Yakin Iran da Amurka: Sojojin Isra'ila Sun Kashe Babban Malamin Addinin Kirista

Yakin Iran da Amurka: Sojojin Isra'ila Sun Kashe Babban Malamin Addinin Kirista

  • Sojojin Isra'ila sun kashe wani limamin cocin Katolika, Pierre al-Rahi a kudancin Lebanon yayin da yake kokarin ceto wadanda hari ya raunata
  • Fafaroma Leo XIV ya nuna alhini kan kisan limamin cocin tare da yin kira ga kasashen duniya da su gaggauta tsagaita bude wuta yanzu
  • Uba al-Rahi ya ki tserewa daga kauyensa domin ya ci gaba da ba mabiyansa kariya ta addini kafin harin tankar yakin Isra'ila ya hallaka shi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Lebanon - Hukumomin cocin Katolika sun tabbatar da mutuwar Pierre al-Rahi, wani limamin cocin darikar Maronite Katolika, a wani harin Isra'ila da ta kai a kudancin Lebanon.

Kafin mutuwarsa, al-Rahi ya ƙi amincewa da umarnin sojojin Isra'ila na ƙaurace wa ƙauyen kirista na Qlayaa, inda ya zaɓi ya tsaya tare da mabiyansa kusan 8,000 domin ba su kariya da tallafi.

Kara karanta wannan

Bidiyon lokacin da makamin Iran ya fada tsakiyar birnin Isra'ila, mutane sun mutu

Sojojin Isra'ila sun kashe wani limamin Katolika a Lebanon
Mutane sun tari a waje don nuna bacin ransu kan kisan limamin kotolika, Pierre al-Rahi a harin Isra'ila a garin Al-Qlayaa a kudancin Lebanon. Hoto: Rabih DAHER / AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Isra'ila ta hallaka malamin Katolika a Lebanon

Rahoton shafin Catholic Register ya bayyana cewa wata tankar yaƙi ta Isra'ila nau'in Merkava ta harbi wani gida har sau biyu a ƙauyen.

Harin farko ya raunata mai gidan da matarsa, inda uba al-Rahi da wasu maƙwabta suka garzaya domin ba su agaji. A daidai wannan lokaci ne tankar ta sake yin harbi na biyu, wanda ya raunata limamin cocin kuma daga baya ya mutu.

Wannan hari na Isra'ila da ya yi ajalin Pierre al-Rahi, wanda aka fi sani da Pierre el-Raï da Faransanci, ya afku ne a ranar 9 ga Maris, 2026.

Fafaroma ya yi martani kan kashe malamin addinin

Fafaroma Leo XIV ya nuna "tsananin baƙin ciki" ga dukkan waɗanda suka rasa rayukansu a yakin Gabas ta Tsakiya, musamman yara ƙanana da kuma waɗanda ke aikin sa-kai kamar Pierre al-Rahi.

Ta hanyar dandalin Telegram na fadar Vatican, Paparoma ya bayyana cewa yana bibiyar lamarin cike da damuwa kuma yana addu'ar ganin an daina fafatawar cikin gaggawa.

Kara karanta wannan

Bayan kwana 10 ana musayar wuta, Firaministan Isra'ila ya mika bukata 1 ga mutanen Iran

A ranar 8 ga Maris, kwana guda kafin mutuwarsa, al-Rahi ya bayyana cewa:

"Dole ne a gare mu mu zauna a wannan gari, duk da haɗarin yin hakan, domin ta haka ne kawai za mu kare ƙasarmu cikin lumana. Babu wanda ke ɗauke da makami a cikinmu; dukkanmu muna ɗauke da zaman lafiya, alheri da ƙaunar juna."
Isra'ila na ci gaba da kai hare-hare a garuruwan Lebanon don mayar da martani ga Hezbollah.
Wani bakin hayaki ya turnuke sararin samaniya a Lebanon bayan harin Isra'ila. Hoto: Kawnat HAJU / AFP via Getty Images
Source: Getty Images

An yi ta'aziyyar malamin cocin Katolikan

Ƙungiyoyin agaji na ƙasa da ƙasa irin su ACN sun yi kira da a yi addu'a ga limamin, wanda aka sani da jajircewa wajen yi wa al'ummarsa hidima a cikin mawuyacin hali.

Rahoton The National Catholic Reporter ya nuna cewa dubunnan fararen hula a Lebanon ne suka tsere daga gidajensu samakakon tsoron karin hare-hare a gundumar Marjayoun.

Babban sakataren majalisar malaman Katolika na Lebanon, Jean Yqounes, ya bayyana cewa:

"Pierre al-Rahi ya fito ne daga kauye na, Dibeh, amma shi ya kasance malamin addinin Qlayaa a Marjayoun. Abun bakin ciki ne yadda ya mutu. Ubangiji ya ba ruhinsa salama."

Kara karanta wannan

Hezbollah ta kakkabo jirgin yaƙin Isra'ila, an kashe fiye da mutane 1330 a Iran

Hezbollah ta kakkabo jirgin Isra'ila

Kun dai ji cewa, wasu jami'an Hezbollah a yankin Bekaa sun tabbatar wa manema labarai cewa an yi nasarar kakkabo jirgi mai saukar ungulu guda ɗaya na Isra'ila.

Tun da fari, Hezbollah ta bayyana cewa ta gano "shigar kusan jirage masu saukar ungulu 15 na abokan gaba" daga ɓangaren iyakar Siriya zuwa gabashin Lebanon.

Ƙungiyar ta ce dakarunta sun yi artabu da jiragen da kuma sojojin da suka shigo da "makamani," kuma har ta samu nasarar kakkabo daya daga cikin jiragen.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com