Iran Ta Yi Martani ga Barazanar Trump, Ta Magantu kan Kawar da Shi a Doron Kasa
- Babban jami’in tsaron Iran, Ali Larijani ya yi magana game da barazanar da Donald Trump ke yi na kai hari mai tsanani
- Trump ya yi barazanar cewa Amurka za ta kai wa Iran hari ba iyaka idan ta hana zirga-zirgar man fetur a mashigar ruwa na Hormuz
- Yakin da ya barke bayan hare-haren Amurka da Isra’ila ya dagula jigilar kusan kashi 20 na man fetur na duniya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tehran, iran - Babban jami’in tsaron Iran, Ali Larijani, ya yi martani mai zafi game da barazanar Amurka na kai munanan hari kan kasar.
Larijani wanda sakataren majalisar koli ne ya yi gargadi ga shugaban Amurka Donald Trump, yana cewa ya kula da kansa kada a kawar da shi.

Source: Getty Images
Larijani ya bayyana haka ne a cikin wani rubutun Larabci da ya yi a shafinsa na X da ranar yau Talata 10 ga watan Maris, 2026.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Rasha ta yi nasara, ta fi kowa amfana da yakin Iran da Amurka, Isra'ila
Yadda yaki ya barke tsakanin Iran, Isra'ila
A ranar 28 ga Fabrairun 2026, Amurka da Isra’ila sun kaddamar da hare-hare kan Iran, lamarin da ya haifar da barkewar yaki a yankin Gabas ta Tsakiya.
Hare-haren sun yi sanadiyyar mutuwar jagoran addinin Iran, Ali Khamenei, lamarin da ya kara tsananta rikicin.
Tun daga lokacin Iran ta mayar da martani da hare-haren jiragen yaki marasa matuki da makamai masu linzami kan Isra’ila da wasu kasashe a yankin.
Iran ta dura kan Trump bayan mata barazana
Babban jami'in ya bayyana cewa Iran ba ta tsoron abin da ya kira barazanar banza da Trump ke yi.
Ya rubuta a shafinsa na X cewa:
“Iran ba ta tsoron barazanarka marar tasiri. Har ma wadanda suka fi ka karfi ba su iya rushe al’ummar Iran ba.”

Source: Twitter
Barazanar da Trump ya yi ga Iran
Kalaman nasa sun zo ne bayan Trump ya yi barazanar kai wa Iran hari mai tsanani idan ta hana zirga-zirgar man fetur ta mashigar ruwa na Hormuz.
Trump ya rubuta a shafin Fadar shugaban kasa a X cewa idan Iran ta dauki wani mataki da zai dakatar da zirga-zirgar mai ta mashigar Hormuz, Amurka za ta kai mata hari ba iyaka.
Rahotanni sun nuna cewa zirga-zirgar jiragen ruwa ta mashigar Hormuz ta samu tangarda sosai.
Mashigar ruwa na Hormuz na daya daga cikin hanyoyin da ake jigilar kusan kashi 20 cikin 100 na man fetur na duniya.
Dakarun Iran sun kuma yi barazanar cewa ba za su bari ko lita daya na man fetur ya fita daga yankin zuwa kasashen da ke goyon bayan Amurka da Isra’ila ba muddin yakin na ci gaba.
Fargaba a Amurka kan yakin Iran da Isra'ila
An ji cewa tasirin da yakin Amurka/Isra'ila da Iran ya ke haifarwa a bangaren makamashi ya fara jefa fargaba a gwamnatin shugaba Donald Trump.
Jami'an gwamnatin Trump sun yi zama a karshen makon da ya wuce domin sake nazari game da hanyar da za su shawo kan lamarin.
Tun bayan kashe Ayatollah Ali Khamenei, hukumomin Iran suka rufe mashigar Hormuz da ake bi wajen jigilar mai zuwa kasashe duniya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
