Harin da Iran Ta Kai Isra'ila Ya Hallaka Ɗan Uwan Netanyahu? Bayanai Sun Fito

Harin da Iran Ta Kai Isra'ila Ya Hallaka Ɗan Uwan Netanyahu? Bayanai Sun Fito

Isra'ila - Rikici na ci gaba da ruruwa a Gabas ta Tsakiya, inda aka rahoto cewa mutane fiye da 1,200 sun mutu a Iran da kuma 13 a Isra'ila, yayin da ake zargin an kashe ɗan uwan Benjamin Netanyahu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

A irin wannan yanayin ne ake yawaitar samun yaɗuwar labaran ƙarya a yanar gizo. Sau da yawa ana yaɗa bayanan da ba a tantance ba a dandalin sada zumunta.

Ana fargabar an kashe dan uwan Benjamin Netanyahu a wani irin Iran
Benjamin Netanyahu, Firayim Ministan Isra'ila a wata ziyara da ya kai garin Beit Shemesh kusa da yammacin Kudus bayan harin Iran. Hoto: Avi Ohayon / GPO / Handout/Anadolu via Getty Images
Source: Getty Images

Ɗaya daga cikin irin waɗannan labaran ya nuna cewa an kashe Iddo Netanyahu, ɗan uwan Firayim Ministan Isra'ila, yayin da Itamar Ben-Gvir, Ministan Tsaron Isra'ila, ya jikkata a wani harin sama da Iran ta kai a Tel Aviv, in ji rahoton First Post.

Ana iƙirarin kashe ɗan uwan Benjamin Netanyahu

Wasu shafukan dandalin sada zumunta sun riƙa iƙirarin cewa harin Iran na sama ya yi sanadiyyar mutuwar ɗan uwan Benjamin Netanyahu, Iddo, tare da raunata Ministan Tsaron Isra'ila, Itamar Ben-Gvir.

Kara karanta wannan

Yakin Iran da Amurka: Sojojin Isra'ila sun kashe babban malamin addinin Kirista

Rahotannin sun ƙara da iƙirarin cewa Ben-Gvir ya jikkata ne bayan da ake zargin gidansa ya kama wuta. Wasu daga cikin shafukan sun ci gaba da iƙirarin cewa hukumomin Isra'ila na ƙoƙarin ɓoye gaskiyar lamarin.

Akwai wasu rahotanni da ke yawo cewa kafafen yaɗa labarai na Isra'ila sun bayar da rahoton ƙarya cewa Ben-Gvir ya yi haɗarin mota ne domin ɓoye raunukan da ya samu a yayin harin da ake zargin an kai.

Wani shafin watsa labarai, Daily Iran News, ya wallafa a shafinsa na X cewa:

"Ɗan uwan Benjamin Netanyahu, Iddo Netanyahu, ya rasa ransa bayan harin makaman Iran a gidan da iyalan Netanyahu suke zama."

Fiye da mutane 50,000 suka karanta wannan sako wanda ke hade da bidiyon gobara na tashi a wani gida da ake zargin na su Netanyahu ne.

Shin ɗan uwan Benjamin Netanyahu ya mutu?

Babu wasu rahotanni ko tabbaci daga hukuma dake nuna cewa an kai hari gidan Itamar Ben-Gvir dake Tel Aviv. A cewar rahotannin kafafen yaɗa labarai, faifan bidiyon dake nuna gidan yana ci da wuta an ɗora shi ne a yanar gizo makonni da dama kafin ɓallewar yaƙin a Yammacin Asiya.

Kara karanta wannan

Ga dama ta samu: WikkiTimes ta kaddamar da shirin 'Femi Falana Legal Defenders'

A cewar kafar wata labaran Yahoo News, an ɗauki faifan bidiyon ne a New Jersey, ba a Yammacin Asiya ba. Babu wasu rahotannin labarai masu tushe dake nuna cewa Iddo Netanyahu ya samu wata cutarwa a kowace gobara yanzu.

Rahoton jaridar ya nuna cewa an dauki bidiyon ne a New Jersey, ba wai a Gabas ta Tsakiya ba. Kuma har zuwa lokacin wallafa wannan bincike, babu wata sahihiyar kafar labarai da ta rahoto cewa an kashe Iddo Netanyahu.

Wane ne Iddo Netanyahu?

An tabbatar da cewa babu wata kafar labarai mai inganci da ta rahoto mutuwar Iddo Netanyahu.
Iddo Netanyahu, dan uwan Firayim Ministan Isra'ila da ake zargin Iran ta hallaka. Hoto: Yves Forestier/Getty Images
Source: Getty Images

An haifi Iddo Netanyahu ne a shekarar 1952, kuma ƙani ne ga Firayim Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu. Iddo likitan fannin hasken radiology ne da ya ƙware a wannan fanni, in ji rahoton The News International.

Ya samu digirin sa na MD daga Jami'ar Hebrew dake Kudus kuma ya kammala horon sa na kwararru a asibitin Jami'ar Georgetown da kuma cibiyar lafiya ta Mount Sinai.

Baya ga aikin likitanci, an san shi da wasannin kwaikwayo, rubuce-rubucen kasidu da litattafai. Iddo ya rubuta litattafai da dama da suka shahara a duniya.

Zargin Iran ta hallaka Netanyahu

Tun da fari, mun ruwaito cewa, wani sako da ya yadu a kafofin sadarwa ya bayyana cewa Firayim ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya mutu.

Kara karanta wannan

Hezbollah ta kakkabo jirgin yaƙin Isra'ila, an kashe fiye da mutane 1330 a Iran

Sakon da aka wallafa a ranar 28 ga Fabrairun 2026, wanda mutane kusan 954,000 suka karanta, ya yi ikirarin cewa Firayim Ministan ya mutu ne a harin Iran.

Sai dai, binciken kwakwaf da Legit Hausa ta gudanar ya tabbatar da cewa Netanyahu na raye kuma yana ci gaba da rike mukaminsa na Firaminista.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com