Yau Amurka Ta Shirya Kai Hare Hare mafi Muni kan Iran, "Mazauna Tehran Su Shirya"
- Sakataren Tsaron Amurka ya bayyana cewa yau ce rana mafi muni da kasar Iran za ta fuskanci hare-haren jiragen yaki da bama-bamai
- Gwamnatin Iran ta yi watsi da maganar tsagaita wuta inda ta yi barazanar daukar fansa mai radadi kan Amurka da Shugaba Donald Trump yau.
- Farashin danyen mai ya ci gaba da kasancewa sama da dala casa'in yayin da Amurka ta daki mazaunai dubu biyar a cikin Iran yanzu.
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Amurka - Sakataren Tsaron Amurka, Pete Hegseth, ya yi gargaɗin cewa yau Talata ita ce rana mafi muni da Iran za ta fuskanci hare-hare ta sama tun farkon yaƙin.
Hegseth ya bayyana cewa Amurka ta tura mafi yawan jiragen yaƙi da bama-bamai domin farmakar wurare mafi muhimmanci a cikin Iran.

Source: Twitter
Amurka ta zafafa hare-hare a Iran
Ya ƙara da cewa a cikin sa'o'i 24 da suka gabata, Iran ta harba mafi ƙarancin makaman linzami tun farkon yaƙin, wanda hakan ke nuna cewa ƙarfin dakarunta ya fara raguwa, in ji rahoton NBC.
Babban Hafsan Sojan Amurka, Janar Dan Caine, ya bayyana cewa dakarun Amurka sun farmaki fiye da wurare 5,000 a cikin Iran yayin da yakin ya shiga rana ta 11.
Babban burin waɗannan hare-haren shi ne lalata makama masu linzamin Iran da jirage marasa matuƙa, da nakasa rundunar sojin ruwanta domin buɗe mashigar Hormuz.
Hakazalika, Amurka da kuma kawarta, Isra'ila na kokarin ganin sun farmaki masana'antun soja dake can cikin sassan ƙasar Iran.
Firayim Ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya jaddada cewa manufarsu ita ce ruguza mulkin kama-karya na Iran, inda ya ce "babu shakka ayyukanmu na kassara su."
Martanin Iran da barazana ga Trump
A ɓangaren Tehran kuma, kalaman sun kasance masu zafi. Shugaban majalisar dokokin Iran, Mohammad Bagher Qalibaf, ya bayyana a cewa Iran "ba za ta nemi tsagaita wuta ba".
Ya bayyana cewa dole ne a koya wa Amurka da Isra'ila hankali, don kar su sake tunanin taɓa Iran a nan gaba, in ji rahoton Aljazeera.
Wani babban jami'in tsaron Iran, Ali Larijani, ya yi barazana ga rayuwar Shugaba Donald Trump, inda ya gargaɗe shi da ya yi hattara kada a "kawar da shi" sakamakon barazanar da yake yi wa Iran.

Source: Twitter
Halin da tattalin arziki ke ciki yanzu
Iran na amfani da dabarar farmakar wuraren makamashi da toshe mashigin Hormuz domin haddasa raɗaɗin tattalin arziki ga duniya, da nufin tilasta wa Amurka da Isra'ila su dakatar da yaƙin, in ji rahoton Military Times.
Farashin ɗanyen mai na Brent ya kusa kai dala 120 a ranar Litinin kafin ya dawo dala 90 a yau Talata — wanda har yanzu ya ninka kashi 24% fiye da lokacin da yaƙin ya fara ranar 28 ga Fabrairu.
Shugaba Trump ya yi ƙoƙarin kwantar da hankalin mutane inda ya ce wannan yaƙin "na taƙaitaccen lokaci ne" kuma karin farashin sadaukarwa ne ga wanzar da zaman lafiya.
Rigima ta barke tsakanin Amurka da Isra'ila
A wani labari, mun ruwaito cewa, hare-haren da Isra'ila ta kai wa rumbunan adana man fetur 30 na Iran ya kawo sabani tsakaninta da Amurka.
Harin na ranar Asabar, 7 ga watan Maris 2026 ya zama sabani na farko da ya auku tsakanin Amurka da Isra'ila tun fara yaki da kasar Iran.
Amurka tana fargabar cewa hare-haren Isra'ila kan kayayyakin more rayuwa da ke amfanar talakawan Iran na iya haifar da koma-baya ta fuskar dabarun yaƙi.
Asali: Legit.ng


