuwar makamashi ta duniya, wanda zai shafi Amurka
  • Tun bayan ɓallewar yaƙin Gabas ta Tsakiya a ranar 28 ga Fabrairu, 2026, kusan mutane 3,750 ne aka tabbatar sun riga mu gidan gaskiya a yankin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Amurka - Manyan shugabannin kamfanonin man fetur na Amurka sun gargaɗi Shugaba Donald Trump cewa matsalar makamashi da yaƙin Iran ya haddasa tana iya ƙara muni.

Shugabannin kamfanoni irin su ExxonMobil da Chevron sun gana da Ministan lmakamashi na Amurka, Chris Wright, da ministan cikin gida, Doug Burgum, don fada masu masifar da ke tunkaro kasar da duniya baki daya.

Kara karanta wannan

'Ba Amurka ba ce,' an gano kasa 1 da take da makullin bude kasuwar mai ta duniya

Shugabannin kamfanonin man fetur na Amurka sun gargadi Trump kan yaki da Iran
Matatar man kamfanin Marathon Petroleum Corp's da ke Los Angeles, Arewacin Amurka. Hoto: David McNew/Getty Images
Source: Getty Images

Shugabanni sun gargadi Trump kan yaki da Iran

A cewar wadannan shugabanni, yaƙin da Trump ke yi da Iran zai ci gaba da jefa kasuwannin mai na duniya cikin halin ha-ula-i, kamar yadda The Wall Street Journal ta ruwaito.

Shugabannin sun ce tsaikon safarar mai da sauran kayan makamashi ta mashigar Hormuz zai haddasa rashin tabbas a kasuwar makamashi ta duniya, wanda zai shafi Amurka.

Sai dai, kafar watsa labarai ta Reuters ta bayyana cewa ba ta iya tantance gaskiyar wannan rahoto na WSJ ba zuwa yanzu.

Wannan gargaɗi na zuwa ne a daidai lokacin da kasashen biyu ke nuna taurin kai, ttare da ci gaba da kai wa juna farmaki.

Lalacewar maganar sulhun Amurka da Iran

Shugaba Trump ya bayyana cewa zai amince da sulhu ne kawai idan an samar da sharuɗɗa masu tsauri, ciki har da gargaɗin cewa lallai sai Iran ta janye aniyarta ta mallakar makamin nukiliya.

Kara karanta wannan

Manyan Kasashen duniya 2 da ke samun riba duk da yakin Iran, Amurka da Isra'ila

A gefe guda, Ministan wajen Iran, Abbas Araghchi, ya maida martani da cewa Iran ba ta nemi tattaunawar tsagaita wuta da Amurka ba, yana mai cewa Amurka ba za ta taba yin nasara a wannan "haramtaccen yaƙin da ta fara" ba.

Yayin da zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar ruwan Hormuz ta kusan tsayawa cik, ƙasashen Turai suna tattaunawa kan faɗaɗa ayyukan rundunar sojin ruwa ta Aspides domin samar da tsaro.

Masana sun yi gargadin cewa rufe mashigar ruwan Hormuz zai jawo tsadar makamashi
Wani na nuna mashigar Hormuz da ke kusa da gabar tekun Iran a jikin taswira. Hoto: JULIEN DE ROSA / AFP via Getty Images
Source: Getty Images

An rasa rayuka 3,750 a Gabas ta Tsakiya

Gwamnatin Trump na shirin sanar da kafa wata haɗakar ƙasashe a wannan makon domin raka jiragen ruwa ta cikin mashigar ruwan, cewar wani rahoto na BBC.

Tun bayan ɓallewar yaƙin a ranar 28 ga Fabrairu, 2026, sakamakon harin haɗaka na Amurka da Isra'ila, kusan mutane 3,750 ne aka tabbatar sun riga mu gidan gaskiya a faɗin yankin.

Wannan babban adadi na asarar rayuka tare da karyewar tattalin arziki ya jefa duniya cikin fargaba, musamman ganin yadda babu alamun sanyi a kalaman shugabannin biyu.

Shugaba Trump ya fallasa dabarar Iran

A wani labari, mun ruwaito cewa, Donald Trump ya gargaɗi duniya kan haɗarin amfani fasahar AI inda ya zargi Iran da ƙirƙirar hotunan yaƙi na ƙarya domin yaudarar duniya.

Kara karanta wannan

Za a yi ruwan bama bamai kan Iran, Amurka ta fadi halin da Khamenei yake ciki

Shugaban Amurka ya yi iƙirarin cewa hotunan taron magoya bayan sabon jagoran addinin Iran Mojtaba Khamenei da ake yadawa ƙirƙirar AI ce kawai.

Hukumar FCC ta yi barazanar soke lasisin kafafen yaɗa labaran da ba sa bayar da rahotannin da suka yi daidai da manufofin gwamnatin Shugaba Trump.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com