Asiri Ya Tonu: An Bankado Yadda Amurka Ta Jefa Bam a kan Daliban Iran
- Rahotanni sun nuna cewa tabbas bama-baman Amurka ne suka fada a kan makarantar Minab inda aka kashe dalibai da dama a kasar Iran
- Tun a farkon hare-haren da Amurka ta fara kai wa Iran ne aka kashe daruruwan daliban, yawancinsu yara da ke daukar darussa a makaranta
- Sai dai Donald Trump ya sha musanta cewa kasarsa ce ta kashe yaran, lamarin da yanzu bincike ya tabbatar da cewa Amurka ce da danyen aikin
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
United States – Rahotanni sun bayyana cewa makarantar harin Amurka ne ya salwantar da rayukan daliban da ke makarantar da ke garin Minab a Iran.
Sai dai binciken da aka yi ya bayyana cewa an gina makarantar ne a kusa da wasu gine-ginen da rundunar ruwa ta Iran ke amfani da su.

Source: Facebook
New York Times ta wallafa cewa makaranyar na daya daga cikin manyan wuraren da sojojin Amurka suka mayar da hankali a hare-haren da suke kai wa yayin rikicin.
An bankado kuskuren kasar Amurka
The Times ta wallafa cewa bincike ya nuna cewa ginin da ake amfani da shi a matsayin makaranta a yau a da can ba makaranta ba ce.
Rahoton ya ce a baya, wannan wuri wani bangare ne na sansanin soja. Sai dai ba a san takamaiman shekarar da aka fara amfani da ginin a matsayin makaranta ba.
Binciken da aka yi ta hanyar hotunan tauraron dan adam ya nuna cewa tsakanin shekarun 2013 zuwa 2016 ne aka raba ginin makarantar da sauran sansanin sojan ta hanyar gina katanga.
A wannan lokaci ne aka fara nuna alamun cewa an canza amfani da wurin daga sansanin soja zuwa makaranta.
An yi bincike kan harin Amurka a Iran
Hotunan tauraron dan adam sun kuma nuna cewa an cire wasu hasumiyoyin sa ido da ke kusa da ginin.

Source: Getty Images
Haka kuma an bude hanyoyi uku ga jama’a zuwa makarantar. An kebe fili a harabar makarantar, sannan aka zana wuraren wasa da filin wasanni a kan kwalta.
Haka kuma an shafe bangon makarantar da launin shudi da ruwan hoda domin ya dace da muhalli irin na makarantu.
Sai dai har yanzu masu bincike sun gaza fahimtar yadda tsofaffin bayanai suka isa ga rundunar Amurka ko yadda aka yi aka gaza sabunta su.
Jami’an Amurka sun ce har yanzu binciken yana gudana kuma akwai sauran abubuwa da za a gano.
Haka kuma ana nazarin ko wasu manhajojin fasaha kamar tsarin basirar wucin gadi ko shirye-shiryen nazarin bayanai ne suka taimaka wajen jawo kuskuren.
Iran ta magantu kan yaki da Amurka
A baya, mun wallafa cewa Amurka da Isra'ila na ci gaba da kai hare-hare kan kasar Iran, yayin da take mayar da martani a yakin da ake yi a Gabas ta Tsakiya.
Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya bayyana cewa kasarsa na son ganin an samu zaman lafiya a yankin, amma wannan ba ya nufin za ta bari a ci zarafinta.
Pezeshkian ya gindaya sharudda guda uku da dole sai an cika su matukar ana son a kawo karshen yakin da ake yi a Gabas ta Tsakiya da ke ci gaba da kazanta.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


