Ana tsaka da Yakin Iran da Isra'ila, Bam Ya Tarwatse a Kusa da Makarantar Yahudawa
- Wani bam da ake zargin wani mutumi ya dasa, ya fashe a bangon makarantar Yahudawa da ke garin Amsterdam a ƙasar Netherlands
- Hukumomi sun bayyana cewa fashewar ta faru ne a gundumar Buitenveldert da ke kudancin Amsterdam, amma babu wanda ya ji rauni
- Dakarun 'yan sanda da jami'an hukumar kashe gobara sun isa wurin da wuri kuma tuni suka fara gudanar da bincike
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Amsterdam, Netherlands - An samu wata fashewar bam da daddare a bangon waje na wata makarantar Yahudawa a birnin Amsterdam na ƙasar Netherlands.
Sai dai rahotanni daga hukumomim kasar sun tabbatar da cewa babu wanda ya jikkata ko rasa rai sakamakon wannan ibtila'i.

Source: Getty Images
A rahoton The Washington Post, Magajin garin birnin, Femke Halsema, ta bayyana lamarin a matsayin “mummunan hari na tsoro”, tana mai cewa dole ne a kare al’ummar Yahudawa da ke zaune a birnin.

Kara karanta wannan
Luguden wutar Amurka da Isra'ila ya yi barna a kasar Musulunci ta Iran, sama da mutum 100 sun mutu
Jami'an tsaro sun fara bincike
Hukumomi sun bayyana cewa fashewar ta faru ne a gundumar Buitenveldert da ke kudancin Amsterdam.
Jami’an ‘yan sanda da na hukumar kashe gobara sun isa wurin cikin gaggawa domin gudanar da bincike, kamar yadda Channels tv ta ruwaoto.
A cewar Halsem, ginin wurin ya dan tabu kadan amma lamarin ya haifar da fargaba a tsakanin al’ummar Yahudawa.
Magajin Garin ta ce:
“Makaranta wuri ne da yara ya kamata su je su yi karatu cikin aminci da cikakken tsaro. Dole ne Amsterdam ta kasance wurin da Yahudawa za su rayu cikin aminci.”
An gano wanda ya da bam ɗin
‘Yan sanda sun ce kyamarorin tsaro (CCTV) sun dauki hoton wani mutum da ake zargi yana ajiye na’urar bam din a wajen makarantar kafin fashewar ta faru.
An fara bincike a hukumance domin gano wanda ke da hannu a lamarin, wanda bayanai suka nuna cewa ya faru ne a makon da ya shige.
Lamarin ya zo ne bayan wasu hare-haren dare da aka kai a gaban majami’ar Yahudawa a birnin Liege na ƙasar Belgium da kuma majami’a a tashar jiragen ruwa ta Rotterdam a Netherlands.
Firaministan Netherlands ya yi Allah wadai
Firaministan ƙasar Netherlands, Rob Jetten, ya bayyana harin a matsayin abin takaici sosai, yana mai cewa, “Kiyayyar Yahudawa ba ta da wuri a Netherlands.”
Ya kuma ce zai gana da shugabannin al’ummar Yahudawa domin kwantar da hankalinsu tare da tabbatar da tsaro.

Source: Getty Images
Ma’aikatar harkokin wajen Isra'ila ta ce irin waɗannan hare-hare na nuna cewa ƙiyayyar Yahudawa na ƙaruwa a Netherlands, tana mai kira ga gwamnatin ƙasar da ta ƙara ƙoƙari wajen magance matsalar.
Kasar Yahudawa, Isra'ila ta lashe malami
A wani labarin, kun ji cewa Isra'ila ta jikkata wani babban limami a masallacin Nabatieh al-Fawqa a hare-haren da take kai wa kan dakarun kungiyar Hezbollah a Lebanon.
Sheikh Hassan Ghandour ya rasu ne sakamakon raunukan da ya samu bayan wani harin sama da Isra’ila ta kai a gidansa.
Rahotanni daga yankin sun ce sojojin Isra’ila sun kai wasu hare-haren sama guda biyu kan garuruwan Qantara da Qabrikha a Kudancin Lebanon.
Asali: Legit.ng
