Ramadan: Kasashen Musulmi Sun Fadi Illar Rufe Masallacin Kudus a Isra’ila
- Kasashe Musulmi da Larabawa takwas sun soki Israel kan rufe Masallacin Al-Aqsa a Jerusalem yayin watan Ramadan
- Ministocin harkokin wajen kasashen sun ce hana shiga masallacin ya sabawa dokokin kasa da kasa kuma tsokana ce ga masu ibada
- Sun bukaci gwamnatin Benjamin Netanyahu ta bude wuraren ibada a tsohon birnin Jerusalem nan take
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tel Aviv, Israel - Kasashe Musulmi da Larabawa takwas sun yi Allah-wadai da matakin Isra'ila na rufe Masallacin Kudus a watan Ramadan.
Kasashen sun nuna bakin ciki bayan rufw masallacin da sauran wuraren ibada a tsohon birnin Jerusalem a lokacin watan Ramadan.

Source: Getty Images
Dalilin rufe masallacin Kudus a Isra'ila
Isra’ila ta rufe dukkan wuraren ibada da ke tsohon birnin na Jerusalem saboda dalilan tsaro bayan ta fara hare-haren sama tare da Amurka kan Iran, lamarin da ya haifar da rikicin yankii, cewar Al Jazeera.

Kara karanta wannan
Bayan kwana 10 ana musayar wuta, Firaministan Isra'ila ya mika bukata 1 ga mutanen Iran
Rufe masallacin ya zo ne a lokacin Ramadan, lokacin da dubban Falasdinawa Musulmi kan halarci sallar Juma’a a Masallacin Al-Aqsa, wanda shi ne na uku mafi tsarki a addinin Musulunci.
Ministocin harkokin wajen kasashen Pakistan, Masar, Jordan, Hadaddiyar Daular Larabawa, Indonesia, Turkiyya, Saudi Arabia da Qatar sun ce ci gaba da hana shiga masallacin “haramun ne kuma babu hujja a kansa”.
Rufe masallacin Kudus: Martanin kasashen Larabawa
A cikin wata sanarwar hadin gwiwa, ministocin sun ce wannan mataki “babban keta dokokin kasa da kasa ne da kuma ka’idar bai wa mutane damar shiga wuraren ibada ba tare da takura ba”.
‘Yan sandan Isra’ila sun sanar a ranar Litinin cewa duk wuraren ibada a tsohon birnin, ciki har da Masallacin Kudus, Western Wall da Cocin Holy Sepulchre, za su ci gaba da kasancewa a rufe domin kare lafiyar jama’a.

Source: Getty Images
Yadda Isra'ila ta mamaye Gabashin Jerusalem
Isra'ila ta mamaye Gabashin Jerusalem tun shekarar 1967 sannan daga baya ta hade yankin da kasarta, matakin da kasashen duniya da dama ba su amince da shi ba.
Tun bayan fara yakin, hukumomin Isra’ila sun hana shiga tsohon birnin ga kowa sai mazauna yankin ko ‘yan kasuwa domin kare lafiyar al'ummar yankin.
Ministocin kasashen takwas sun jaddada cewa Isra’ila ba ta da ikon mallakar Jerusalem da wuraren ibada na Musulmi da Kiristoci da ke can.
Sun bukaci gwamnatin Isra’ila da ta janye haramcin shiga wuraren ibada domin bai wa masu ibada damar gudanar da ibadunsu cikin ‘yanci,cewar rahoton Times of Israel.
Isra'ila ta hana salla a masallacin Kudus
A wani labarin, Isra'ila ta hana Musulmai Falasdinawa gudanar da ibada a masallacin Al-Aqsa a rana ta uku a jere duk da ana cikin watan Ramadan.
Sheikh Ikrima Sabri ya bayyana cewa rufe masallacin ya saba wa hakkin gudanar da ibada kuma kokari ne na karbe ikon masallacin.
Ma'aikatan hukumar Wakafi sun koka kan yadda aka hana su kai abinci ga masu tsaron masallacin tun fara yaki da Iran.
Asali: Legit.ng
