Amurka Ta Je Barbara, Za Ta Iya Dawo wa da Ciki a Yakin Iran
- Masanin harkokin tsaro, Joe Cirincione ya ce dogon yaƙi na iya sauya siyasar Amurka fiye da ta daular Musulunci ta Iran
- Ya bayyana haka ne a yayin da yakin da Amurka da Isra'ila suka fara da Iran ya shiga rana ta 13 ana ci gaba da gwabzawa
- Joe Cirincione ya bayar da tabbacin cewa tarihi ya nuna cewa yaƙe-yaƙe kan sauya ra’ayin jama’a da tsarin shugabanci a ƙasashe
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
USA – Masanin harkokin tsaro Joe Cirincione ya bayyana cewa duk wani yaƙi mai tsawo a duniya kan iya haifar da sakamako na siyasa da ba a zata ba.
Joe Cirincione ya bayyana haka ne bayan gwamnatin Amurka da Isra'ila sun sha kiraye-kiraye ga 'yan Iran su karbe gwamnati bayan kashe Ayatollah Ali Khamnei.

Source: Facebook
A wani nazari da aka wallafa a shafin Facebook na World Times Institute, Joe Cirincione ya kara da cewa yakin zai iya kawo canji a cikin manyan ƙasashe kamar Amurka.
An yi wa Amurka mummunan hasashe
A wani nazarin da ya gabatar, Cirincione ya ce akasari mutane kan ɗauka cewa irin waɗannan rikice-rikice sukan fi girgiza ƙasashen da ake kai wa hari, kamar Iran.
Sai dai a cewarsa, tarihin duniya ya nuna cewa wani lokaci sakamakon siyasar da yaƙi ke haifarwa kan fi bayyana a ƙasashen da ke shiga yaƙin.

Source: Getty Images
Ya ce idan rikici ya daɗe yana gudana, yana iya canza yadda jama’a ke kallon gwamnati da shugabanni, wanda hakan kan iya sa a samu matsin lamba ga masu mulki.
A cewarsa, irin wannan yanayi na iya haifar da sauyi a cikin siyasa, musamman idan jama’a suka fara tambayar dalilin yaƙin ko kuma yadda gwamnati ke tafiyar da al’amura.

Kara karanta wannan
To fa: Musayar wutar da ake tsakanin Amurka, Isra'ila da Iran ta shiga wani muhimmin mataki
Yadda yaki da Iran zai shafi Amurka
Joe Cirincione ya yi nuni da cewa tarihin duniya ya nuna misalai da dama inda rikice-rikicen yaƙi suka haifar da sauye-sauye a cikin tsarin siyasa, ko kuma suka sa shugabanni suka rasa karɓuwa a idon jama’a.
Haka kuma, irin wannan rikici kan sa a samu rarrabuwar ra’ayi a tsakanin al’umma, wanda wani lokaci kan jawo matsin lamba ga gwamnati ta sake duba manufofinta. Cirincione ya bayyana cewa a irin wannan yanayi, shugabanni kan fuskanci ƙalubale wajen tabbatar da cewa suna da goyon bayan jama’a, musamman idan yaƙin ya jawo asarar rayuka ko kuma matsin tattalin arziki.
Ya kara da cewa wannan yaki da Amurka ta tsunduma kanta zai iya jawo canji a cikin kasar fiye da Iran da suke kokarin kawo wa matsala.
Amurka na tafka asara - Masani
Kwamred Sa'idu Bello ya shaida wa Legit cewa yaƙin Amurka da Iran ya ɗauki fuskoki biyu, kuma ba za a sassauta ba sai Trump ya dakatar da harin da ake kai wa Iran.

Kara karanta wannan
Lauya ya kitsawa gwamnatin Tinubu yadda za ta tursasa wa Trump kawo karshen yaki da Iran
A kalamansa:
"Matukar Amurka ba za ta daina kai hari Iran ba, su ma ba za su fasa kai hari wuraren duk wuraren da Amurka da Isra'ila suke ba."
"A munafurce, Amurka tana kokarin ya za ta yi a dakatar da yaƙin saboda tana ganin suna asara ba karama ba, musamman a Gabas ta Tsakiya.
"Yadda suke rike da tattalin arziki Gabas ta Tsakiya, lokaci guda an zo an yi wannan yakin sun yi asara."
"Ba karamar asara Amurka ta yi ba na dukiya da rayukan al'umma."
Ya ce wannan yaki zai zo karshe ne idan Iran ta ke da tabbacin za ta samu sauƙin al'amura amma ba saboda karfin soja ba.
Amurka ta tabbatar da bacewar jirginta
A baya, kun ji cewa rundunar sojin Amurka ta tabbatar da bacewar jirgin dakon manta a yammacin Iraki yayin da ake gudanar da farmakin Epic Fury kan kasar Iran.
Jami'an soji sun bayyana cewa ba wai harin makiya ne ya jawo bacewar jirgin ba, kuma ana cigaba da kokarin neman mutanen da ke cikinsa don tabbatar da halin da ake ciki
Wannan ne jirgi na hudu da Amurka ta rasa a yakin Gabas ta Tsakiya bayan an kakkabo jiragen F-15 guda uku a kasar Kuwait bisa kuskure yayin da yakin ya shiga kwana na 13.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
