Wata Sabuwa: Ana cikin Gwabza Fada, Trump Ya Fadi Bukatar da Shugabannin Iran Suka Nema

Wata Sabuwa: Ana cikin Gwabza Fada, Trump Ya Fadi Bukatar da Shugabannin Iran Suka Nema

  • Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya sake yin ikirarin samun nasara a yakin da ake yi da Iran a yankin Gabas ta Tsakiya
  • Donald Trump ya bayyana cewa Amurka da Isra'ila sun yi nasarori girma kan Iran sakamakon hare-haren da suke kai wa
  • Hakazalika, shugaban kasar na Amurka ya bayyana abin da Iran ke nema wanda ya ce ko kadan ba zai amince da shi ba

​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Washington, Amurka - Shugaban kasar Amurka Donald Trump, sake yon magana kan yakin da kasarsa ke yi da Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Donald Trump ya bayyana cewa “an yi gagarumar nasara kan Iran” a yaƙin da Amurka da Isra’ila suke yi da ita.

Donald Trump ya ce Amurka ta yi nasara kan Iran
Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian da Shugaba Donald Trump na Amurka Hoto: @drpezeshkian, @RealDonaldTrump
Source: Twitter

Donald Trump ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na Truth Social a ranar Asabar, 14 ga watan Maris 2026.

Kara karanta wannan

Trump ya gano shugaban kasa 1 da zai iya taimakon Iran a yaki da Amurka, Isra'ila

Me Donald Trump ya ce Iran na nema?

Shugaban kasar na Amurka ya bayyana cewa Iran na son wata yarjejeniya da shi ba zai amince da ita ba, duk da cewa jami’an Iran sun yi alwashin ci gaba da fafatawa.

“Kafofin yaɗa labarai na ƙarya sun tsani bayar da rahoton yadda rundunar sojojin Amurka ta nuna ƙwazo a kan Iran, wadda aka riga aka yi wa kaca-kaca kuma take son shiga yarjejeniya, amma ba yarjejeniyar da zan amince da ita ba!”

- Donald Trump

Amurka ta kai sababbin hare-hare kan Iran

Kalaman na Trump sun zo ne bayan ya bayyana cewa Washington ta yi luguden bama-bamai a kan wuraren ayyukan sojoji a tsibirin Kharg na Iran, wanda shi ne cibiyar man fetur ɗin ƙasar.

Hakazalika ya kuma bayyana cewa rundunar sojojin ruwa ta Amurka za ta fara rakiya ga jiragen dakon mai ta mashigar ruwa ta Hormuz nan ba da jimawa ba.

Sai dai yayin da hare-haren Amurka a kan Iran suka ci gaba, Tehran ta ƙaddamar da wani sabon rukunin hare-hare na jirage marasa matuƙa da makaman linzami a kan Isra’ila da maƙwabtanta na yankin Gulf.

Kara karanta wannan

Da gaske Netanyahu ya bata yayin yakin Isra'ila da Iran? An samu bayanai

Amurka ta kai hare-hare kan Iran
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump Hoto: Donald J. Trump
Source: Facebook

An nuna goyon baya ga gwamnatin Iran

A gefe guda kuma, manyan jami’an Iran da dama sun halarci wata zanga-zangar nuna goyon baya ga gwamnati a Tehran ranar Juma’a, inda suka yi tattaki tare da masu zanga-zangar da ke ɗauke da kwalaye masu rubutun “Mutuwa ga Amurka” da “Mutuwa ga Isra’ila.”

Tashar NBC News ta ce babban jami’an diflomasiyyar Iran, Abbas Araghchi, ya bayyana a wannan makon cewa tattaunawa ba ta cikin tsarin da suke kai, kuma hare-hare za su ci gaba muddin ana buƙatar hakan..

“Ba na jin tattaunawa da Amurkawa tana cikin tsarin ayyukanmu kuma."

- Abbas Araghchi

Iran ta sha alwashi kan Amurka

A wani labarin kuma, kun ji cewa babban kwamandan rundunar sojojin Iran, Amir Hatami, ya sha alwashin daukar fansa kan nutsar da jirgin ruwan yakin Iran da Amurka ta yi.

Amir Hatami ya bayyana cewa nutsar da jirgin ruwan mai suna IRS Dena, ba abu ba ne da za su bari ya tafi a banza ba.

Babban kwamandan ya bayyana cewa sojojin da ke cikin jirgin an farmake su ne yayin da suke kan hanyar komawa gida.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng