"Dole Mu Dauki Fansa," Sabon Jagoran Iran, Mojtaba Khamenei Ya Kada Hantar Amurka da Isra'ila

"Dole Mu Dauki Fansa," Sabon Jagoran Iran, Mojtaba Khamenei Ya Kada Hantar Amurka da Isra'ila

  • Jagoran addinin Iran, Mojtaba Khamenei ya sha alwashin daukar fansar mahaifinsa da sauran wadanda suka yi shahada a yakin Isra'ila/Amurka
  • Mojtaba ya bayyana haka ne a jawabinsa na farko bayan ya gaji mahaifinsa, Ali Khamenei, wanda ya fitar yau Alhamis, 12 ga Maris, 2026
  • Ya bukaci al'ummar Iran su hada kansu a wannan lokaci mai wahala, inda ya ce gwamnati za ta biya diyyar wadanda aka kashe a yaki

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Iran - Jagoran addinin Iran, Mojtaba Khamenei, ya gabatar da jawabinsa na farko ga jama’a tun bayan nada shi a matsayin magajin mahaifinsa, Marigayi Ayatollah Ali Khamenei.

A jawabin da ya yi, Mojtaba ya yi kira ga al’ummar kasar su hada kai, tare da amincewa da wahalhalun da ake fuskanta sakamakon yakin da Iran ke yi da Amurka da Isra'ila.

Kara karanta wannan

Mojtaba Khamenei: Sabon Jagoran Iran ya fadi abin da yake son kasashen Larabawa su yi wa Amurka

Mojtaba Khamenei.
Jagoran addini na jamhuriyar musulunci ta Iran, Mojtaba Khamenei Hoto: Jaafar Hamid
Source: Getty Images

A rahoton da tashar al-jazeera ta tattaro, jagoran Iran ya bayyana radadin da yakin kasar ya jefa shi a ciki, wanda ya hada da kashe mahaifinsa da wasu daga cikin iyalansa.

Jagoran Iran ya mika sakon ta'aziyya

An karanta jawabin ne a gidan talabijin na gwamnati, inda ya mika ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu, tare da alkawarin cewa gwamnatin Iran za ta biya diyya ga wadanda suka yi asarar dukiya ko ‘yan uwa.

Sabon jagoran Iran ya danganta wahalhalun da kasar ta fuskanta da asarar da shi kansa ya yi a cikin iyalinsa, kamar yadda jaridar Vanguard ta kawo a rahotonta.

Mojtaba Khamenei ya tuna mahaifinsa

Ya ce a hare-haren hadin gwiwa na Amurka da Isra'ila, ya rasa mahaifinsa, tsohon jagoran Iran, Ayatollah Ali Khamenei, matarsa yayin da ‘yar uwarsa ta rasa ɗanta da mijinta.

Ya ce imani da Allah da hakuri su ne abin da ke taimaka wa mutane su jure irin wadannan jarabawa mai matukar wahala.

Kara karanta wannan

Isra'ila ta ji ruwan wuta, ta fara karaya a shirin da ta yiwa gwamnatin Musulunci ta Iran

Mojtaba Khamenei ya kuma yabawa ‘yan Iran daga kowane bangare na rayuwa saboda juriyar da suka nuna a lokacin yakin, yana mai cewa dole ne a tuna da dukkan wadanda suka mutu, wadanda ya kira da shahidai.

Khamenei da matarsa.
Marigayi tsohon jagoran addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei da matarsa Hoto: Majid Saeedi
Source: Getty Images

Iran za ta dauki fansar kisan 'shahidai'

A karshen jawabin, sabon jagoran ya tabbatar wa ‘yan kasar cewa Iran ba za ta manta da wadanda aka kashe ba, yana mai cewa za a dauki fansa kan wadanda ya kira “shahidai”.

“Ba za mu yi watsi da batun daukar fansar shahidanmu ba,” in ji shi, yana mai nuni da kashe tsohon jagora da wasu manyan jami’ai a hare-haren baya-bayan nan.

Isra'ila ta fara fargaba a yaki da Iran

A wani rahoton, kun ji cewa Isra'ila ta nuna alamun karaya da shakku kan yunkurinta na kifar da gwamnatin Musulunci ta kasar Iran.

Rahotanni tsun nuna cewa Isra'ila karkashin jagoranci Firmaninista, Benjamin Netanyahu ta fara fargabar cewa da wuya ta iya sauya gwamnatin Iran a wannan yaki.

Wani babban jami'in Isra'ila ya shaida cewa har yanzu gwamnatin musulunci ta Iran na da goyon bayan jama’ar ƙasar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262