Shugaba Edogan Ya Yi Gargadi da Ya Hango Gagarumar Matsala a Yakin Iran da Amurka
- Recep Tayyip Erdogan na Turkiyya ya ce akwai matsala mai girma a Gabas ta Tskiya idan ba a dakatar da yakin Iran, Amurka da Isra'ila ba
- Shugaba Erdogan ya bayyana cewa wannan rikici na iya mamaye gaba daya yankin idan ba a gaggauta samar da mafita mai dorewa ba
- Sannan shugaban kasar ya ce za a iya warware komai a samar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya idan aka bi tsarin diflomasiyya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Turkey - Shugaban kasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya yi kira da a dakatar da yakin da ke gudana tsakanin Iran da hadakar Amurka da Isra'ila tun kafin ya bazu ya mamaye yankin Gabas ta Tsakiya.
Shugaba Erdogan ya yi gargadin cewa matukar ba a gaggauta dakatar da yakin ba, to babu makawa sai ya kara jefa tattalin arzikin duniya cikin gagarumar matsala.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Rasha ta yi nasara, ta fi kowa amfana da yakin Iran da Amurka, Isra'ila

Source: Getty Images
Jaridar Al-Arabiyya ta ruwaito cewa Erdogan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 11 ga watan Maris, 2026 inda ya ce yankin Gabas ta Tsakiya “ya sake fadawa cikin rikici da zubar jini."
“Dole ne a dakatar da wannan yaki kafin ya kara girma ya kuma mamaye dukkan yankin,” in ji shi.
Erdogan ya kawo yadda za a samu mafita
Shugaban kasar na Turkiyya ya ce akwai yiwuwar kawo karshen rikicin idan aka bi hanyar diflomasiyya, yana mai cewa ya kamata kasashen su koma kan teburin tattaunawa.
Sai dai wannan kira na zuwa ne kwana guda bayan ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya nuna cewa Tehran ba ta da niyyar tattaunawa da Amurka.
Araghchi ya jaddada cewa Iran ba za ta koma teburin tattaunawa da Amurka ba saboda ta yi a baya kuma ba ta ji dadin abin da ya biyo baya ba.
Yakin ya kara dagula kasuwar mai
Yakin ya fara ne bayan hare-haren hadin gwiwa da Amurka da Israel suka kai Iran a ranar Asabar, 28 ga Fabrairu, 2026.
Rikicin ya haddasa mutuwar mutane da dama, raba jama’a da gidajensu da kuma lalacewar muhimman kadarori, sannan ya girgiza kasuwar makamashi ta duniya, inda farashin man fetur ya tashi sosai.

Source: Getty Images
Erdogan ya yi gargadi cewa idan aka ci gaba da wannan yaki za a kara tafka asarar rayuka da dukiyoyi masu dumbin yawa.
“Za a samu karin asarar rayuka da dukiyoyi, sannan kuma tattalin arzikin duniya zai kara shiga matsala idan ba adakatar da wannan yaki ba," in ji shi.
Erdogan ya ce Turkiyya na ci gaba da kokarin nemo mafita ta diflomasiyya domin kawo karshen rikicin, kamar yadda tashar Al-Jazeera ta ruwaito.
Tun bayan fara yakin, Iran ta mayar da martani da hare-haren makamai masu linzami a wasu sassan Gabas ta Tsakiya.
Iran ta kai hari mafi muni kan Isra'ila
A wani labarin, kun ji cewa Iran ta sanar da kai hare-hare mafi muni kan Isra'ila tun bayan barkewar yaki a tsakaninsu a yankin Gabas ta Tsakiya.

Kara karanta wannan
Akwai matsala: Majalisar Dinkin Duniya ta hango abin da zai faru sakamakon yakin Amurka da Iran
Rundunar juyin juya hali ta Iran (IRGC) ce ta tabbatar da hakan, inda ta bayyana cewa ta ƙaddamar da rukuni na 37 na farmakin nan mai suna “True Promise 4”.
Dakarun IRGC sun ce samamen ya haɗa da hare-hare kan wurare a Tel Aviv da sauran wurare a cikin Isra'ila, tare da sansanonin da ke da alaƙa da Amurka.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
