Shugaban Iran Ya Fadi Yawan Albashinsa da Yaki Ya Taba Tattalin Arzikin Kasar

Shugaban Iran Ya Fadi Yawan Albashinsa da Yaki Ya Taba Tattalin Arzikin Kasar

  • Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ya yi magana kan tattalin arzikin kasar yayin da ake ci gaba da yaki
  • Pezeshkian ya bayyana yawan albashinsa na shugaban kasa a wata ba saboda matsalar kudin kasar
  • Ya amince cewa matsin tattalin arziki ya sa mutane da dama sun nuna rashin jin dadi ga gwamnatin Iran

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Tehran, Iran - Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ya bayyana yawan albashin da yake dauka yayin da ake fama da yaki a kasar.

Shugaba Pezeshkian ya bayyana cewa albashinsa na shugaban kasa bai wuce dala $1,000 a wata ba sakamakon matsananciyar faduwar darajar kudin kasar.

Shugaban Iran ya fadi yawan albashinsa a kasar
Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian. Hoto: Anadolu Ajansi.
Source: Getty Images

Ya bayyana hakan ne yayin wata ziyara da ya kai lardin Golestan inda ya amince cewa tattalin arzikin kasar na cikin matsala, cewar The National.

Yawan albashi da shugaban Iran ke karba

Kara karanta wannan

Da gaske Netanyahu ya bata yayin yakin Isra'ila da Iran? An samu bayanai

Pezeshkian ya ce wasu ‘yan kasar Iran sun nuna rashin jin dadi da yadda gwamnati ke tafiyar da al’amura.

Ya kuma amince cewa a baya ma’aikata sun fi samun karfin saye idan aka kwatanta da halin da ake ciki yanzu.

Ya ce:

“Yanzu albashina a matsayin shugaban kasa kusan dala $1,000 ne a wata.”

Rahotanni sun nuna cewa mutane da dama a Iran na samun kudin shiga kasa da hakan.

A bara, an sanya mafi karancin albashi a kasar a kusan $3.76 a rana wanda ya jawo maganganu a fadin kasar baki daya.

Tun daga lokacin kuma darajar kudin Riyal ta ci gaba da faduwa sosai a kasuwar musayar kudade.

Shugaban Iran ya magantu kan halin tattalin arzikin kasar
Shugaba Masoud Pezeshkian na kasar Iran. Hoto: Anadolu.
Source: Getty Images

Abin da ya jawo zanga-zanga a kasar Iran

A watan da ya gabata, darajar kudin ta kai kusan rial miliyan 1.5 kan dala guda, wanda shi ne mafi muni a tarihin kasar.

Faduwar darajar kudin ta haifar da zanga-zanga mai tsanani a Iran kafin fara wannan yaki da ake yi da Isra'ila da ke samun goyon bayan Amurka.

Kara karanta wannan

Mojtaba Khamenei ya yi jawabin farko, ya faranta wa wadanda yakin Iran ya shafa

Masu fafutuka sun ce kusan mutane 7,000 ne suka mutu yayin matakan tsaro da gwamnati ta dauka domin dakile zanga-zangar.

Iran ta zargi Amurka da daukar nauyin zanga-zanga

Gwamnatin Iran ta zargi Amurka da Isra’ila da haddasa tarzoma ta hanyar goyon bayan masu zanga-zangar, cewar Middle East Monitor.

Sai dai yayin ganawarsa da 'yan gwagwarmaya a Golestan, shugaban ya dauki salo mai sauki inda ya nemi afuwa kan matsalolin da jama’a ke fuskanta.

Ya kuma ce gwamnati za ta kafa wata kungiya ta musamman domin duba matsalar kudin kasar da kuma hanyoyin magance ta.

Vladimir Putin ya tattauna da Shugaban Iran

Mun ba ku labarin cewa Shugaban ƙasar Rasha, Vladimir Putin, ya kira waya inda suka tattauna da Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian kan yakin da ake yi.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa Putin ta tattauna da Pezeshkian kan yakin Iran da Isra'ila mai goyon bayan kasar Amurka.

Fadar Kremlin ta ce yayin tattaunawar, Putin ya jaddada matsayinsa na goyon bayan dakatar da rikicin da wuri domin rage tashin hankali.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.