Wata Sabuwa: Iran Ta Bukaci Kasashe Su Fatattaki Jakadun Amurka da Isra'ila

Wata Sabuwa: Iran Ta Bukaci Kasashe Su Fatattaki Jakadun Amurka da Isra'ila

  • Kasar Iran ta fara kokarin raba Amurka da Isra'ila da abokon huldarsu na duniya saboda toshe mashigar Hormuz da ake jigilar mai ta cikinta
  • A wata sanarwa da suka fitar, dakarun Iran sun bukaci kasashen da ke bukatar jigilar man fetur cikin sauki su kori jakadun Amurka da Isra'ila
  • Toshe mashigar Hormuz da kasar Iran ta yi saboda yakin da ake ya jawo tashin farashin mai a fadin duniya, lamarin da aka dade ba a gani ba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Iran - Rundunar juyin juya halin Iran (IRGC) ta sanar da cewa za ta bai wa wasu kasashe damar wucewa ta mashigar Hormuz, amma ta ce wannan damar za ta kasance da sharadi.

Iran ta toshe mashigar Hormuz ne bayan hare-haren da Amuka ta hada kai da kasar Isra'ila suka kai mata a karshen watan Fabrairun 2026.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Sojojin Iran sun ja kunnen Trump kan neman tsayar da yaki

Sojojin Iran yayin wani fareti a shekarun baya
Sojojin Iran na fareti a gaban marigayi Ayatollah Ali Khamenei. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rahoton Arab News ya nuna cewa bayan korafi da kasashe da dama suka fara yi game da tsadar makamashi, Iran ta kafa sharadin bude musu mashigar.

Iran na so a kori jakadun Amurka

IRGC ta ce kasashen Larabawa ko na Turai da za su kori jakadun Isra’ila da na Amurka daga kasashensu ne kawai za su samu damar wucewa ta mashigar Hormuz.

Legit Hausa ta rahoto cewa ta mashigar ruwan Hormuz ake jigilar kusan kashi 20 cikin 100 na man da ake amfani da shi a kasashen duniya.

Sanarwar Iran na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar kai hari idan Tehran ta yi yunkurin hana jigilar mai ta mashigar.

Maganar yanke alaka da Amurka/Isra'ila

Rahoton WIO News ya bayyana cewa IRGC ta ce kasashen da za su yanke hulda da Isra’ila da Amurka ne kawai za su samu cikakkiyar damar wucewa da danyen mansu ta wajen

Kara karanta wannan

Akwai matsala: Majalisar Dinkin Duniya ta hango abin da zai faru sakamakon yakin Amurka da Iran

Wannan mataki na zuwa ne yayin da ake ci gaba da rikicin Iran, inda farashin mai ya haura dala 100 kan kowace ganga saboda dalilai da dama.

Daga cikin dalilan akwai tsayawar zirga-zirgar jiragen dakon mai ta mashigar Hormuz da kuma raguwar samar da mai a yankin Gabas ta Tsakiya.

Donald Trump zai sassauta takunkumin mai

A ranar Litinin, Shugaban Amurka Donald Trump ya yi gargadin cewa zai kai hari mafi girma kan Iran idan Tehran ta hana jigilar mai amma ya dan sassauto.

A wata sanarwa ta ya fitar, Shugaban kasar Amurkan ya bayyana cewa zai sassauta wasu takunkumin da suka shafi mai saboda rikicewar kasuwa.

Shugaban Amurka, Donald Trump
Shugaba Donald Trump a wani taro a Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ya ce wa manema labarai bayan tattaunawarsa da Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, tare da ambaton Shugaban China Xi Jinping cewa:

“Za mu sassauta wasu takunkumin da suka shafi mai domin rage tashin farashi.”

Dakatar da yaki: Iran ta gargadi Shugaba Trump

A wani rahoton, kun ji cewa sojojin Iran sun yi wa Shugaba Donald Trump martani game da maganar dakatar da yaki da ya fara.

Kara karanta wannan

Kasar Iran ta farmaki wani jirgin yaki, ta kara yi wa Amurka da Isra'ila babbar illa

Sun bayyana cewa su suke da ikon fadar yaushe za a dakatar da yakin, ba wai Donald Trump ya hada kai da Isra'ila wajen fara kai hari ba.

Sun kuma kara da cewa Trump na neman hanyar fita daga yakin ne ganin babu alamun zai yi nasara a gwabzawar da ake cigaba da yi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng