Yaki da Canza Salo, Iran Ta Sauya Dabarun Kai Hare Hare kan Sansanonin Amurka da Isra'ila

Yaki da Canza Salo, Iran Ta Sauya Dabarun Kai Hare Hare kan Sansanonin Amurka da Isra'ila

  • Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sanar da sauya dabaru da salon ka hare-hare a yakin da take da kasashen Amurka da Isra'ila
  • Babbar hedkwatar sojojin Iran ta Khatam al-Anbiya ta ce ta dakatar da tsarin kai hare-haren ramuyar gayya kan wadanda ta kira 'makiya'
  • Ta kuma jaddada cewa daga yanzu za ta fara kai hare-hare kai tsaye kan Isra'ila da sansanonin Amurka, lamarin da ake ganin zai iara tsananta rikicin

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Iran - Rundunar sojojin kasar Iran ta sanar da canza salo da dabarun kai hare-hare a yakin da ke kara zafi a yankin Gabas ta Tsakiya.

Dakarun Iran sun bayyana cewa sun kammala kai hare-haren ramuwar gayya kan abokan fadansu, Amurka da Isra'ila kuma yanzu za su fara kai jerin hare-hare babu kakkautawa.

Mojtaba Khamenei.
Jagoran addini na kasar Iran, Mojtaba Khamenei Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

Kasar Iran ta canza tsarin kai hare-hare

Kara karanta wannan

Tsautsayi ya gitta, harin kasar Iran ya rutsa da 'dan Najeriya da wasu mutane sama da 100

Tashar Sky News ta tattaro cewa mai magana da yawun hedikwatar sojoji ta Khatam al-Anbiya ta Iran, Ebrahim Zolfaqari, ne ya sanar da hakan a wata sanarwa yau Laraba, 11 ga watan Maris, 2026.

Ebrahim Zolfaqari ya bayyana wani gagarumin sauyi a sabuwar dabarar yaki da kasar za ta rika amfani da ita yayin da wannan yaki ya shiga rana ta 12.

A wata sanarwa da aka fitar, jami’in ya ce gwamnatin Iran ta daina tsarin ramuwar gayya kai tsaye da ta saba amfani da shi a baya.

Sabon tsarin yaki da Iran ta bullo da shi

Maimakon haka, ya ce Iran za ta koma dabarar kai hare-hare ba tare da kakkautawa ba, wanda ke nuna wani babban sauyi a tsarin dabarun sojojin Jamhuriyar Musulunci

Sanarwar canza salon yakin ta fito ne kai tsaye daga kakakin Khatam al-Anbiya, wadda ake dauka a matsayin daya daga cikin manyan cibiyoyin sojoji na kasar Iran.

Wannan mataki na sauyawa daga tsarin “ramuwar gayya” zuwa tsarin “hare-hare ba kakkautawa” na nuni da cewa Iran na shirin daukar matsaya mafi tsauri kuma ta kai tsaye a yakinta da kasashen Amurka da Isra'ila.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Rasha ta yi nasara, ta fi kowa amfana da yakin Iran da Amurka, Isra'ila

Mojtaba.
Jagoran kasar Iran, Mojtaba Khamenei da yadda ake harba makami mai linzami Hoto: Majid Saedi
Source: Getty Images

Masu lura da al’amura na ganin wannan sabon mataki na iya nuna cewa Iran na son barin tsarin mayar da martani kawai, ta koma tsarin kai hare-hare akai-akai a ayyukanta da sojoji, musamman a wannan yaki.

Iran dai ta sha nanata cewa ba za ta koma teburin tattaunawa da Amurka ba saboda abik da ta kira, "mummunar cin amana," da aka mata a tattaunawar da aka yi a baya, kamar yadda NBC News ta ruwaito.

Erdogan ya bukaci a tsagaita wuta

A baya, kun ji cewa Recep Tayyip Erdogan na Turkiyya ya ce akwai matsala mai girma a Gabas ta Tskiya idan ba a dakatar da yakin Iran, Amurka da Isra'ila ba.

Shugaba Erdogan ya yi gargadin cewa matukar ba a gaggauta dakatar da yakin ba, to babu makawa sai ya kara jefa tattalin arzikin duniya cikin gagarumar matsala.

Shugaban kasar na Turkiyya ya ce akwai yiwuwar kawo karshen rikicin idan aka bi hanyar diflomasiyya, yana mai cewa ya kamata kasashen su koma kan teburin tattaunawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262