Iran Ta Ji Wuta Ta Shirya Mika Wuya ga Amurka? Trump Ya Yi Magana

Iran Ta Ji Wuta Ta Shirya Mika Wuya ga Amurka? Trump Ya Yi Magana

  • Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi taro da shugabannin kasashe bakwai mafi tattalin arziki a duniya
  • A wajen taron Donald Trump ya tabo batun mika wuyar kasar Iran da kuma yakin da ake yi a Gabas ta Tsakiya
  • Shugabannin kasashen sun nuna damuwarsu kan yadda yakin yake taba tattalin arziki, inda suka bukaci a gaggauta kawo karshensa

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Washington, Amurka - Shugaba Donald.Trump ya yi taro da shugabannin kasashe bakwai mafi karfin tattalin arziki (G7), ta hanyar yanar gizo.

Shugaba Trump a taron na ranar Laraba, 11 ha watan Maris 2026 ya shaida wa shugabannin kasashen na G7 cewa Iran na gab da mika wuya.

Trump ya ce Iran ta shirya mika wuya
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump Hoto: Donald J. Trump
Source: Facebook

Tashar Axios ta bayyana cewa jami'ai uku daga ƙasashen G7 da aka yi wa bayani kan abubuwan da aka tattauna a taron suka bayyana hakan.

Kara karanta wannan

"Dole mu dauki fansa," Jagoran Iran, Mojtaba Khamenei ya kada hantar Amurka da Isra'ila

Iran ta sha alwashin ci gaba da yaki

Sa'o'i 24 bayan haka, sabon jagoran addini na Iran ya fitar da bayaninsa na farko ga jama'a inda ya sha alwashin ci gaba da fafatawa.

A cikin wani sako da aka karanta a gidan talabijin na gwamnati ranar Alhamis, Mojtaba Khamenei ya sha alwashin ɗaukar fansar "shahidan" Iran da kuma buɗe sababbin fagagen yaƙi "inda maƙiyi ba shi da kwarewa sosai kuma yake da rauni ƙwarai."

Gwamnatin Iran ba ta nuna wata alamar mika wuya ko rugujewa nan kusa ba, kuma a rana ta 14 na yaƙin, tana ƙoƙarin samun ƙarin ƙarfin dabarun yaƙi ta hanyar toshe mashigar ruwa ta Strait of Hormuz.

Me Trump ya ce kan Iran?

Trump ya yi fahari game da sakamakon aikin soja na "Operation Epic Fury" a kiran na G7 na safiyar Laraba, inda yake shaida wa ƙawayen Amurka cewa, "Na kawar da cutar da take yi mana barazana dukkanmu."

Kara karanta wannan

Isra'ila ta ji ruwan wuta, ta fara karaya a shirin da ta yiwa gwamnatin Musulunci ta Iran

Yayin da yake iƙirarin cewa Iran na gab da mika wuya, ya kuma bayyana cewa babu sauran jami'an da suka rage a raye a Tehran waɗanda ke da ikon yanke wannan shawarar.

A cewar jami'ai biyu da aka yi wa bayani kan taron, Trump ya bayyana cewa:

"Babu wanda ya san wane ne shugaba, don haka babu wanda zai iya sanar da mika wuya."
Trump ya ce Iran za ta mika wuya
Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian da Shugaba Donald Trump na Amurka Hoto: @drpezeshkian, @RealDonaldTrump
Source: Twitter

An nemi Trump ya kawo karshen yaki da Iran

Wannan taron ya gudana ne a daidai lokacin da shugabannin G7 ke nuna damuwa ƙwarai kan yadda yaƙin ke ƙara shafar tattalin arziki.

Duk sauran shugabannin sun bukaci Trump da ya kawo ƙarshen yaƙin cikin gaggawa, inda suka jaddada cewa dole ne a samar da tsaro a mashigar Hormuz muddin zai yiwu.

Iran ta fadi sharadin tsagaita wuta

A wani labarin kuma, kun ji cewa mahukunta a Iran sun yi magana kan tsagaita wuta a yakin da suke yi da Amurka da Isra'ila.

Babban sakataren majalisar tsaron Iran, Ali Larijani ya bayyana cewa kasarsa ba za ta janye daga yaki ba har sai Amurka ta yi nadamar abin da ya kira babban kuskuren da ta yi na fara yaki.

Larijani ya jaddada cewa Iran za ta ci gaba da gwagwarmaya har sai Amurka ta gane kuskuren matakin da ta dauka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng