Amurka da Isra'ila Sun Yi Babbar Barna a Kasar Musulunci, Fiye da Mutane 1,400 Sun Rasu

Amurka da Isra'ila Sun Yi Babbar Barna a Kasar Musulunci, Fiye da Mutane 1,400 Sun Rasu

  • Hukumomin Lafiya a Iran sun fitar da alkaluman mutanen da hare-haren Amurka suka shafa tun daga ranar Asabar, 28 ga Fabrarairu, 2026 zuwa yau
  • Ma'aikatar Lafiya ta Iran ta bayyana cewa akalla mutane 1,444 ne suka mutu yayin da wasu fiye da 18,000 suka samu raunuka daban-daban
  • Wannan na zuwa ne yayin da yakin Amurka/Isra'ila da Iran ya kai rana ta 14, lamarin da ke kara zama barazana ga tattalin arzikin duniya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Iran - Ma’aikatar lafiya ta Iran ta bayyana cewa akalla mutane 1,444 sun mutu yayin da 18,551 suka jikkata sakamakon hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kai wa kasar tun daga ranar 28 ga Fabrairu 2026, lokacin da aka fara yakin.

Wannan adadi na nuna yadda yakin ya kara tsananta a cikin kwanaki kadan da suka gabata, yayin da hare-haren sama suka lalata wurare da dama a cikin Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Kara karanta wannan

Rana ta 14: Iran ta jikkata dubban 'yan Isra'ila, an ji babban kara a Tehran

Shugaban kasar Iran.
Shugaban kasar Musulunci ta Iran, Masoud Pezeshkian Hoto Anadolu
Source: Getty Images

An kashe sama da mutum 1,400 a Iran

Tashar Al-Jazeera ta tabbatar da wannan alkaluma na wadanda aka kashe a Iran a wani rahoto da ta wallafa yau Juma'a, rana ta 14 da fara yakin Gabas ta Tsakiya.

Rahotannin hukumomin lafiya na Iran sun nuna cewa mafi yawan wadanda abin ya shafa fararen hula ne, ciki har da mata da yara.

Tun daga farkon yakin, adadin wadanda suka mutu yana ci gaba da karuwa daga daruruwan mutane zuwa sama da dubu, yayin da dubban mutane ke ci gaba da karbar magani a asibitoci saboda raunuka daban-daba.

Amurka da Isra'ila sun tafka barna a Iran

Baya ga asarar rayuka, hare-haren sun kuma haddasa lalacewar asibitoci da cibiyoyin lafiya da dama, rushewar gine-gine da muhimman ababen more rayuwa da kuma matsanancin matsin tattalin arziki.

Yakin ya barke ne bayan sojojin Amurka da Isra’ila sun kaddamar da hare-haren sama a sassa da dama na Iran, ciki har da manyan birane kamar Tehran.

Kara karanta wannan

Kasashen da ke goyon Iran a yakin da ta ke da America da Isra'ila

Hare-haren sun nufi wuraren soji, cibiyoyin makamai da wasu muhimman gine-ginen gwamnati, lamarin da ya yi ajalin jagooran addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei.

Iran na ci gaba da kokarin maida martani

A martanin da ta yi, Iran ta kaddamar da hare-haren makamai masu linzami da jiragen yaki marasa matuki zuwa Isra’ila da wasu kasashen yankin da ke dauke da sansanonin sojin Amurka.

Wannan mataki ya kara fadada rikicin zuwa wasu sassan Gabas ta Tsakiya, lamarin da ya ja hankalin duniya gaba daya, cewar rahoton NBC News.

Shugabannin Isra'ila da Amurka.
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu da Shugaban Amurka, Donald J. Trump Hoto: Anadolu, @DonaldJTrump
Source: Getty Images

Tun daga wannan lokaci da aka fara yakin zuwa yau, hukumomin Iran sun tabbatar da mutuwar mutane 1,444 yayin da wasu 18,551 suka jikkata.

Iran ta jikkata dubban mutane a Isra'ila

A wani rahoton, kun ji cewa Gwamnatin Isra'ila ta bayyana adadin mutanen da suka samu raunaka sakamakon hare-haren da Iran ta kai kasar.

Ma'aikatar lafiyar Isra'ila ta bayyana cewa a cikin sa'o'i 24 da suka gabata, an kai mutane 179 da suka ji rauni zuwa asibitoci sakamakon rikicin da ake yi da Iran.

Daga cikin waɗanda ake yi wa magani a asibitoci, mutane huɗu suna cikin yanayi matsakaici, yayin da 157 suke cikin kyakkyawan yanayi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262