Rundunar Sojin Ruwan Amurka Ta Karaya duk da Kurin Trump ga Iran

Rundunar Sojin Ruwan Amurka Ta Karaya duk da Kurin Trump ga Iran

  • Rundunar sojin ruwan Amurka ta yi martani ga kamfanonin jigilar kaya da ke neman a raka su domin ratsawa a mashigar Hormuz da ke Iran
  • Rundunar ta ce haɗarin hare-hare ya yi yawa don haka ba za ta iya rakiyar jiragen kasuwanci a mashigar Hormuz a yanzu ba
  • Duk da alkawarin da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi, sojoji na ci gaba da nazarin hanyoyin tsaro kafin a fara rakiyar jiragen

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

USA – Rundunar sojin ruwan Amurka ta ƙi amincewa da roƙon kamfanonin jigilar kaya na duniya na a ba su rakiyar sojoji a mashigar ruwa ta Hormuz.

Hormuz ia ce daya daga cikin manyan hanyoyin ruwa da jiragen dakon mai ke wucewa daga Gabas ta Tsakiya zuwa sauran sassan duniya.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Iran ta bukaci kasashe su fatattaki jakadun Amurka da Isra'ila

Sojin ruwan Amurka sun ba za a raka jiragen mai a Hormuz yanzu ba
Daya daga cikin sojojin ruwan Amurka, Shugaba Donald J Trump Hoto: US Navy/Donald J Trump
Source: Facebook

Reuters a wallafa cewa rahotanni sun nuna cewa kamfanonin jiragen ruwa suna roƙon rundunar sojin Amurka kusan kullum tun bayan fara yaƙin Amurka da Isra’ila da Iran.

Rokon kamfanonin ruwa ga rundunar sojin Amurka

CNA ta ruwaito cewa tun bayan fara yakin kamfanoni sun roki rundunar sojin ruwan Amurka domin a basu kariya yayin da jiragensu ke wucewa ta mashigar.

Sai dai majiyoyi daga bangaren harkokin jiragen ruwa sun ce rundunar sojin ruwan Amurka ta bayyana cewa a halin yanzu ba za ta iya samar da rakiyar ba.

Ta bayar da dalilin cewa akwai hadarin gaske a tattare da bi a mashigar, musamman a yanzu da Iran ta kafa ta tsare.

An ce sojojin ruwan Amurka na yin tarurrukan bayani akai-akai da kamfanonin jigilar kaya da na man fetur domin tattauna halin da ake ciki.

A irin waɗannan tattaunawa ne aka shaida masu cewa har yanzu ba a ga damar samar da rakiyar jiragen ba.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Sojojin Iran sun ja kunnen Trump kan neman tsayar da yaki

Shugaban Amurka ya yi alkawari ga kamfanoni

Mashigar Hormuz na da muhimmanci sosai ga kasuwancin man fetur na duniya, domin kusan kashi ɗaya bisa biyar na man da ake fitarwa a duniya na wucewa ta wannan hanya.

Tun bayan fara yaƙin da Iran fiye da mako guda da ya wuce, zirga-zirgar jiragen ruwa ta ragu sosai a mashigar, lamarin da ya haifar da tashin farashin man fetur a kasuwannin duniya.

Duk da wannan matsayi na rundunar sojin ruwa, Shugaban Amurka Donald Trump ya sha bayyana cewa kasarsa a shirye take ta samar da rakiyar jiragen dakon mai idan bukatar hakan ta taso.

Trump ya ce idan lokaci ya yi, rundunar sojin ruwan Amurka tare da abokan hulɗarta za su iya rakiyar jiragen dakon mai domin su ratsa mashigar Hormuz cikin aminci.

Amurka ta sake gargadin Iran

A wani labarin, kun ji cewa Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi gargadi mai tsauri ga Iran kan yiwuwar hana zirga-zirgar mai a mashigar Hormuz a yakin da ake gwabzawa.

Kara karanta wannan

Iran ta gargaɗi Amurka, ta faɗi abin da zai faru da jiragen da Trump zai tura Hormuz

Trump ya ce Amurka za ta kai hari ninkin ba ninke har sau 20 fiye da yadda aka yi a baya idan dai Iran ta katse hanyoyin wucewar mai da mashigar tekun da ta ratsa a kasarta,

Trump ya yi barazana ga Iran
Shugaban Amurka Donald Trump a wani taro a ofishinsa Hoto: Getty
Source: Twitter

Shugaban ya kara da cewa kasashe da dama, musamman China, za su amfana idan aka ci gaba da bude mashigar tare da fatan lamarin ba zai kai ga ninka hare-haren ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng