Manyan Kasashen Duniya 2 da ke Samun Riba duk da Yakin Iran, Amurka da Isra'ila
Rikicin da ya ɓarke tsakanin Amurka da Isra’ila a gefe guda da Iran ya jefa yankin Gabas ta Tsakiya cikin yanayi mara dadi tare da jawo matsala ga kasuwar man fetur ta duniya.
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Kasar Iran – Yaƙin da Amurka da Isra'ila suka jawo ya tilasta dubunnan mutane barin muhallansu, yayin da kuma kasuwannin makamashi na duniya suka fara girgiza sakamakon tashin farashin mai.

Source: Getty Images
BBC Hausa ta wallafa cewa babban dalilin hauhawar farashin makamashin shi ne tsaikon jigilar mai da iskar gas da ake samu ta mashigar Hormuz.
Yakin Iran ya daga farashin mai
Mashigar na daya daga cikin hanyoyin ruwa mafi muhimmanci a duniya wajen jigilar makamashi musamman man fetur da iskar gas.
Wannan matsala ta sa farashin ganga ɗaya na mai ya tashi sosai, lamarin da ke iya amfani ga wasu ƙasashe masu fitar da mai.
Masana harkokin siyasa da tattalin arziki sun yi nuni da cewa rikicin Amurka da Isra'ila na iya zama wata dama ga Rasha da kuma kasar China.
Yadda Rasha da China ke morar yakin Iran
1. Rasha
Duk da cewa Iran na daga cikin manyan ƙawayen Moscow a fannin tsaro, sababbin abubuwan da suka faru a yankin sun haifar da wasu sauye-sauye a alakar.
A baya Iran ta taimaka wa Rasha da jirage marasa matuƙa samfurin Shahed da kuma fasahar ƙera su a shekarun 2022 da 2023 domin amfani a yaƙin Ukraine.
Sai dai wasu masana sun ce a yanzu Rasha ta kai matakin da za ta iya ƙera irin waɗannan jirage da kanta ba tare da dogaro da Iran ba.

Source: Facebook
Nicole Grajewski, wata masaniya kan harkokin ƙasa da ƙasa, ta ce sauya mayar da hankali ga rikicin Gabas ta Tsakiya na iya rage irin taimakon da Ukraine ke samu daga Amurka da ƙawayenta.
A cewarta, hakan na iya bai wa Rasha damar samun sauƙi a fagen daga, yayin da za a ci gaba da kai farmaki Ukraine.
Haka kuma tashin farashin mai na iya ƙara kuɗin shiga ga Rasha. Kasafin kuɗin ƙasar ya ginu ne kan farashin mai kusan Dala 59 kan kowace ganga.
Amma yanzu farashin ya haura Dala 100 a kasuwanni. Hakan na iya ba Moscow damar ƙara sayar da mai ga manyan abokan hulɗarta kamar China da Indiya.
2. China
Kwamred Sa'idu Bello, Mai sharhi ne a kan al'amuran Gabas ta Tsakiya. Ya shaidawa Legit cewa bayan Rasha, China ce ta biyu a cin moriyar yakin da ake yi da Iran.

Source: Getty Images
Ya kara da cewa:
"Wadanda suke cin moriyar yakin daga China sai Rasha. Sannan ita kanta hukumomin Iran sun bayar da sanarwa cewa duk kasar da ta mara masu baya a Gabas ta Tsakiya suka kori jami'an difomasiyya na Isra'ila daga kasashensu su ma za su iya wuce wa da jiragen mansu su sayar a kasashen duniya."
Kwamred Sa'idu Bello ya ce:

Kara karanta wannan
Yadda yakin Iran da Amurka zai shafi ibadun watan Ramadan, Umrah da aikin Hajjin 2026
"Turkiyya ma ta mara wa Iran baya, ta kuma ce ba za a sake amfani da wani wurinta ba a kai wa Iran hari. Domin suna ganin suna da kyakkayar alaka kuma kusan yawancin yan kungiyar NATO ba su mara wa Amurka da Isra'ila baya ba."
Ya kara da cewa dukkanin kasashen da za su mara wa Iran baya a yanzu ko ta fuskantar hana Amurka amfani da kasarsu wajen kai hari ko korar jami'an Isra'ila, za su samu cin moriyar wuce wa ta mashigar Hormuz.
Iran ta dauki sabon alwashi
A wani labarin, kun ji cewa a kwanakin baya ne dai babban jirgin ruwan yakin Amurka da ke tafiya a karkashin ruwa ya nutsar da wani jirgin ruwan yakin Iran a cikin teku.
Nutsar da jirgin ruwan mai dauke da ma'aikata 180 ya jawo an samu asarar rayukan wasu sojojin ruwa na Iran da ke cikinsa, lamarin da Iran ta ce ba za ta bari ba.
Babban kwamandan rundunar sojojin Iran, Amir Hatami, ya yi gargadin cewa ba za su kyale danyen aikin na kasar Amurka ya tafi a banza ba, saboda haka a zauna da shiri.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

