Mojtaba Khamenei: Sabon Jagoran Iran Ya Samu Rauni a Harin Isra'ila da Amurka

Mojtaba Khamenei: Sabon Jagoran Iran Ya Samu Rauni a Harin Isra'ila da Amurka

  • Ana cigaba da maganganu kan rashin ganin sabon jagoran addini na kasar Iran, Mojtaba Khamenei tun bayan zaben shi da aka yi
  • Wasu rahotanni sun nuna cewa wani rauni da sabon jagoran ya samu na cikin dalilan da suka hana shi bayyana a bainar jama'a
  • An nada Mojtaba Khamenei a matsayin sabon jagoran Iran bayan harin da Amurka da Isra'ila suka kai ya yi sanadiyyar mahaifinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Iran - Masu sharhi kan lamuran yau da kullum na cigaba da tsokaci game da rashin bayyanar sabon jagoran Iran, Mojtaba Khamenei a gaban jama'a.

A baya, wasu majiyoyi daga Iran sun nuna cewa yana cikin koshin lafiya tun bayan harin da aka kai ranar 28 ga Fabrairun 2026.

Mojtaba Khamenei a wani waje a Iran
Sabon jagoran addini na Iran, Mojtaba Khamenei. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Sai dai New York Times ta ce ta samu sababbin bayanai game da halin da ya ke ciki daga majiyoyin Iran da kuma bangaren Isra'ila.

Kara karanta wannan

China ta shata wa Amurka da Isra'ila layi kan sabon jagoran addinin Iran, Mojtaba Khamenei

Mojtaba Khamenei ya samu rauni a hari

An ce sabon jagoran Iran, Mojtaba Khamenei, ya samu raunuka a kafafunsa a ranar farko da Amurka da Isra’ila suka kaddamar da hare-hare kan Iran.

Rahoton ya ambato wasu jami’ai daga Isra’ila da Iran inda suka ce Mojtaba Khamenei ya samu raunukan ne a lokacin da aka fara kai hare-haren.

A ranar Lahadi aka sanar da Mojtaba Khamenei mai shekaru 56 a matsayin wanda zai gaji mahaifinsa kuma tsohon jagoran Iran a aka kashe a ranar farko ta yakin.

Mojtaba Khamenei bai yi jawabi ba

Rahoton ya ce Mojtaba Khamenei ya samu raunuka a ranar farko, ciki har da a kafafunsa, wanda hakan na iya kasancewa daya daga cikin dalilan da suka sa har yanzu bai bayyana a bainar jama’a ko a cikin wani bidiyo ba.

Times of Israel ta ce har zuwa safiyar ranar Laraba, fiye da sa’o’i 48 bayan nadinsa, bai fitar da wata sanarwa ba kuma bai fito fili a bainar jama’a ba.

Kara karanta wannan

Ana cikin musayar wuta, Shugaba Putin ya aika sako ga sabon jagoran Iran, Mojtaba Khamenei

Wasu majiyoyi sun shaida cewa baya ga raunukan da ya samu, akwai kuma fargabar cewa za a iya kai masa hari idan ya yi wata sanarwa a bainar jama’a.

Mutanen Iran dauke da hoton mojtaba Khamenei
Yadda aka yi zanga-zangar goyon bayan Mojtaba Khamenei a Iran. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rahotannin da suka gabata sun nuna cewa Mojtaba Khamenei ya ji rauni a yakin, inda wasu kafafen yada labarai na gwamnatin Iran suka bayyana lamarin da samun rauni a hannun makiya.

Sai dai duk da haka, har yanzu ba a tabbatar ko raunukan da ya samu za su hana shi gudanar da shugabancin kasar ba ko kuma zai warke nan kusa kadan.

Koriya ta caccaki Amurka saboda taba Iran

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin Koriya ta Arewa karkashin jagorancin Koriya ta Arewa ta caccaki Amurka da Isra'ila kan kai hari Iran.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Koriya ta Arewa ya ce kasar ta goyi bayan nada Mojtaba Khamenei a matsayin sabon jagoran addini.

Kasar ta kuma bayyana kisan Ayatollah Ali Khamenei da Amurka da Isra'ila suka a matsayin keta hakkin kasa da kasa a duniya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng