Rana Ta 14: Iran ta Jikkata Dubban 'Yan Isra'ila, an Ji Babban Kara a Tehran
- A yau Juma'a aka shiga rana ta 14 da fara yaki tsakanin Iran da Amurka/Isra'ila, lamarin da ya shafi kasashe da dama a yankin Gabas ta Tsakiya
- Yayin da ake cigaba da kai hare-hare, ma'aikatar lafiya ta Isra'ila ta sanar da adadin dubban mutanen da suka samu munanan raunuka
- Da safiyar yau Juma'a, 13 ga Maris 2026, an ji kara a birnin Tehran yayin da dubban jama'a suka fito kan tituna domin zagayen ranar Kudus
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Iran - Tun baya fara yakin Iran da Isra'ila/Amurka a ranar 28 ga Fabrairun 2026, dubban mutane sun jikkata yayin da daruruwa suka riga mu gidan gaskiya.
Hakan na zuwa ne saboda hare-haren da aka rika kaiwa kasashen da suke yaki da juna da ma wadanda suke kusa da su a Gabas ta Tsakiya.

Source: UGC
Iran ta jikkata dubban mutane a Isra'ila
Al-Jazeera ta rahoto Ma’aikatar lafiyar Isra’ila ta ce akalla mutane 2,975 sun jikkata tun bayan fara yakin Amurka da Isra’ila kan Iran a ranar 28 ga Fabrairun 2026.
Hakan ya biyo bayan harba makamai masu linzami da Iran ta rika yi zuwa Isra'ila, musamman birnin Tel Aviv a kwanakin da aka shafe ana yakin.
Rundunar sojin Isra’ila ta ce ta kai hare-hare lokaci guda a biranen Tehran, Shiraz da Ahvaz, tana mai ikirarin cewa ta kai hari kan wuraren kera makamai da wuraren ajiyarsu.
Kasar Iran ta kama mutane 4
Iran ta bayyana cewa rundunar IRGC ta kama mutane hudu da ake zargi da mika bayanai masu muhimmanci ga tashar Iran International mai amfani da harshen Farsi da ke Birtaniya.
Rahoto ya nuna cewa ta bayyana tashar a matsayin:
“Wata kafar yada labarai mai adawa da Iran.”
Rahoton ya ce mutanen da aka kama sun adana bayanai na sirri a wayoyinsu game da wuraren da makamai masu linzami da bama-bamai suka fada, sannan suka aika wa wannan kafar.

Kara karanta wannan
Yaki da canza salo, Iran ta sauya dabarun kai hare hare kan sansanonin Amurka da Isra'ila

Source: Getty Images
Iran ta tattauna da kasar India
Ministan harkokin wajen Iran ya tattauna ta waya da takwaransa na India kan yakin da ke gudana da kuma batutuwan tsaron yankin.
A yayin tattaunawar Iran ta jaddada muhimmancin kungiyar BRICS wajen tallafa wa zaman lafiya da daidaito a yankunansu da ma duniya baki daya.
Rahoto ya nuna cewa Iran ta kuma bukaci kungiyoyin kasa da kasa da na yankin su yi Allah-wadai da hare-haren Amurka da Isra’ila a Tehran.
Mutanen Iran sun ji babban kara a Tehran
Rahotannin kai tsaye sun ce an ji karar manyan fashe-fashe da dama a tsakiyar birnin Tehran a ranar Juma’a, kamar yadda kafafen yada labarai na gwamnatin Iran suka ruwaito.
Rahoton Hindustan Times ya kara da cewa hare-haren sun afka wa wani yanki da ke kusa da wurin da ake gudanar da zanga-zangar goyon bayan gwamnati.
Mutane da dama sun taru a Tehran da sauran manyan birane domin zagayen ranar Kudus da ake yi a Juma’ar karshe ta watan Ramadan.
An kashe sojan Faransa a kasar Iraq
A wani labarin, kun ji cewa Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron ya tabbatar da wani hari da ya ce an kai sansanin sojojinsu a Iraq.
Macron ya bayyana cewa an kashe musu soja daya yayin da wasu dakaru suka samu rauni, amma bai fadi irin illar da aka musu ba.
Hakan na zuwa ne yayin da ake cigaba da gwabza yaki tsakanin Amurka/Isra'ila da Iran, inda Macron ya ce bai kamata hakan ya shafi Faransa ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

