Wata Sabuwa: Rasha Ta Yi Nasara, Ta Fi Kowa Amfana da Yakin Iran da Amurka, Isra'ila

Wata Sabuwa: Rasha Ta Yi Nasara, Ta Fi Kowa Amfana da Yakin Iran da Amurka, Isra'ila

  • Ana ganin kasar Rasha ce a sahun farko wajen cin gajiyar yakin da ke kara tsananta tsakanin Amurka/Isra'i'la da kasr Iran
  • Shugaban Majalisar tarayyar Turai, Antonio Costa ya ce Rasha tana amfana da wannan yaki ta bangarori daban-daban
  • A cewar Costa, farashin mai da ya karu ya samar wa Rasha karin kudaden shiga, sannan kuma Amurka ta dakatar da taimakon Ukraine

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Russia - Yayin da yakin Amurka, Isra'ila da Jamhuriyar Musulunci ke kara zafafa, ana ganin kasar Rasha ta fi kowa cin gajiyar wannan rikici na Gabas ta Tsakiya a Duniya.

Shugaban Majalisar Tarayyar Turai, Antonio Costa, ya ce har zuwa yanzu Rasha ce kadai ke cin gajiyar yakin da kasashen Amurka da Isra'ila ke yi da Iran.

Shugaba Putin.
Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin a gidan gwamnati Hoto: Gavril Grigoroc
Source: Getty Images

Tashar Al-Jazeera ta tattaro cewa Costa ya bayyana hakan ne yayin wani jawabi ga jakadun kungiyar tarayyar turai a birnin Brussels yau Talata.

Kara karanta wannan

Iran ta yi martani ga barazanar Trump, ta magantu kan kawar da shi a doron kasa

Idan ba ku manta ba, yaki ya barke ne bayan farmakin hadin gwiwa da Amurka da Isra'ila suka kai Iran a ranar Asabar, 28 ga watan Fabrairun 2026.

Wannan farmaki ya yi ajalin jagoran addini na kasar Iran, Ayatollah Alli Khamenei da wasu iyalansa, da daruruwar mutane a kasar ta Musulunci.

Wannan lamari ya harzuka kasar Iran, inda ta fara kai hare-haren ramuwar gayya kan sansanonin sojojin Amurka dake yankin da kuma biranen Isra'ila.

Yakin dai ya jawo tashin farashin danyen mai a kasuwannin duniya, lamarin da ya jefa tattalin arzikin duniya cikin mawuyacin hali.

Dalilan da suka sa yaki ke amfanar Rasha

Da yake magana kan haka, Costa ya ce tashin farashin mai sakamakon rikicin na bai wa Rasha karin kudaden shiga da za ta iya amfani da su wajen daukar nauyin yakin da take yi da Ukraine.

A cewar Costa, farashin mai da ya karu ya samar wa Rasha karin kudaden shiga, sannan kuma Amurka ta karkatar da wasu makamai da za a iya turawa Ukraine.

Haka zalika, ya ce a yanzu hankalin kasashen duniya ya koma kan rikicin Gabas ta Tsakiya maimakon yakin Ukraine, kamar yadda NBC News ta kawo.

Kara karanta wannan

Hezbollah ta kakkabo jirgin yaƙin Isra'ila, an kashe fiye da mutane 1330 a Iran

Netanyahu, Trump da Khamenei.
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, Shugaba Donald Trump na Amurka da marigayi Ayatollah Khamenei Hoto: @RealDonaldTrump, Anadolu
Source: Twitter

EU ta yi gargadi kan yaduwar rikici

Costa ya jaddada bukatar kasashen Turai su kare tsarin dokokin kasa da kasa da aka gina bisa ka’idoji, wanda ya ce yana fuskantar kalubale.

Ya kuma yi kira da a guji kara tsananta rikicin Iran da Amurka/Isra'ila, yana mai cewa:

“Dole ne mu guji karin tashin hankali. Wannan hanya na iya barazana ga Gabas ta Tsakiya, Turai, da sauran sassan duniya,” in ji shi.

Shugaban Rasha ya taya jagoran Iran murna

A wani rahoton, kun ji cewa Shugaba Viladimir Putin na kasar Rasha ya aika sakon taya murna ga sabon jagoran addini na Iran, Mojtaba Khamenei.

Putin ya bayyana cikakken goyon bayansa ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran da sabon jagoranta a daidai lokacin da rikicin Gabas ta Tsakiya ke ƙara tsananta.

Ya kara da cewa shugabancin Mojtaba zai bukaci jarumtaka da sadaukarwa, musamman a lokacin da Iran ke fuskantar hare-haren yaki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262