Harin Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ya Rutsa da 'Dan Najeriya, Mutane Sun Mutu a UAE

Harin Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ya Rutsa da 'Dan Najeriya, Mutane Sun Mutu a UAE

  • Harin da Amurka ta kai Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ya rutsa da 'dan Najeriya da wasu 'yan kasashe daban-daban
  • Hukumomin UAE sun tabbatar da mutuwar mutum shida da jikkata fiye da mutane 120 a hare-haren da Iran ta kai kasar tun farkon yakin da ya barke
  • Yan Najeriya na ci gaba da kiraye-kiraye ga gwamnatin tarayya domin ta shirya yadda za a kwaso su a dawo da su gida saboda rikicin Gabas ta Tsakiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

United State Emirate - 'Dan Najeriya na cikin mutane da dama da suka jikkata bayan da aka kakkabo makamai masu linzami da Iran ta harba zuwa Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE).

Wannan farmaki da kasar Iran ta kai na zuwa ne a daidai lokacin da rikicin Gabas ta Tsakiya ke kara tsananta.

Kara karanta wannan

Bidiyon lokacin da makamin Iran ya fada tsakiyar birnin Isra'ila, mutane sun mutu

Hadaddiyar Daular Larabawa.z
Wasu yankuna da Iran ta kai farmaki a Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) Hoto: Christopher Pike
Source: Getty Images

A rahoton tashar Al-Jazeera, hukumomin UAE sun ce tsarin kariyar sararin samaniyarsu na ci gaba da kakkabo makamai da jirage marasa matuki da Iran ke harbawa tun bayan fara yakin a ranar 28 ga Fabrairu, 2026.

Iran ta harba makamai 262 zuwa UAE

A wata sanarwa da ma’aikatar tsaron kasar ta fitar a ranar Talata, ta ce an gano makamai masu linzami 262 da aka harbo daga Iran tun bayan fara rikicin.

Ta ce jami'an tsaro sun yi nasarar kakkabo 241 daga cikinsu, 19 sun fada cikin teku, yayin da wasu makamai biyu suka fada cikin yankin UAE, wanda ya janyo asarar rayuka da kuma jikkata mutane.

Mutane shida sun mutu a UAE

Ma’aikatar tsaron kasar ta ce hare-haren Iran sun yi sanadin mutuwar mutane shida, wadanda suka hada da ‘yan asalin UAE, Pakistan, Nepal, da Bangladesh.

Haka kuma mutane 122 sun jikkata, ciki har da ‘yan kasashe daban-daban da suka hada da, Masar, Sudan, Habasha, Philippines, Indiya, Iran, Sri Lanka, Turkiyya, Uganda, Lebanon, Afghanistan, Bahrain, Yemen, Jordanz Falasdinu da kuma Najeriya.

Kara karanta wannan

Akwai matsala: Majalisar Dinkin Duniya ta hango abin da zai faru sakamakon yakin Amurka da Iran

Shugaba Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da yadda ake musayar wuta a Gabas ta Tsakiya Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Rahotanni sun nuna cewa Iran na kai wadannan hare-hare ne a matsayin ramuwar gayya, bayan zargin UAE ta ba Amurka damar amfani da sansanonin sojinta da ke wajen kai hare-hare kan Iran.

A ranar Laraba, ma’aikatar tsaron UAE ta ce sojojinta sun sake kakkabo wasu makamai masu linzami da jirage marasa matuki, tare da tabbatar da cewa kasar na cikin shiri domin kare kanta daga duk wata barazana.

‘Yan Najeriya na neman a kwashe su

A halin yanzu, wasu ‘yan Najeriya da ke makale a kasashen yankin Gulf sun bukaci gwamnatin Nigeria da ta fara shirya jiragen kwaso ‘yan kasarta idan har rikicin ya kara tsananta.

Har yanzu ba a san yawan ‘yan Najeriya da ke cikin Iran ko sauran kasashen Gabas ta Tsakiya da rikicin ya shafa ba, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Iran ta farmaki jiragen ruwan Isra'ila

A wani rahoton, kun ji cewa sojojin kasar Iran sun kai farmaki kan wasu jiragen ruwa guda biyu da ake zargin mallakin kasar Isra'ila ke a mashigar Strait of Hormuz.

Kara karanta wannan

Saudiyya ta shiga duniya neman kariya daga hare haren Iran

Sanarwar da Iran ta fitar ta ce jiragen sun yi biris da gargaɗi da sanarwar gaggawa da dakarun ruwa na IRGC suka bayar kafin a buɗe musu wuta tare da tsayar da su.

Hedkwatar rundunar sojin Iran ta Khatam al-Anbiya ta yi gargaɗin cewa Iran za ta sauya salon yaƙinta da kasashen Amurka da Isra'ila.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262