Isra'ila Ta Shiga Uku, Iran Ta Kaddamar da Hari Mafi Muni tun Farkon Fara Yaki
- Ana ci gaba da fafatawa tsakanin Iran da kasashen Amurka da Isra'ila tun farkon fara yaki a ranar 28 ga watan Fabrairun 2026
- Rundunar IRGC ta bayyana cewa ta kaddamar da rukuni na 37 na farmakin 'True Promise 4' kan kasar Isra'ila
- Ta bayyana cewa harin shi ne mafi tsanani da ta kai tun farkon fara yakin inda ta bayyana kalar makamai masu linzami da ta yi amfani da su
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Tehran, Iran - Rundunar dakarun kare juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta sanar da cewa ta ƙaddamar da rukuni na 37 na farmakin nan mai suna “True Promise 4”.
Rundunar ta bayyana sabon rukunin na 37 a matsayin hari mafi muni da aka taɓa kaiwa tun farkon fara yakin.

Source: Twitter
Tashar NBC News ta ce bisa sanarwar ta IRGC a ranar Laraba, 11 ga watan Maris 2026, wannan sabon harin ya nufi sansanonin sojin Isra'ila da kuma wuraren da ke da alaƙa da Amurka a faɗin yankin.

Kara karanta wannan
Iran ta sake harba makamai, ta yi wa yahudawa mummunar barna a Isra'ila cikin awanni 24
Sabon harin na nuna ci gaba da nuna tsanantar artabu tsakanin Iran, Isra'ila, da Amurka wanda ya fara tun ranar 28 ga Fabrairun 2026.
Wuraren da IRGC ta farmaka
Dakarun sun ce samamen ya haɗa da hare-hare kan wurare a Tel Aviv da sauran wurare a cikin Isra'ila, tare da sansanonin da ke da alaƙa da Amurka, ciki har da hedkwatar runduna ta biyar ta sojojin ruwan Amurka da kuma wasu wurare a Erbil.
Jami'an Iran sun bayyana samamen a matsayin wani ɓangare na babban shirin martani ga yaƙin haɗin gwiwa na Amurka da Isra'ila wanda ke nufar yankunan Iran da ababen more rayuwarta, shafin Palestine Chronicle ya kawo labarin.
IRGC ta ce wannan hari na baya-bayan nan wani babban mataki ne a cikin yaƙin da ake ci gaba da yi, wanda ke nuna cewa Iran tana da niyyar ci gaba da faɗaɗa girma da tsananin hare-haren makaman linzami da take kaiwa.
Makaman da aka yi amfani da su
A cikin sanarwar, IRGC ta ce samamen ya dogara ne kacokan kan makaman linzami masu dogon zango, da masu dauke da makamai masu nauyi, waɗanda wasu daga cikinsu nauyinsu ya kai kusan tan ɗaya.

Kara karanta wannan
Tofa: Rigima ta barke tsakanin Amurka da Isra'ila kan yaki da Iran, an ji dalilin sabanin
Daga cikin makaman da aka ba da rahoton yin amfani da su akwai makaman linzami nau'in Kheibar da Qader waɗanda ke ɗauke da kawuna da dama, da kuma babban makamin linzami na Khorramshahr.
Dakarun sun ce an harba makaman Khorramshahr a jere da dama domin nufar sansanonin Amurka da na Isra'ila.
An kwashe sa'o'i ana ruwan wuta
A cewar IRGC, wannan rukuni na 37 ya ci gaba da gudana na tsawon akalla sa'o'i uku, wanda hakan ya sa ya zama ɗaya daga cikin ayyukan harba makamai masu linzami mafi tsayi da aka gudanar tun farkon yaƙin.
A cikin wannan lokacin, an ba da rahoton cewa dakarun Iran sun harba makamai masu linzami a matakai daban-daban zuwa wuraren da aka nufa a Isra'ila da sauran wurare a yankin.

Source: Twitter
Makamai sun haifar da fashe-fashe a Isra'ila
Kafafen yaɗa labarai na Isra'ila sun ba da rahoton cewa an ji kuwwar na'urorin gargadi a tsakiyar Isra'ila, har da yankin Tel Aviv, biyo bayan gano makaman linzami na Iran da ke tafe.
Rahotanni sun kuma nuna an ji ƙarar manyan fashe-fashe a yankin Tel Aviv, kodayake girman ɓarnar bai fito fili ba saboda tsatstsauran takunkumin yaɗa labarai na sojoji da hukumomin Isra'ila suka sanya a lokacin yaƙi.
Isra'ila ta gano sabon salon Iran
A wani labarin kuma, kun ji cewa Hukumar tsaron yanar gizo ta Isra'ila ta gano shirin kutse na kasar Iran.
Hukumar ta bayyana cewa ana kutse a cikin kyamarorin tsaro domin leƙen asiri tun bayan barkewar yakin Gabas ta Tsakiya.
Hakazalika, ta bayyana cewa an gano dozin-dozin na kutsen Iran cikin kyamarorin tsaro, lamarin da ya sa ta bukaci jama’a su kasance cikin shiri.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
