Kim Jong Un Ya Shiga Batun Yaki da Iran, Ya Ragargaji Trump da Netanyahu

Kim Jong Un Ya Shiga Batun Yaki da Iran, Ya Ragargaji Trump da Netanyahu

  • Koria ta Arewa da Kim Jong Un ke jagoranta ta yi magana game da yakin da aka shafe sama da kwana 10 ana gwabzawa a Gabas ta Tsakiya
  • Gwamnatin Kim Jong Un ta goyi bayan nadin Mojtaba Khamenei a matsayin sabon jagoran addinin Iran bayan kashe mahaifinsa a harin Amurka/Isra'ila
  • Shugaban Koria ta Arewa ya caccaki Amurka da Isra'ila a kan fara kai hare-hare Iran a ranar 28 ga watan Fabrairun 2026 da ya jawo kashe mutane

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Koriya ta Arewa ta shiga sahun kasashen duniya da suka yi magana game da yakin da ake cigaba da yi a Gabas ta Tsakiya.

Rahotanni sun nuna cewa Koria ta Arewa, karkashin Kim Jong Un ta nuna goyon baya ga Iran yayin da take fafatawa da Amurka da Isra'ila.

Kara karanta wannan

Amurka ta shiga uku, Shugaban Rasha, Putin ya kira Shugaban Iran ta wayar tarho

Shugaban Koria ta Arewa, Kim Jong Un
Kim Jong Un na bayani a wani taro. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Tashar Al-Jazeera ta wallafa cewa ma'aikatar harkokin wajen Koria ta Arewa ta yi Allah wadai da kashe jagoran addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei da Isra'ila da Amurka suka yi.

Kim Jong Un ta goyi bayan Iran

Kasar Koriya ta Arewa ta bayyana goyon bayanta ga nadin Mojtaba Khamenei a matsayin sabon jagoran addini na kasar Iran.

Ta kuma yi Allah-wadai da abin da ta kira harin soja na “ba bisa ka’ida ba” da Amurka da Isra’ila suka kai wanda ya kashe mahaifinsa.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Koriya ta Arewa ya bayyana cewa Pyongyang na girmama matakin da Tehran ta dauka na nadin Mojtaba Khamenei, dan marigayi Ali Khamenei.

Ya ce dangane da sanarwar da aka yi kwanan nan cewa majalisar kwararrun Iran ta zabi sabon jagoran juyin juya halin Musulunci, Koriya ta Arewa na girmama ra'ayin al’ummar Iran da zabinsu.

Kim Jong Un ya caccaki Trump

Kara karanta wannan

Rasha ta fadi dalilin da ya sa ba ta kai dauki ga Iran ba a yakinta da Isra'ila

Kakakin Koriya ta Arewa ya kuma soki kasashen Amurka da Isra’ila saboda kaddamar da abin da ya kira harin da ya saba wa doka kan Iran.

Times of India ta wallafa cewa ya ce:

“Mun nuna matukar damuwa tare da yin Allah-wadai da hare-haren Amurka da Isra’ila, wadanda ta hanyar kai harin soja da ya sabawa doka kan Iran suka lalata ginshikan zaman lafiya da tsaro a yankin, tare da kara rashin kwanciyar hankali a duniya.”
Jagoran addinin kasar Iran da ya rasu
Marigayi Ayatollah Ali Khamenei a Iran. Hoto: Getty Images
Source: Twitter

Sanarwar ta kara da cewa irin wadannan matakai na lalata tsarin siyasa da cikakken ikon kasa a yankinta, wanda ba abin yarda ba ne kuma dole duniya baki daya ta yi Allah-wadai da shi tare da yin watsi da shi.

Iran ta jikkata sojojin Amurka 150

A wani labarin, kun ji cewa Amurka ta sanar da cewa Iran ta jikkata mata sojoji 140 a hare-haren da ta kai a sansanoninta a Gabas ta Tsakiya.

Sai dai wasu rahotanni da ba na gwamnati ba sun nuna cewa an raunata sojoji sama da 150, sabanin bayanin da ma'aikatar yakin Amurka ta yi.

Baya ga raunata sojojin, Amurka ta sanar da cewa an kashe mata dakaru 7 a Kuwait da Saudiyya a wasu hare-hare da Iran ta kaddamar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng