An Sanar da Yanayin da Jagoran Addinin Iran, Mojtaba Khamenei ke Ciki bayan Kai Masa Hari
- Gwamnatin Iran ta sake tabbatar da cewa jagoran kasar, Mojtaba Khamenei na nan cikin koshin lafiya duk da raunin da ya samu
- Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Arahhchi ya ce babu wata matsala dangane da yanayin lafiyar Mojtaba Khamenei bayan kai masa hari
- Wannan na zuwa ne bayan bayan Mojtaba ya fitar da rubutaccen jawabi na farko tun bayan nada shi a matsayin jagoran Iran
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Iran - Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya bayyana cewa babu wata matsala game da yanayin lafiyar jagoran addini na ƙasar, Mojtaba Khamenei.
Ministan ya ce duk da rahotannin da jami’an Amurka suka fitar cewa an ji masa rauni a hare-haren da aka kai kan Iran kwanakin baya, Mojtaba na nan cikin koshin lafiya.

Source: Twitter
Araghchi ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi a yau Asabar, 14 ga watan Maris, 2026, kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Trump ya fadi halin da Mojtaba Khamenei ke ciki bayan harin Isra'ila
Da yake martani kan rade-radin raunata jagoran Iran, Abbas Araghchi ya ce:
“Babu wata matsala a lafiyar sabon jagoran mu, ya fitar da saƙonsa jiya kuma zai ci gaba da gudanar da ayyukansa.”
Abin da Amurka ta ce kan lafiyar Khamenei
A ranar Juma’a, ministan tsaron Amurka Pete Hegseth ya ce ya samu bayanan cewa Mojtaba Khamenei ya ji rauni kuma wataƙila fuskarsa ta lalace sakamakon harin da aka kai kasar.
Tun bayan harin, Mojtaba Khamenei bai fito fili a bainar jama’a ba, wanda hakan ya kara rura wutar rahoton da ke nuna cewa ya ji rauni, cewar rahoton Al-Jazeera.
Sai dai gwamnatin Iran ta tabbatar cewa an ji masa rauni, amma ba ta bayyana cikakken bayani kan halin da yake ciki ba.
Jagoran Iran ya yi jawabin farko
Amma a ranar Alhamis, jagoran Iran ya fitar da wani rubutaccen saƙo ga al’ummar Iran inda ya yi alhinin mutuwar wasu daga cikin ‘yan uwansa.
A cik byin saƙon nasa, Mojtaba ya ce harin ya yi sanadiyyar mutuwar mahaifinsa, tsohon jagora Ayatollah Ali Khamene, matarsa, ‘yar’uwarsa, ɗanta, da kuma mijin ‘yar’uwarsa

Kara karanta wannan
"Dole mu dauki fansa," Jagoran Iran, Mojtaba Khamenei ya kada hantar Amurka da Isra'ila
Ya ce wadannan rashi da ya yi sun sa ya fi fahimtar halin da al’ummar Iran ke ciki tun bayan fara yakin.

Source: Getty Images
Mojtaba Khamenei ya kuma jaddada cewa ƙasar za ta ɗauki fansa kan waɗanda suka kashe ‘yan uwansa da sauran al'ummar Iran wannan yaƙi.
Yaƙin da Amurka da Isra’ila suka fara kan Iran ya zuwa yanzu ya janyo asarar rayuka da dama tare da jefa yankin cikin tashin hankali, yayin da har yanzu ba a ga alamar kawo ƙarshensa ba.
Iran ta gindaya sharuddan tsagaita wuta
A wani rahoton, kun ji cewa babban sakataren majalisar tsaron Iran, Ali Larijani, ya kalubalanci Shugaba Donald Trump kan bugun kirji game da yakin da ake yi.
Larijani ya bayyana cewa kasarsa ba za ta janye daga yaki ba har sai Amurka ta yi nadamar abin da ya kira babban kuskuren da ta yi na fara yaki.
Ya bayyana hakan ne a matsayin martani ga Trump, yana mai jaddada cewa Iran za ta ci gaba da gwagwarmaya har sai Amurka ta gane kuskuren matakin da ta dauka.
Asali: Legit.ng