Bayan Kwana 10 Ana Musayar Wuta, Firaministan Isra'ila Ya Mika Bukata 1 ga Mutanen Iran
- Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya sake tsoma baki kan tsarin mulkin da kasar Iran ke tafiya a kansa karkashin jagoran addini
- Netanyahu ya bukaci mutanen Iran su tashi tsaye, su canza gwammati mai ci, inda ya ce makomar sauyin siyasar Iran na hannun al’ummarta ne
- Wannan kalamai na Firaministan na zuwa ne a daidai lokacin da yaki ke kara zafi tsakanin Jamhuriyar Musulunci da hadakar Amurka da Isra'ila
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Isra'ila - Bayan shafe ranaku 11 ana musayar wuta, Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya mika bukata ga al'ummar Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Netanyahu, ya yi kira ga al’ummar Iran da su kawo sauyin siyasa a kasarsu ta hanyar kawo karshen mulkin shugabannin da ke kan karagar iko a Tehran.

Source: Getty Images
Netanyahu ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin wata ganawa da wakilan ma’aikatar lafiya ta Isra’ila, inda ya ce makomar sauyin siyasar Iran na hannun al’ummarta ne, in ji Washington Post.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Rasha ta yi nasara, ta fi kowa amfana da yakin Iran da Amurka, Isra'ila
Manufar Isra'ila kan kasar Iran
A cewarsa, manufar Gwamnatin Isra’ila ita ce ganin al’ummar Iran sun kubuta daga abin da ya kira mulkin danniya.
“Manufarmu ita ce mu taimaka wajen ganin al’ummar Iran sun kawar da mulkin zalunci, amma a karshe su ne za su yanke shawara,” in ji Netanyahu.
A wata sanarwa da ofishin Firaministan Isra'ila ya fitar, Netanyahu ya ce lokaci ya yi da Iraniyawa za su canza tsarin mulkin kasarsu.
“Mun karya karfinsu” — Netanyahu
Da yake magana kan shugabannin Iran, Netanyahu ya ce matakan da Isra’ila ta dauka zuwa yanzu sun yi tasiri sosai, yana mai ikirarin cewa sun karya karfin gwamnatin Iran.
“Babu shakka muna karya karfinsu da matakan da muka dauka zuwa yanzu,” in ji shi.
Ba wannan ne karon farko da Netanyahu ke kira ga sauyin siyasa a Iran ba, domin a lokuta da dama ya taba bukatar al’ummar kasar su yi juyin juya hali kan tsarin mulkin gwamnati mai ci.

Source: Getty Images
Jawabinsa na zuwa ne a daidai lokacin da musayar wuta tsakanin Isra’ila da Iran ke kara tsananta, yayin da rikicin ke ci gaba da mamaye yankin Gabas ta Tsakiya, cewar Vanguard.
Gwamnatin Iran ta sha nanata cewa al'ummar kasar na tare da shugabannin su, kuma za su yi duk mai yiwuwa wajen bai wa kasarsu kariya daga wadanda ta kira da "makiya."
Iran ta kara kai hare-hare Isra'ila
A wani labarin, kun ji cewa Rundunar sojojin Isra'ila ta bayyana cewa tuni tsarin kariya na sararin samaniya ya fara aiki domin kakkabo makaman da Iran ta harbo zuwa cikin kasar.
An ruwaito cewa kasar Isra'ila yi nasarar kakkabo daya daga cikin makamai masu linzami da aka harba daga Iran, yayin da wani ya fada cikin teku a Tel Aviv.
Rahotanni sun nuna cewa rundunar Isra’ila ta kuma kai hari kan na’urar harba makamai a Iran da ake zargin ita ce ta harba makaman da suka nufi Isra’ila.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
