Trump Ya Fadi Lokacin da Zai Dauki Amurka Ta Jefa Kasar Iran cikin Tsananin Duhu
- Shugaba Donald Trump ya bayyana cewa Amurka na iya lalata tashar wutar lantarkin Iran cikin sa'a guda amma ta zabi ta kyale su
- Shugaban ya yi ikirarin cewa sojojin Amurka sun ruguza kusan daukacin makaman da sojojin Iran suke takama da su wajen kai hari
- Trump ya jaddada cewa Amurka ta ceci kasar Isra'ila da ma daukacin yankin Gabas ta Tsakiya daga mamayar kasar Iran a halin yanzu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Amurka - Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa ƙasarsa tana da cikakkiyar damar ruguza dukkan hanyoyin samar da wutar lantarki da ababen more rayuwa na ƙasar Iran cikin sa'a guda.
Sai dai, Shugaba Donald Trump ya ce Amurka ta zaɓi ta kawar da kai daga ɗaukar irin wannan matakin, saboda wani jin kai nata.

Source: Getty Images
Donald Trump ya tabo batun wutar lantarkin Iran
Trump ya yi wannan ikirari ne a ranar Laraba yayin da yake zantawa da manema labarai a sansanin sojin sama na Joint Base Andrews dake Maryland, bayan dawowarsa daga tafiyar da ya yi zuwa Kentucky, in ji rahoton Tribune.
A cewar shugaban ƙasar, kodayake Amurka tana da ƙarfin soji na musamman da zai iya tarwatsa tushen wutar lantarkin Iran, Washington tana kauce wa hakan da gangan saboda irin mummunar asarar da hakan zai haifar na dogon lokaci ga fararen hula.
Trump ya jaddada cewa idan suka lalata wutar lantarkin Iran, zai iya ɗaukar ƙasar shekaru 25 kafin ta sake ginawa. Ya ce babban burin Amurka yanzu shi ne tabbatar da cewa Iran ba ta kuma samun damar sake gina ƙarfin sojinta da zai zama barazana ga duniya ba.
Nasarorin da sojojin Amurka suka samu
Trump ya yi iƙirarin cewa dakarun Amurka sun riga sun raunata ƙarfin sojin Iran sosai a cikin wannan yaƙin da ake yi, kamar yadda CNN ta rahoto.

Kara karanta wannan
Bidiyon lokacin da makamin Iran ya fada tsakiyar birnin Isra'ila, mutane sun mutu
Ya bayyana cewa kusan daukacin dakarun sojojin ruwan Iran an riga an nakasa su, sannan hare-hare sojojin Amurka sun yi mummunar ɓarna ga tsarin tsaron ƙasar.
Shugaban ya ƙara da cewa Amurka tana ci gaba da sanya ido sosai kan mashigar ruwan Hormuz yayin da take gudanar da ayyukan soji domin hana Iran sake farfaɗo da ƙarfinta.

Source: Getty Images
Amurka ta kare Isra'ila daga Iran
Bugu da ƙari, Trump ya bayyana cewa Iran tana shirin "mamaye daukacin Gabas ta Tsakiya" ne idan har Amurka da Isra'ila ba su kai mata harin kariya na rigakafi ba.
Ya ce an lalata mafi yawan makamai masu linzami da sauran makaman da Iran ta mallaka, waɗanda ya ce an saita su ne domin kai hari ga ƙasashen Gabas ta Tsakiya waɗanda ba su ji ba ba su gani ba.
Ya jaddada cewa Iran tana shirin ruguza Isra'ila, amma Amurka ta dakatar da hakan ta hanyar amfani da dabarar kai hari a kan lokaci.
Trump ya yi barazana ga kasar Iran
A wani labari, mun ruwaito cewa, Donald J. Trump, ya yi gargadi mai tsauri ga gwamnatin Iran dangane da yiwuwar dasa nakiyoyi a mashigar ruwa ta Hormuz.

Kara karanta wannan
Yau Amurka ta shirya kai hare hare mafi muni kan Iran, "mazauna Tehran su shirya"
Wannan ya biyo bayan rahotannin da aka samu cewa akwai yiwuwar Iran na dasa nakiyoyi a wannan muhimmin wuri da jiragen ruwa ke bi domin safarar man fetur da sauran kayayyaki.
Trump ya jaddada cewa idan aka tabbatar cewa an dasa nakiyoyi kuma ba a cire su ba, to Amurka za ta dauki matakin soja mai tsauri wanda ba a taba ganin irinsa ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
