Tofa: Iran Ta Gagari Trump, Ya Fara Neman Dauki wajen Manyan Kasashen Duniya
- Iran na ci gaba da hana manyan jiragen ruwa na dakon kaya wucewa ta mashigar ruwa ta Hormuz sakamakon rikicin da ake yi a Gabas ta Tsakiya
- Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya sha yin barazana ga Iran kan kulle mashigar Hormuz saboda muhimmancin da take da shi
- Sai dai, duk da barazanar da Trump ke yi, Iran ta kafe kan bakanta na dakatar da zirga-zirgir manyan jiragen ruwa a mashigar
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Washington, Amurka - Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya sake yin magana kan bude mashigar ruwa ta Hormuz wadda Iran ta kulle.
Donald Trump ya yi kira ga sauran ƙasashe a da su tura jiragen yaƙi na ruwa domin taimaka wa wajen tabbatar da tsaron mashigar ruwa Hormuz.

Source: Getty Images
Shugaban na Amurka ya bayyana hakan ne a cikin sako da ya wallafa a shafinsa na Truth Social a ranar Asabar, 14 ga watan Maris 2026.
Iran ta kulle mashigar Hormuz
Kalaman na Trump na zuwa ne bayan Iran ta kulle mashigar ruwan wadda ta kasance babbar hanyar jigilar man fetur cga duniya sakamakom rikicin Gabas ta Tsakiya.
Sabon jagoran addini na Iran, Mojtaba Khamenei, ya sha alwashin ci gaba da kulle mashigar ta Hormuz domin matsawa Amurka lamba kan yakin da take yi da kasarsa.
Mashigar Hormuz tana ɗaya daga cikin muhimman hanyayoyin safarar makamashi na duniya, inda ake gudanar da gagarumin wani kason jigilar man fetur na duniya.
Fiye da gangar mai miliyan 20 ne ke ratsawa ta mashigar kowace rana, kusan kashi ɗaya cikin biyar na abin da duniya ke amfani da shi gaba ɗaya.
Katsewar zirga-zirga a mashigar ya riga ya janyo tashin farashin mai yayin da kasuwanni ke fargabar ƙarancin kayayyaki na dogon lokaci.
Wace bukata Donald Trump ya roka?
Shugaba Trump ya ce ƙasashe da dama za su iya haɗa kai da Amurka domin buɗe wannan hanyar ruwa ga jiragen dakon kaya na ƙasa da ƙasa.

Kara karanta wannan
Iran ta shiga matsala: Bataliyar sojojin Amurka mai hatsari ta bar Japan zuwa Gabas
“Ƙasashe da dama, musamman waɗanda ƙoƙarin Iran na rufe mashigar Hormuz ya shafa, za su turo jiragen yaƙi, tare da haɗin gwiwar Amurka, domin bude mashigar da kuma ba ta tsaro.” - Donald Trump
Ya ƙara da cewa ya kamata manyan ƙasashen tattalin arziki na duniya da wannan matsala ta shafa su bayar da tasu gudunmawar.
“Ina fatan China, Faransa, Japan, Koriya ta Kudu, Burtaniya da sauran ƙasashe, waɗanda wannan katsewa ta shafa, za su tura jiragen ruwan yaki zuwa yankin.”
- Donald Trump

Source: Facebook
Trump ya sha alwashin bude mashigar Hormuz
Hakazalika, Trump ya kuma sha alwashin tabbatar da cewa an bude mashigar ruwan ta Hormuz.
"Ta kowace hanya, nan ba da jimawa ba za mu sa mashigar Hormuz ta kasance a bude, cikon tsaro kuma kyauta."
- Donald Trump
Shugaban Amurka ya ki karbar shawarar Putin
A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin, ya ba Donald Trump shawara kan yadda za a kawo karshen yaki da Iran.
Putin ya ba da shawarar kwashe sinadarin uranium na Iran da aka inganta zuwa ƙasar Rasha a matsayin ɓangare na yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin.
Sai dai, shugaban kasar na Amurka ya sa kafa ya yi fatali da wannan shawarar da Putin ya gabatar masa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
