Isra'la Ta Kashe Babban Kwamandan Iran, An Jero Kwamandojoji 3 da Suka Mutu a baya
- Isra'ila ta kashe Birgediya Janar Abdullah Jalali Nasab da Amir Shariat a wani harin sama da ta kai kan cibiyar leken asiri a birnin Tehran
- Wadannan kwamandoji ne ke da alhakin nazarin bayanan sirri na yaki da Isra'ila kuma kisan su babban koma-baya ne ga tsaron Iran
- Iran ta rasa manyan kwamandojin tsaro da suka hada da Ministan Tsaro da Shugaban IRGC tun bayan barkewar wannan babban yaki
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Iran - Rundunar sojin kasar Iran ta tabbatar da mutuwar Birgediya Janar Abdullah Jalali Nasab, wanda aka kashe yayin wani harin sararin samaniya da dakarun Isra'ila suka kai.
Sanarwar da sojin Iran suka fitar ta bayyana cewa Janar Nasab ya yi "shahada ne yayin da yake kare kasarsa" daga harin da suka kira na "yan sahyoniya."

Kara karanta wannan
To fa: Musayar wutar da ake tsakanin Amurka, Isra'ila da Iran ta shiga wani muhimmin mataki

Source: Twitter
Isra'ila ta kashe dakarun sojojin Iran
Wannan kisan na zuwa ne a matsayin wani babban koma-baya ga tsarin leken asirin kasar Iran, kamar yadda rahoton Aljazeera ya nuna.
Dakarun tsaron Isra'ila (IDF) sun tabbatar da nasarar kakkabe Janar Nasab tare da wani babban jami'in leken asiri mai suna Amir Shariat ta hanyar amfani da jiragen yakin IAF a birnin Tehran.
A sanarwar da ta fitar a shafinta na X, Isra'ila ta bayyana mutanen biyu a matsayin kashin bayan cibiyar leken asiri ta "Khatam al-Anbiya", sannan ta bayyana su a matsayin na-hannun-daman shugabannin gwamnatin Iran.
Manyan shugabannin sojin Iran da suka mutu
Tun farkon barkewar wannan yakin, Iran ta rasa manyan kusoshi a rundunoninta daban-daban. Ga jerin sunayen manyan kwamandojin da aka tabbatar da mutuwarsu zuwa yanzu:
- Abdolrahim Mousavi: Babban hafsan hafsoshin dakarun kasar Iran baki daya.
- Aziz Nasirzadeh: Ministan tsaro kuma mataimakin babban hafsan hafsoshin soji.
- Mohammad Pakpour: Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci (IRGC).
- Abdollah Jalali-Nasab: Babban jami'in leken asiri na cibiyar Khatam al-Anbiya.
- Amir Shariat: Babban jami'i a sashin bayanan sirri na gaggawa.

Source: Twitter
Mahimmancin harin ga tsaron Isra'ila
A cewar rahoton Asian Net News, dakarun IDF sun bayyana cewa Jalali-Nasab da Shariat an nada su ne a matsayin masu rikon kwarya bayan kisan magabacinsu, Saleh Asadi, a farkon farmakin da Isra'ila ta kira "Operation Roaring Lion."
Cibiyar Khatam al-Anbiya ita ce ke da alhakin tattara da kuma nazarin bayanan sirri wadanda shugabannin tsaron Iran ke amfani da su wajen tsara dabarun yaki da Isra'ila.
Kakakin rundunar sojin Isra'ila, Birgediya Janar Effie Defrin, ya bayyana cewa wannan samame na daya daga cikin gagarumin kamfe na ruguza ayyukan sojin Iran.
Ya kara da cewa tun farkon wannan fafatawar, daruruwan jiragen yakin Isra'ila sun kai hare-hare kan daruruwan wurare dake da alaka da gwamnatin Iran a fadin kasar, lamarin da ya jefa shugabancin kasar cikin babban kalubale.
Asali: Legit.ng
